Shugaba Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa rahotanin da ya samu game  kyawawan dabi’u da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje suke nunawa a kasashen da suke, yana mai cewa hakan zai zaburar da matasa kan dabi’un da ke kara martabar kasa.

Shugaban ya yabawa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje yayin da ya karbi wasiku daga jakadan kasar  Kanada a Najeriya, Pasquale Salvaggio, da jakadan Saliyo, Dr Julius F.

Sandy, a fadar gwamnati.

Har ila yau, shugaba Tinubu ya karbi wasikun amincewa da nuna gamsuwa daga Legesse Geremew Haile, jakadan kasar Habasha a Najeriya, da Archbishop Michael Francis Crotty, shugaban Bishop Bishop na fadar Vatican a Najeriya.

Babban Kwamishinan na Kanada ya shaida wa Shugaba Tinubu cewa ’yan Najeriya suna da himma a fannin ilimi, da wasannin motsa jiki, da kimiyya, da lafiya, da kasuwanci a kasarsa.

Ya ce ‘yan Najeriya a Kanada suna nuna kyawawan dabi’u da wayewa, da kwazo yayin  cimma burinsu.

Salvaggio, wanda a baya ya yi aiki a Ghana da Cote’Ivoire, ya ce Kanada na neman fadada sha’awarta a kan man fetur da iskar gas, da al’amuran da suka shafi fasahar zamani, da noma, a dangantakar ta Najeriya.

Shugaba Tinubu ya yaba da nasarorin da ‘yan Najeriya suka samu a kasashen waje, yana mai bayyana su a matsayin abin zaburarwa ga mutane da dama.

A wani taron da ya yi da babban jakadan Saliyo kuwa, shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa, muradin Najeriya na ci gaban gabar tekun Yamma da Afirka shi ne abin da ya sa a gaba.

Shugaban ya shaida wa jakadan cewa jarin da Najeriya ta yi a Saliyo na tsawon shekaru da dama ya taimaka wajen ci gaban Afirka da kuma inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Jakadan ya godewa shugaban kasar bisa goyon bayan da Najeriya ke bayarwa wajen cigaban kasarsa.

Ya ce “A Saliyo, ‘yan Najeriya sun fi ‘yan kasar  yin kasuwanci, yawancin malamai a makarantu ‘yan Najeriya ne, babu bambanci tsakanin dan Najeriya da dan Saliyo idan kana tafiya a kan titin Freetown.”

“Muna bukatar ci gaba da neman zaman lafiya a nahiyarmu, ya kamata mu hada karfi da karfe wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kalubalen da muke fuskanta a Afirka shi ne rashin tsaro, wanda ke hana ci gaba, ba mu da wanda zai kawo mana zaman lafiya, ssai in mun yi aiki tukuru.” in ji shi.

 

Daga Bello Wakili

 

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: xYan Najeriya Mazauna kasashen waje Shugaba Tinubu ya yan Najeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi tazarce

Shugaba Samia Suluhu Hassan ta kasar Tanzania ta sake lashe zaɓen shugaban ƙasar mai cike da ruɗani.

Hukumomin zaɓen ƙasar sun sanar da cewa Shugaba Samia Suluhu ta lashe zaɓen ne da kashi 97 na kuri’un da aka jefa.

Hukamar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa mutum 31,913,866 ne suka kaɗa kuri’a a zaɓen, wanda ya gudana a yayin da kasar ke fama da ƙazamar zanga-zanga.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • El-Zakzaki: Yakin Sudan Yana Kare Maslahar Kasashen Yamma ne Kawai
  • Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 
  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  • Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi tazarce
  • Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta
  • Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare