Don namen mulki ’yan siyasa ke sukan Tinubu —Gwamnan Kaduna
Published: 4th, February 2025 GMT
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya soki ’yan siyasar da ke sukar gwamnatin Shugaban Bola Tinubu da cewa suna yi ne kawai domin neman mulki.
Uba Sani ya bayyana cewa ’yan siyasar da ke yawan sukan Tinubu a baya-bayan nan ba su da wani abin da za magance matsalolin Najeriyar da suke suka shugaban kasan a kai.
Ya kara da cewa masu sukan Tinubun su ne suke ta yabon shugaban kasar, amma yanzu da mulki ya bar hannunsu suka dawo suna zagin sa.
A cewarsa, babu mutum daya a cikin taron masu kushe Tinubun da ke da nagartar da ta fi shugaban kasar, yana mai jaddada cewa Tinubu ya yi yaki kai da fata kuma har yanzu yana kare muradun tsarin dimokuradiyya.
Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala —Uba Sani Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa BaIdan ba a manta ba a makon jiya ne a yayin wani taro da suka gudanar a Abuja, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar da takwaransa na Jam’iyyar LP, Peter Obi da tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon Gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi, da tsohon Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi da sauransu suka salon mulkin Tinubu da jam’iyyar APC.
Amma a yayi wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin na TVC a ranar Litinin, Gwamna Uba Sani ya bayyana zargin nasu matsayin mara tushe.
Ya ce, “yawancin wadannan ’yan siyasan kamar a kan kansu suke magana. Ai da a jam’iyya daya muke da su, don haka ina makamin abin da suke yi.”
Ya bayyana maganganun nasu da soki-burutsu da “neman wautar da hankalin ’yan Najeriya,” amma ai yawancinsu masu rike mukaman gwamnati ne kimanin shekaru biyu da suka gabata, mai suka yi a lokacin?”
Don haka ya zarge su da sukan Tinubu domin samun karbuwa a wurin ’yan Najeriya a yunkurinsu na samun madafun iko.
Amma ya ce, “’Yan Najeriya na da hankuale, sun san cewa ’yan siyasar na yakar Tinubu ne kawai saboda babu abin da suka fi shi da shi. Sun samu dama a bayan, amma me suka yi da ita?”
Ya kara da cewa yawancin masu sukar Shugaban Kasar su ke yabon Tinubu, amma da suka sauka daga mulki sai suka sauya baki.উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan Najeriya Siyasa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi ritaya a matakin jiha da kananan hukumomi.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.
A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.
Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.
Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.