2025-05-23@19:45:43 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4095
«Kwadebuwa»:
Mahaifinta, Everistus Nnadozie, ya ce an sanar da shi cewa surukinsa Esosa Imasuen ne ya yi wa ‘yarsa duka har ta samu raunika sosai. Ya ƙara da cewa an kai ta asibiti inda likita ya tabbatar da cewa tana fama da zubar jini a cikin jikinta. Ya ce kafin ya isa asibitin, ‘yarsa ta rasu....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Dangantaka na ƙara rincaɓewa tsakanin masu shirya finafinai Kannywood da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, wacce daya daga cikin jaruman fina-finan Kannywood Abba El-Mustapha, ke jagoranta. A baya-bayan nan, hukumar ta dakatar da fina-finai masu dogon zango guda 22, bayan saɓaninta da wasu masu shirya fina-finai, inda...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce iran ba ta bukatar izinin kowa kan inganta sinadarin urenium din ta, don haka Amurka ta daina maganar banza da dagewa akan wannan batu inji shi. Ayatullah Khamenei ya kara da cewa, babban kuskure ne a ce su (Amurka) ba za su...
Birtaniya ta dakatar da tattaunawar cinikayya cikin ‘yanci da Isra’ila, bayan firaminista Keir Starmer ya ce ya kadu da yadda Isra’ila ke ci gaba da yakin Gaza. Sakataren harkokin wajen Birtaniya, David Lammy ya bayyana matakin jingine batun ciniki tsakanin Birtaniya da Isra’ila, ya kuma nemi jakadan Isra’ila a Birtaniya ya bayyana a gaban Ofishin...
Hukumar Ba da Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu a Gabas ta Tsakiya (UNRWA) ta yi gargadin cewa akwai yiyuwar Gaza ta fuskanci matsalar jin kai mafi muni tun watan Oktoban 2023. A cikin wani sako da ta wallafa a shafin X, UNRWA ta ce yanzu haka makonni 11...
Bayan sanarwar ba-zata da Amurka ta yi a makon da ya gabata, Tarayyar Turai ta ce za ta dage takunkumin da ta kakaba wa Syria. Ministocin harkokin waje da ke taro a Brussels ne suka yanke shawarar dage dukkan takunkumin tattalin arzikin kan Siriya. “Muna son taimakawa al’ummar Siriya wajen sake gina sabuwar Siriya,” in...
Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa ya zama wajibi ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da yaki da rashin tsaro a kafatanin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar Kwamishinan Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Birgediya Janar Mohammad Bello Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan 279 ga Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta Najeriya (NURTW reshen jihar Jigawa karkashin shirinta na tallafawa masu sana’o’i. Kwamishinan Muhalli, Sabunta Makamashi da Sauyin Yanayi na jihar, Dr. Nura Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan...
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta sayar da gidaje 753 da aka ƙwato daga tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele. Wannan sanarwar ta fito ne daga Ministan Gidaje, Ahmed Dangiwa, a ranar Talata yayin da yake karɓar takardun mallakar gidajen daga hannun Hukumar EFCC. Mun dakatar da sanya tallan magungunan gargajiya a...
A ziyarar da ya kai jerin kogon Longmen, mai shekaru sama da 1,500 wanda UNESCO ta sanya cikin jerin wuraren tarihi da aka gada na duniya, wanda kuma shi ne ke wakiltar matsayin koli na fasahar sassaka kan dutse ta kasar Sin, shugaban ya bayyana muhimmancin karewa da gado da ma yayata al’adun gargajiya na...
A yau Talata ne dai sojojin Sudan su ka sanar da cewa, baki dayan jihar Khartum ta zama ‘yantacciya daga dakarun kai daukin gaggawa na ( RSF), bayan da su ka kwace iko da fadar shugaban kasa dake cikin birnin a watan Maris. Kakakin rundunar sojan Sudan ya sanar da cewa; Sojojin kasar da dukkanin...
Ministan harkokin wajen Faransa ya kira yi tarayyar turai da ta sake bitar alakarta da Isra’ila saboda ci gaba da kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Gaza da kuma hana shigar da kayan agaji. Matakin na Faransa dai ya biyo bayan na kasashen Spain, Ireland da kuma Holland, da suke son ganin an gudanar...
Kamfanin dillancin labarun ” Mehr” na Iran ya ambato tashar talabijin din ‘aljazira’ tana fadin cewa: ” yawan sojojin da suke kashe kansu, da kuma masu kamuwa da cutukan kwakwalwa yana karuwa.” Majiyar tsaron ‘yan sahayoniya ta tabbatar da cewa; sojojin nasu sun shiga wannan halin ne na kashe kai da tabin kwakwalwa, tun bayan...
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda yake mayarwa da Amurka martani ya bayyana cewa: Ya kamata su daina yin Magana maras ma’ana, fadin cewa Iran ba ta da izinin tace sanadarin Uranium, ganganci ne,domin jamhuriyar musulunci ba ta da bukatar izinin wani mahaluki.” Jagoran juyin musuluncin na Iran wanda...
Zainab Ishaq Muhammad, wadda aka fi sani da ‘Queen Zeeshaq’ za ta shiga daga ciki a ranar Lahadi mai zuwa. Duk da cewa ba a yayata batun auren ba, Aminiya ta tabbatar da ganin katin gayyata da ke nuna za a ɗaura auren nata da angonta, Hussain Muhammad Koya, a ranar 25 ga watan Mayu,...
Da safiyar yau Talata mazauna yankin “al-Daraj’dake Gaza su ka farka daga cikin sanadiyyar harin da jiragen yakin HKI su ka kai wa makarantar ” Musa Bin Nusair” dake karkashin hukumar agaji ta UNRWA” wacce take kunshe da daruruwan ‘yan hijira. Dama dai wannan ba shi ne karon farko da wannan yankin yake fuskantar hare-hare...
Tshouwar Mawakiyar Hausa Hip-Hop, Zainab Ishaq Muhammad, wadda aka fi sani da ‘Queen Zeeshaq’ za ta shiga daga ciki a ranar Lahadi mai zuwa. Duk da cewa ba a yayata batun auren ba, Aminiya ta tabbatar da ganin katin gayyata da ke nuna za a ɗaura auren nata da angonta, Hussain Muhammad Koya, a ranar...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama wasu mutum shida da ake zargi da aikata fashi da makami tare da ƙwato motocin sata guda huɗu, bayan wani samame da suka kai. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun samu nasarar ne a ranar 10 ga watan Mayu, 2025, inda tawaga ta musamman ƙarƙashin...
A yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar bude dandalin hadin gwiwa na Shanghai ko SCO na 2025, game da rage talauci da wanzar da ci gaba, wanda ke gudana a birnin Xi’an, na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin. Cikin sakon na sa shugaba Xi ya bayyana cewa,...
Ya misalta rashin basaraken da cewa, ba rashin ne kawai ga iyalai ko al’ummar masarautarsa ba, a’a rashi ne ga illahirin masarautar Bauchi da ma jihar Bauchi baki ɗaya. Gwamna Muhammad ya misalta Alhaji Garba a matsayin babban basaraken gargajiya wanda aka sani da hikima, tawali’u, da sadaukar da kai ga hidimta wa al’ummarsa....
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da sayen ƙarin motoci guda 10 don taimaka wa sojoji da ’yan sa-kai wajen yaƙi da ’yan Boko Haram da ISWAP. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai Kala-Balge, inda ya gana da ƙungiyoyi daban-daban. An kashe makiyaya 2 a wani hari...
Wasu makiyaya biyu sun rasu bayan da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka buɗe musu wuta a kusa da ƙauyen Tahore, da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos, a Jihar Filato. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da mamatan ke dawowa daga kasuwar Maikatako a kan babur. Yadda ’yan sanda...
’Yan sanda sun bindiga wani wanda ake zargin dan fashi ne har lahira, sa’annan suka kwato bindigogi bakwai a unguwar Maitama da Abuja. Kwamishinn ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, Ajoa Adewale, ya sanar a safiyar Talata, cewa rundunar ta kama gungun wasu mutum bakwai da suka kware wajen aikata fashi d makami da kuma...
Ado Aliero ya shahara wajen kai hare-hare, sace mutane da kashe-kashe a Jihar Zamfara da wasu sassan Arewa Maso Yammacin Nijeriya. An daɗe ana nemansa ba a samu nasarar kama shi ba, saboda ƙungiyarsa na da haɗin kai da goyon baya daga wurare da dama. Ko da yake hukumomin Saudiyya ba su tabbatar da sunayen...

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ba Ta Da Alkiblar Siyasa
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da wani yanki na siyasa mai zaman kansa Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniya ba su da wata kafa ta siyasa mai cin gashin kanta, a maimakon haka dole ne a fahimci matsayinsu...
Hare-haren wuce gona da irin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Gaza tun daga safiyar yau, sun yi sanadiyyar shahadan Falasdinawa da dama tare da jikkatan wasu na daban Rahotonni sun bayyana cewa: Fararen hulan Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu na daban tun daga wayewar garin ranar yau...
Wani harin kwanton bauna da rundunar sojin al-Qassam suka kai kan sojojin mamayar Isra’ila a Beit Lahiya ya yi sanadiyar halaka tare da jikkatan sojojin mamaya masu yawa Rundunar Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta sanar da cewa: Mayakanta sun kai wani kazamin harin kwantan bauna a yankin al-Atatra da ke...
Wasu shugabannin kasashen Yamma suna barazana ga gwamnatin mamayar Isra’ila kan daukan matakan ladabtarwa kanta Shugabannin kasashen Faransa da Birtaniya da kuma Canada sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila da su dakatar da kai farmakin da suke kai wa Zirin Gaza tare da yin barazanar daukar...
Akalla Falasdinawa 38 ne suka rasa rayukansu a wani jerin hare-haren jiragen yaƙin Isra’ila da aka kai a sassa daban-daban na Gaza cikin rabin sa’a da dare, in ji likitocin Falasɗinawa. Rahotanni daga hukumar agajin gaggawa da ke ƙarkashin Hamas sun ce jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hari a wurare da dama, ciki har da...
Gwamnatin kasar Masar na shirin yin arangama ta soji da haramtacciyar kasar Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, musamman tashar talabijin ta 14, sun watsa wani rahoto cewa: Gwamnatin kasar Masar na kokarin karfafa karfinta na soji a tsibirin Sinai, tana mai gargadin abin da ta bayyana a matsayin “yiwuwar rugujewar yarjejeniyar zaman lafiya” da aka...
Ya ce, “Eh, an kama Galadi yau yayin da ake tantance shi da nufin zuwa Saudiyya.” Kama Galadi na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan kama wani riƙaƙƙen ɗan bindiga a sansanin alhazai da ke Abuja. Ana zargin mutumin da hannu a wasu manyan sace-sacen mutane a Jihar Kogi da Abuja. An shiga ruɗani yayin da...
Ta kuma yi kira da a cafke masu safarar mutane tare da fallasa sunayensu bayan an gurfanar da su a gaban kotu, domin daƙile laifi. NiDCOM ta miƙa waɗanda aka ceto ga hukumar NAPTIP domin tantance su da kuma ci gaba da ba su kulawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
Mutane sun koma kwana a cikin jejin a sakamakon hare-haren ’yan bindiga a yankin Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda da ke Jihar Zamfara. Mazauna yankunan sukan dawo cikin gari su yini, idan dare ya yi kuma su shiga daji su kwana, sakamakon ƙaruwar hare-haren ’yan ta’adda, inda suka kashe mutum huɗu suka yi garkuwa da wasu...
Akalla dalibai marasa galihu 300 da ke makarantun gaba da sakandare daga zababbun al’ummomi a kananan hukumomin Edu/Patigi/Moro na jihar Kwara sun samu tallafin karatu don tallafa musu. Da yake jawabi a wajen taron rabon tallafin karatu da aka gudanar a Ilorin, mai taken “Hatsarori na Shaye-shayen Miyagun Kwayoyi Tsakanin Dalibai A Manyan Makarantu”...
Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na horar da matasa sana’o’i daban-daban a fadin kasar nan. Sakataren Ma’aikatar Agaji da Rage Talauci, Dokta Yakubu Adam Kofar Mata, ya bayyana haka, a lokacin da ya kai ziyarar wayar da kan mahalarta shirin “Skill to Wealth” na shiyyar Arewa maso Yamma, wanda aka gudanar a Kano. ...
Gwamnatin jihar Kwara ta kafa tutar hadin kai mai tsayin mita 70 a hukumance, wanda ke zama alamar “hadin kan kasa, tafiya tare da buri a matsayin al’umma”. Da yake jawabi a wani takaitaccen biki a Ilorin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ce jihar ba ta daga tuta kawai ba, a’a tana nuna kwarin guiwar...
An dauke kashin farko na maniyyata 550 daga jihar jigawa zuwa Saudiyya a filin jirgin Nuhu Muhammadu Sunusi domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025. Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan jim kadan bayan tashinsu zuwa kasa mai tsarki. Ya bayyana cewa maniyyatan sun fito ne daga kananan hukumomi...
Dubun wani ɗan bindiga ta cika a yayin da yake shirin shiga jirgi tare da sauran maniyyata aikin Hajji a Jihar Sakkwato. Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kama ɗan ta’addan mai suna Sani Galadi ne a yayin da ake yi wa maniyyata tantancewar ƙarshe kafin hawa jirgi zuwa Ƙasa Mai Tsarki a Filin Jirgi...
Dubun wani ɗan bindiga ta cika a yayin da yake shirin shiga jirgi tare da sauran maniyyata aikin Hajji a Jihar Sakkwato. Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kama ɗan ta’addan mai suna Sani Galadi ne a yayin da ake yi wa maniyyata tantancewar ƙarshe kafin hawa jirgi zuwa Ƙasa Mai Tsarki a Filin Jirgi...
Jami’an tsaron ƙasar Saudiyya sun kama wasu mata biyu da ake zargin cewa mata da kuma mahaifiyar jagoran ’yan bindiga da gwamnatin Najeriya ke nema ruwa a jallo, Ado Aliero, bayan sun je aikin Hajji. An kama matar Aliero da mahaifiyar tasa ne a birnin Madina bayan sun je yin ziyara gabanin fara aikin Hajji....
An shirya sake zama a ranar Alhamis mai zuwa don kammala tattaunawar gaba ɗaya. Cikin waɗanda suka halarci ganawar har da wakilan MOPPAN kamar su Abdul Amart, Nazifi Asnanic, da Abubakar Bashir Maishadda. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, tattaunawar dake tsakanin Iran da Amurka za ta iya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen dandalin tattaunawa na Tehran, Araghchi ya ce kasashen yankin suna goyon bayan tattaunawar da...
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yayi tattaunawa ta wayar tarho mai aramashi da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, inda suka tattauna kan batutuwa da dama ciki har da yunkurin fara tattaunawar tsagaita bude wuta nan da nan tsakanin Rasha da Ukraine. Kamfanin dillancin labaran Rasha na RIA shi ma ya ambato, shugaban Kremlin...
Yemen ta yi barazanar killace babbar tashar jiragen ruwan Haifa ta Isra’ila, tare da gargadin cewa jiragen ruwa da ke tafiya a can. “Dukkan kamfanonin da jiragensu ke nan ko kuma suka nufi wannan tashar, ana sanar da su cewa, ya zuwa wannan sanarwar, an saka tashar cikin jerin wuraren da muke son kaiwa hari,”...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Jihar Kebbi ta amince da naɗin sabbin sakatarorin ƙananan hukumomi guda 21 a faɗin jihar. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Yakubu Bala ya sanya wa hannu, wacce aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi. Ya bukaci sabbin sakatarorin da aka naɗa da su yi...
Mai dakin Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta sake jaddada kudurin gwamnatin jihar na ganin an kawar da tu’ammali da miyagun kwayoyi a fadin jihar. Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta karɓi shugabannin Hukumar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi da Hana Safarar Mutane ta Jihar Zamfara, waɗanda suka kai mata ziyarar...
Jami’an Sashen Binciken Laifuka na Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Nasarawa (SCID) sun kama wani mai garkuwa da mutane a Kasuwar Shinge da ke Lafia, bisa rahotonnin sirri da suka samu. An samu nasarar cafke wanda ake zargin bayan shafe dogon lokaci rundunar na nemasa ruwa a jallo saboda laifuka da dama da suka hada...
Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano da masu shirya fina-finai sun cimma matsaya bayan dakatar da wasu fina-finai 22 da suka haɗa da Labarina da Dadin Kowa, Manyan Maga da Garwashi. An bai wa masu shirya fina-finan wa’adin mako guda daga Litinin 19 zuwa Lahadi 25 ga watan Mayu 2025 domin miƙa fina-finansu don tantancewa...
A kwanakin baya, an dawo da babi na 2 da na 3 masu taken “Wu Xing Ling” da “Gong Shou Zhan” na Rubutun siliki na Zidanku, wato kayan tarihi mai muhimmanci na kasar Sin, ta hanyar hadin gwiwa kan kayan tarihi tsakanin Sin da Amurka. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin...