Gaza : Sabon kisan kiyashi a kusa da wurin rarraba kayan abinci
Published: 2nd, June 2025 GMT
Jami’ai a Falasdinu sun ce akalla mutum 31 ne sukayi shahada sannan wasu sama da 150 sun jikkata, bayan wani hari da Isra’ila ta kai kusa da wurin rabon abinci a birnin Rafah.
Dama shugaban hukumar MDD da ke kula da yan gudun hijirar Falasdinawa, Philippe Lazzarini, ya ce rabon kayan agajin ya zama tarkon mutuwa.
Lamarin dai ya faru ne a kusa da wata cibiyar rarraba kayan abinci da gidauniyar agaji ta Gaza (GHF) ke gudanarwa, wani kamfani mai zaman kansa da ke samun goyon bayan Isra’ila da Amurka da kungiyoyin agaji na kasa da kasa suka yi suka.
Kakakin kungiyar Hamas Sami Abu Zohri yayi Allah wadai da gwamnatin Isra’ila kan harin da ta aikata a rabon kayan agaji a Gaza, Inda ya jaddada cewa an yi wannan kisan kiyashi ne tare da goyon bayan Amurka.
Dangane da wannan kisan kiyashi da zubar da jinin shahidai, ya yi kira ga dukkanin al’ummar musulmi da masu son ‘yanci a fadin duniya da su tashi tsaye wajen yakar masu kisan gillar da sahyoniyawa ke yi.
A wani share kuma kungiyar gwagwarmayar Falasdinawan ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya, da cibiyoyinta, musamman ma kwamitinta na tsaro, da su dauki matakan da suka dace don tilastawa gwamnatin Isra’ila ta kawo karshen zubar da jini da take yi, tare da gaggauta bude mashigar Zirin da aka yi wa kawanya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
MDD Ta Gargaɗi Isra’ila Kan Tilasta Wa Al’ummar Deir al-Balah Na Gaza Tashi
Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce umurnin da sojojin Isra’ila suka bai wa Falasɗinawa na ficewa tsakiyar Gaza, babban koma baya ne ga ƙoƙarin ceton rayukan al’ummar yankin da yaƙi ya ɗaiɗaita.
A ranar Lahadi ne Isra’ila ta umarci Falasɗinawa a Deir el-Balah, da su koma kudancin Gaza saboda ayyukan soji.
MDD ta sake nanata gargaɗin da ta yi cewa al’ummar Gaza da dama na mutuwa saboda yunwa kuma suna buƙatar agajin abinci cikin gaggawa yayin da Isra’ila ke ci gaba da taƙaita shigar da kayan agaji.