2025-11-27@22:25:19 GMT
إجمالي نتائج البحث: 405
«yan takarar»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
An zaƙulo gawarwakin mutane 19 bayan wani jirgin fararen hula da jirgin sojoji sun yi karo a sararin samaniya a ƙasar Amurka. A cikin daren Laraba ne wani jirgin Kamfanin American Airlines dauke da fasinjoji 60 da ma’aikata hudu ya yi karo da wani helikwaftan sojojin Amurka, ƙirar Black Hawk, mai ɗauke da mutane a birnin Washington DC. Jiragen da suka yi karo sun auka a cikin kogin Potomac, inda a halin yanzu ake aikin ceto, tun baya aukuwar hatsarin jiragen daga misalin ƙarfe 9 na dare. Jami’an gwamnati sun tabbatar da cewa jirgin fasinjan na dauke da iyalai da kuma tawagar ’yan wasa Skating, bayan sun kammala atisaye. DR Congo: Sojoji sun ƙaddamar da gagarumin hari kan ’yan tawayen...
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta samu nasarar cafke gungun wasu masu yi wa mayaƙan Boko Haram da ’yan bindiga safarar babura a jihohin Neja da Kaduna. Galibai dai ’yan ta’adda a Arewacin Nijeriya sukan yi amfani da babura wajen gudanar da harkokin sufuri domin sheƙe ayarsu ta garkuwa da satar mutane da kai wa al’ummomi hare-hare. Sojoji sun ƙwato tarin makamai a Zamfara Tankar mai ta sake fashewa a Neja Da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ’yan sanda da ke Abuja a ranar Talatar nan, mai magana da yawun rundunar, Benneth Igweh, ya ce sun samu nasarar ce ta hanyar bayanan sirri, inda suka cafke wasu mutum uku a Ƙaramar Hukumar Suleja ta Jihar Neja. Igweh ya bayyana...
Wani katafaren wurin zubar da shara da aka tanada a wajen Kaduna ya koma wata babbar sana’ar kasuwanci inda ‘yan gwangwan ke amfani da gurbataccen ruwan najasa domin amfanin Noma. Wata Kungiyar ‘yan jarida ta ziyarci al’ummar Katanga da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna inda aka fara gudanar da wannan aiki inda suka gano cewa kimanin ‘yan gwangwan 150 ne suka tsunduma kansu domin karfafa tattalin arziki a wurin da ake jibge sharar. Jama’a na yin tururuwa zuwa wurin zubar da sharar na Katanga wanda shi ne babban wurin da gwamnatin jihar ta amince da sharar don tabbatar da tsaftar muhalli. Mallam Zubairu shi ne shugaba, ya shaidawa tawagar ‘yan jarida da sauran kungiyoyin...
A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar ta samu ci gaba mai inganci wajen zurfafa raya zamanantarwarta a cikin “yanayoyi masu sarkakiya da kalubale” a tsakanin watanni 12 da suka gabata. Ya furta hakan ne yayin gudanar da wata kasaitacciyar liyafar maraba da sabuwar shekara ta kasar Sin. Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya Hisbah Ta Ceto Ƴanmata 16 Daga Hannun Masu Safarar Mutane A Kano Shugaba Xi wanda har ila yau shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC) kuma shugaban kwamitin tsakiya na sojojin kasar ya kara da cewa, “a cikin shekarar dabbar Dragon, mun nuna kuzari da ruhi mai karfi na iya aiwatarwa. Mun...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
