2025-08-02@01:14:10 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1501
«Wannan Hassada»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Dangane da sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayar na cewa za ta maido da yin tambayoyi ga dalibai kafin a ba su biza kuwa, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin ta lura da batun, kuma tana fatan Amurka za ta aiwatar da kalaman shugaba Trump na maraba da daliban kasar Sin da su zo Amurka don yin karatu. Dangane da wani rahoto da wata cibiyar bincike ta kasar Switzerland ta fitar, inda ta bayyana cewa, matsayin karfin yin takara na yankin Hong Kong na Sin ya karu zuwa matsayi na uku a duk fadin duniya, Guo Jiakun ya bayyana cewa, wannan na nuni da matsayin Hong Kong na musamman da kuma alfanun da ake da shi, da kuma...
Kafin wannan, yana riƙe da sarautar Walin Gaya, wanda aka ba shi lokacin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiri sabbin masarautu. Masarautar ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin kare mutunci da ƙimar sarautun gargajiya bisa tsarin da aka gada. Sai dai matakin ya zo ne mako guda bayan Alhaji Usman ya soki gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, kan zarginta da karɓar bashi na dala miliyan 6.6. Gwamnatin Kano ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa ba gaskiya ba ne face tsantsar siyasa. Ko da yake masarautar ba ta danganta ƙwace sarautar da wannan suka da Alhaji Usman ya yi ba, lokacin da aka ɗauki matakin ya haifar da zargi da cece-kuce a tsakanin jama’a. Daga kanmu, magana...
Da take aiwatar da rahotannin sirri cikin gaggawa, rundunar hadin gwiwa da ta kunshi jami’an ‘yansandan Nijeriya, Sojoji, jami’an kula da jama’a na jihar, da ’yan banga na yankin sun bi sawun barayin da suka tsere zuwa Dutsen Falale da ke yankin Kurfi-Safana inda aka yi musayar wuta mai tsanani, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan bindigar 12. Sai dai kuma, yayin da yake yabawa wannan bajinta da jajircewa da jami’an tsaron suka yi, Dakta Mua’zu ya bayyana matukar alhininsa game da rasuwar wani dan banga mai suna Alhaji Danmalam wanda ya rasa ransa a fafatawar. Bugu da kari, soja guda ya samu raunuka kuma a halin yanzu yana samun kulawa a Asibiti. Alhaji Danmalam ya rasu...
Idan dai za a iya tunawa, a baya an kai hari gidan dangin Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 15 ga Afrilu, 2025, ba tare da an kama ko daya daga cikin maharan ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Murdyk ya halarci wasan karshe na gasar cin kofin Uefa Conference League da Chelsea ta doke Real Betis a watan da ya gabata, amma kuma ba a cikin tawagar Chelsea ba, a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, FA ta ce “Za mu iya tabbatar da cewa an tuhumi Mykhailo Mudryk da laifin keta dokar hana kara kuzari, ta hanyar amfani da wani abu da aka haramta, wanda kuma ya sabawa doka ta 3 da 4 a kundin dokokin FA na hana kara kuzari. Zuwa yanzu Chelsea ba ta ce komai ba dangane da tuhumar da akeyiwa Murdyk amma a watan Disamba ta ce, ta na fatan dan wasan nata yayi nasara duba da cewa “Mykhailo ya...
Aiki ceton, ya samu hadin gwiwar kungiyoyin ceto da suka hada da Red Cross da Hukumar Kula da Ruwan Kogin (NIWA) da jama’ar garin Yauri. A ranar Laraba, an yi jana’izar Mutane uku, a garin Hikiya da ke karamar hukumar Rohiya a jihar Neja. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An cimma jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa a taron koli na biyu na kasar Sin da tsakiyar Asiya da aka gudanar a birnin Astana na kasar Kazakhstan a ranar 17 ga watan nan agogon kasar. Shugabannin kasashen biyar na tsakiyar Asiya sun yaba wa kasar Sin a matsayin babbar abokiyar hadin gwiwa kuma kawa ta gaskiya da kasashen yankin tsakiyar Asiya za su iya amincewa da ita har abada. Ana iya sa ran cewa, hadin gwiwar da Sin za ta yi da tsakiyar Asiya ba wai kawai za ta inganta manyan ayyukan hadin gwiwa ba ne, har ma za ta kara karfafa kokarin “neman sabbin abubuwa masu dadi” da “sabbin kirkire-kirkire”, da sa kaimi ga kasashen shida wajen cimma zamanantarwa tare...
Sauran sun hada da: Danjuma Azi, Fwangje Bala Ndat, Salome Tanimu Wanglet, Namba Rimuyat, Nimchak Rims, Ishaku Maren da Paul Datugun. Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, wanda ya tabbatar da kamun, ya ce bincike ya nuna cewa tsaffin ‘yan majalisar sun shafe watanni shida ne kawai a kan karagar mulki, sannan gwamnatin jihar ta siya musu motocin alfarma. Bincike ya kuma nuna cewa, motocin da aka ce kudinsu ya kai Naira biliyan 2.5. Bayan sun sauka akan mukaminsu, sun tafi da motocin kuma duk kokarin da aka yi na su dawo da su, lamarin ya ci tura. Sai da gwamnatin jihar ta sake sayo wa ‘yan majalisar na yanzu motocin da kudinsu ya kai kimanin...
An gayyaci shugaban kasar Sin Xi Jinping zuwa kasar Kazakhstan, daga ranar 16 zuwa 18 ga watan Yunin shekarar 2025, don halartar taron koli karo na biyu na Sin da tsakiyar Asiya. A karshen ziyarar, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi wa manema labarai karin haske game da lamarin. Wang Yi ya ce, babban abin da ya fi daukar hankali a wannan taro shi ne sanarwar da shugaba Xi Jinping ya yi ta “Ruhin Sin da Tsakiyar Asiya”. Inda shugabannin kasashen yankin tsakiyar Asiya suka amince baki daya kan kiyaye wannan ruhi, da inganta tsarin kasar Sin da tsakiyar Asiya don samun sabon babban ci gaba. Bugu da kari, dangane da halin da ake ciki a yankin...
Don girmama ziyarar shugaban ƙasa, gwamnatin jihar ta ayyana ranar Laraba a matsayin hutu domin bai wa mazauna yankunan damar halarta taron da kuma bin diddigin abubuwan da suka shafi ziyarar. Wannan ita ce ziyarar farko da Tinubu ya kai Jihar Benuwe tun bayan da rikicin ya ƙara tsananta. Jama’a da dama na kallon wannan ziyara a matsayin gwada gwamnati kan yadda za ta shawo kan matsalolin tsaro, musamman a jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, rikicin makiyaya da na ƙabilanci. Kisan da aka yi a Yelwata, wanda shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-haren, ya janyo suka damuwa a faɗin ƙasar tare da ƙara matsin lamba ga shugaban ƙasa da ya ɗauki matakin gaggawa don tabbatar...
A yayin shari’ar, jami’in ‘yansanda ASP Luka Sadau, ya bayyana cewa wasu daga cikin kwamitin Masallacin ne suka kama Usman a ranar 13 ga watan Yuni, sannan suka kai shi ofishin ‘yansanda. Ya ce bayan sallar Juma’a, Usman ya sace takalma da kuɗinsu ya kai Naira 100,000. Usman ya kuma amsa cewa yana yawan zuwa Masallaci a ranakun Juma’a domin satar takalma, sannan ya sayar da su a kasuwannin Monday Market da Maraban Rido. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Da farko mun ɗauka yana wasa ne, amma kafin wani ya kai ɗauki, ya riga ya kunna wa kansa wuta.” Wata mazauniyar yankin, Aisha Salisu, ta ce yana matashin yana shaye-shaye. “Ba ya cikin hayyacinsa. Ana jin warin wani abu mai ƙarfi a jikinsa, kuma yana karkarwa da ihu,” in ji ta. Mutane sun yi ƙoƙarin taimaka masa. Wasu sun ja shi zuwa cikin ruwan da ke wata magudanar ruwa a gefen hanya, amma wutar ta riga ta yi masa ƙone sa. “Abun ya zama kamar fim kuma mai ban tsoro,” in ji wani direban adaidaita sahu mai suna Ibrahim Jafar. “Ko bayan da suka jefa shi cikin ruwan, wutar ba ta daina ci nan take ba. Fatar jikinsa duk...
Kasar Sin ta cimma nasarar aikin gwajin tserewa lokacin da ake gamu da matsala a matakin farko na harbar kumbo mai dauke da mutane na “Mengzhou” a yau Talata, a cibiyar harbar taurori dan Adam dake birnin Jiuqiu, abin da ya alamanta cewa, Sin ta cimma sabuwar nasara a aikin binciken duniyar wata tare da kumbo mai daukar mutane. Wannan ita ce nasara irinta ta biyu da Sin ta samu a wannan bangare, bayan shekaru 27 da suka gabata, da samun nasara ta farko a aikin gwajin da ta gudanar a shekarar 1998. Aikin gwajin tserewar da aka gudanar ya kasance muhimmin mataki na ba da tabbaci ga rayukan ’yan saman jannati, wato idan an gamu da hadari ko matsala...

Majalisar Wakilai Ta Fara Binciken Yadda Aka Raba Naira Tiriliyan 1.12 Kan Shirin Lamuni Ga Manoma Da Masana’antu
Kwamitin Majalisar wakilai mai kula da samar da abinci mai gina jiki da tattalinsa ya fara bincike kan yadda aka kashe Naira Tiriliyan 1.12 na shirin Ba da Lamuni na Anchors. Har ila yau, binciken ya shafi yadda cibiyar NIRSAL’s ta raba Naira biliyan 215 na ayyukan noma da kuma yadda Bankin Masana’antu (BOI) shi ma ya raba Naira biliyan 3 ga kananan manoma 22, 120 ta shirin AVCF. An Gudanar Da Bikin Mu’amalar Jama’a Da Al’adu A Tsakanin Sin Da Tsakiyar Asiya A Astana Sin Ta Fara Aiwatar Da Matakin Soke Haraji Kan Kayayyakin Kasashen Afirka 53 Da yake jawabi a zaman binciken, shugaban kwamitin Hon. Chike Okafor, ya bayyana damuwarsa cewa, a cikin cibiyoyin hada-hadar kudi 24 da...
“Na ce Shettima ɗanmu ne, kuma muna alfahari da shi. Na kuma gode wa Tinubu bisa yadda ya bai wa ‘yan Arewa maso Gabas muƙamai masu gwaɓi kafin na nemi a mara masa baya,” in ji Salihu. A lokacin taron, wasu matasa sun kusan kai masa hari, amma ya ce hakan ya faru ne saboda wasu ba su fahimci abin da ya yi ba. Ya kuma jaddada cewa a tsarin jam’iyya, mutum ɗaya ne kawai ake zaɓa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a lokacin zaɓen fidda gwani, kuma shi ne ke da ‘yancin zaɓar mataimakinsa. “Ba a daidaita tikitin shugaba da mataimaki a zaɓen fidda gwani. Ɗan takara kawai ake zaɓa, kuma yana da ‘yancin zaɓar wanda zai mara...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karancin kayan ganyayyaki na cigaba da barazana ga lafiyar ‘yan Najeriya. Masana sun bayyana cewa akwai gibi mai girma na rashin kayan ganyayyaki da ya kamata cike. Sai dai hakan na fuskantar tasgaro sakamakon wasu dalilai. NAJERIYA A YAU: Dalilan Durƙushewar Sababbin Sana’o’i Tun Ba A Je Ko’ina Ba DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan matsala da zummar nemo hanyoyin magance ta. Domin sauke shirin, latsa nan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen kasar Rwanda Olivier Nduhungirehe ya bayyana cewa, kwakkwaran zumunci da ake sadawa a aikace a tsakanin Rwanda da kasar Sin na yin tasiri mai kyau ga al’ummar Rwanda. A cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yayin bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na hudu (CAETE) da aka gudanar daga ranar 12 zuwa 15 ga watan Yuni a birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, Nduhungirehe ya kara da cewa, “Muna da kyakkyawar alaka da kasar Sin.” Ya yi karin haske game da hadin gwiwa mai fadin gaske a tsakanin kasashen biyu a fannonin kiwon lafiya, ilimi, aikin gona, fasaha da makamashi. Yana mai cewar, “Muna...
Ƴansandan jihar Kogi sun tabbatar da sace wani basarake mai suna Samuel Ajayi Bello yayin da yake aikin gona a gidan gonarsa na Ponyan da ke kan titin Ponyan-Irele, a ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas. Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, SP William Aya, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da ƙarfe 10 na safe a ranar Litinin. Ya kuma ce Kwamishinan ‘yansandan jihar ya tura rundunar ta musamman don taimakawa wajen gudanar da bincike da kuma ceto wanda aka sace. Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka Ƴan Bindiga Sun Kai Farmaki Kwara, Sun Kashe Mutum 1, Sun Ƙona Gidaje Shugaban ƙungiyar ci gaban yankin Ponyan, Hon. Banjo Fabola, ya tabbatar da cewa an...
Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47. Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen yaƙi — Netanyahu Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan siyasa ta satar kuɗi — EFCC Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga ya raba wa manema labarai a ranar Litinin. Kakakin ya ce an gaggauta kai jamin asibiti domin a ceto rayuwarsa amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya riga ya yi halinsa....
Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47. Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen yaƙi — Netanyahu Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan siyasa ta satar kuɗi — EFCC Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga ya raba wa manema labarai a ranar Litinin. Kakakin ya ce an gaggauta kai jamin asibiti domin a ceto rayuwarsa amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya riga ya yi halinsa....

Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Wanzar Da Bunkasar Masana’antu A Nahiyar Afirka, In Ji Wani Masanin Tattalin Arziki
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan ya nuna ragin hauhawar farashi a faɗin ƙasar nan. Masana na ganin wannan ragi a matsayin alamar ci gaba ga tattalin arziƙi, sai dai har yanzu ‘yan Nijeriya da dama na fama da tsadar rayuwa, musamman wajen samun kayan abinci da wasu muhimman abubuwan buƙara na yau da kullum. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Sojojin Isra’ila Sun Kashe Kananan Yara Masu Yawa A Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kashe adadi mai yawa na yaran Iran a cikin ta’addancin da suke yi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe kananan yara masu yawa na Iran a cikin wannan ta’asa da take gudanarwa kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A cikin wani sako da Ismail Baqa’i ya rubuta a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana cewa: “Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe adadi mai yawa na yara Iraniyawa tare da kai hari kan asibitin yara a tsawon kwanaki uku na hare-haren soji kan Iran. Kamar yadda Ya’ir Golan, tsohon mataimakin hafsan hafsoshin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya amince da cewa: Kashe...
A cikin wata wasika mai kwanan wata 23 ga Mayu, 2025, mai lamba CR/3000/IGP-SEC/MU/ADM/14/ABJ/VOL 118/57, wacce aka aike wa sakataren gwamnatin jihar Kano, na cewa, IGP ya bukaci a mika Bature zuwa gaban wani jami’i, SP Mojirode B. Obisiji a ranar Alhamis 29 ga Mayu, 2025, domin amsa tambayoyi. In ba a manta ba, IGP a watan Disamba, 2024 ya ba da irin wannan umarni tare da tura jami’an sa ido na IGP domin su kamo mai magana da yawun Gwamnan Kano tare da kai shi hedikwatar rundunar da ke Abuja. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Garkuwan sararin samnaiyar kasar Iran a lardin Zanjan ya bada labarin kakkabo jiragen yakin na HKI guda biyi wadanda ake sarrafasu daga nesa a sararin samaniyar. Kamfanin dillancin lbaran Tasnim na sojojin kasar Iran ya nakalto majiyar dakarunn juyin juya halin musulunci na kasar Iran tana fadar haka. Labarin ya kara da cewa rubuce rubucen da aka rubuta a jikin jiragen da aka tarwatsa sun bayyan cewa kirar kasar Amurka ce. Wannan yake tabbatar da irin hannun da Amurka take da shi a cikin yakin da Iran take fafatawa da HKI. A wani labarin kuma yansandar yanar gizo sun kama mutane biyu wadanda suke yada labaran karya dangane da yaki da kuma shuwagabannin kasar. Har’ila yau an kama wasu wadanda...

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce Ba’a Rufe Kofar Diblomasiyya Ba, Matukar HKI Ta Dakatar Da Kaiwa Kasar HKI
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyaana cewa kasarsa bata rufe kofar diblomasiyya dangane da shirinta na makamashin Nukliya ba, matukar HKI zata dakatar da hare-haren da take kaiwa kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Lahadi a taron yan jaridun da ya kira a birnin Tehran. Ya kuma kara da cewa Iran tana son ta ci gaba da shirinta na makamashin Nukliya ta zaman lafiya ta hanyar diblomasiyya idan an bata damar yin haka. Ministan ya ce ikidar JMI ne warware dukkan matsaloli da farko ta hanyar Diblomasiyya, da kuma tattaunawa amma ba zamu taba amincewa wani ya hanamu hakkimu na mallakar makamashi nukliya ta zaman lafiya ba....
Bisa la’akari da haka, a fili kasar Sin tana adawa da matakin da Isra’ila ta dauka na keta dokokin kasa da kasa, inda ta kai wa kasar Iran hari, lamarin da ba za a amince da shi ba, musamman ma ta la’akari da yadda kasashe daban daban ke ci gaba da neman hanyar daidaita batun nukiliyar kasar ta Iran ta hanyar siyasa. Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta bukaci Isra’ila da Iran da su warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari, da lalubo bakin zaren kasancewa tare cikin kwanciyar hankali da lumana. (Bello Wang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Jam’iyyar APC a Yankin Sanatan Kaduna ta Arewa (Zone 1) ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, don sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu. An yanke wannan shawara ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Jami’ar Tarayya ta Ilimi da ke Zaria, inda tsoffin gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisa, da kwamishinoni da shugabannin hukumomi na tarayya da jiha suka halarta. EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Zargi Aikata Damfara A Intanet A Kaduna An Karrama Dalibar Kaduna Da Ta Zo Ta Biyu A Gasar Karatun Alkur’ani Ta Duniya Masu ruwa da tsakin sun jero nasarorin da gwamnati mai ci ƙarƙashin APC...
Wani jami’in ɗan sanda, SP Mustapha Garba Gumau, ya yi gamo ajalinsa a wani hatsarin mota yayin da ya rage aƙalla sa’a ɗaya a ɗaura masa aure. Aminiya ta ruwaito cewa, ajali ya katse hanzarin jami’in ne a kan hanyar Gumau zuwa Magaman-Gumau da ke Ƙaramar Hukumar Toro ta Jihar Bauchi, inda za a ɗaura masa aure. Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikacin Jami’ar Northwest a Kano HOTUNA: Yadda aka yi sulhu da ƙasurgumin ɗan fashin daji Ado Aliero a Katsina SP Gumau wanda hatsarin ya rutsa da shi da abokansa ya rasu ne da misalin ƙarfe 9 yayin da ake shirin ɗaura masa aure da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Asabar. Wata sanarwa da mai magana da yawun...

Iran Ta Sanar Da Dakatar Da Tattaunawa Da Amurka A Wannan Lokaci Da Take Fuskantar Yaki Daga Isra’ila
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Babu wata tattaunawa da zata yi da Amurka a halin da take ciki na kare kanta A yayin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan yankunan kasar Iran, a hukumance Iran ta bayyana rashin yiwuwar ci gaba da zaman tattaunawa da Amurka kan batun shirinta na makamshin nukuliya, tare da dora wa Amurka alhakin abin da ke faruwa kai tsaye. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Akwai hadin kai tsakanin haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka wajen kai hare-hare kan kasar Iran domin rusa zaman tattaunawar nukiliya da haka ke bayyana kawar da duk wata magana ta hakikanin aniyar Amurka na samar da hanyar warware takaddamar Shirin Iran...
Kungiyar ‘Abokan Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya’ ta yi Allah wadai da harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan Iran Kasashe mambobin kungiyar aminan yarjejeniyoyin Majalisar Dinkin Duniya sun fitar da wata sanarwa ta musamman inda suka yi kakkausar suka kan wuce gona da irin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Sanarwar ta yi la’akari da harin hadin gwiwa ta sama da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar a ranar 13 ga watan Yuni a kan wasu wurare da dama a Iran, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da jikkata wasu daruruwa da suka hada da mata da kananan yara da masana kimiyya, matakin da ya saba wa Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya da muhimman ka’idojin dokokin...
Sannan shi ne ya fi kowanne danwasa yunkurin cin kwallo a gasar, inda ya kai hari (attempt) sau 64, 23 daga cikinsu akwai munana (on target) 23. Ya yi nasarar yanka abokan hamayyarsa har sau 62, sannan ya yi bugun kwana 45. Rapinha Zakakurin danwasan gaba na Barcelona da Brazil, Rapinha, na cikin ‘yanwasan da suka fi bai wa mabiya harkokin wasa mamaki a kakar wasa ta bana baki daya – ba a Champions League ba kawai. Tare da dan wasan kungiyar Borussia Dortmund, Serhou Guirassy, su ne kan gaba a cin mafi yawan kwallaye da 13 kowannensu. Sai dai Rapinha ya zarta shi da yawan bayar da kwallo a zira a raga, inda yake da guda 9, Guirassy...
Wakilin dindindin na kasar Sin a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ko IAEA Li Song, ya ce kasarsa na matukar Allah wadai da harin Isra’ila kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar Iran da ake amfani da su domin ayyukan zaman lafiya. Li Song, ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, yayin taron manyan jami’an majalisar gudanarwar hukumar ta IAEA, game da batun hare-haren da Isra’ila ta kaddamar kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar Iran. Ya ce, har kullum Sin na mayar da hankali ga zakulo matakan wanzar da zaman lafiya, dangane da batun nukiliyar Iran ta hanyoyin siyasa da diflomasiyya, tana kuma adawa da kakaba takunkumai ba bisa ka’ida ba daga bangare guda. Har ila yau, Sin za ta ci gaba da...

Za A Watsa Shirin “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” A Kafofin Watsa Shirye-shiryen Kasashen Tsakiyar Asiya Biyar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Semenyo ma ya taka rawar gani saboda kwallo biyun da ya ci a wasan karshe sun sa ya ci wa kungiyarsa Bournemouth kwallo 11 kenan a karonfarko. Danwasan Najeriya Aled Iwobi ya fi abokan wasansa kokari a Fulham da kwallayensa tara da ya ci da kuma taimakawa wajen cin shida, sannan ya dan dara Amad Diallo na Manchester United (wanda ya ci takwas kuma ya bayar aka ci shida). Amma Iwobi ya fi shi buga wasanni saboda Diallo ya yi jinyar wajan watanni uku a kakar da ta gabata. Iwobi ne dai kan gaba wajen kirkirar damarmaki (59) da kuma bayar da cikakken fasin (508) a cikin bangaren abokan hamayya, inda shi kuma. Thomas Partey na Ghana ya fi yawan...
Kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, ta gudanar da taron shekara-shekara na biyu, na hukumar zartaswar cinikayyar hidimomi a birnin Geneva dake kasar Switzerland a jiya Juma’a, inda bangaren Sin ya yi nuni da cewa, matakin Amurka game da harajin kwastam na tattare da rashin fahimta da rashin gaskiya a wasu fannoni, don haka ya bukaci bangaren Amurka da ta bi ka’idojin kungiyar WTO, da daidaita matsaloli ta hanyar yin hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban, da dakatar da daukar matakai daga bangare daya, don tabbatar da tsarin ciniki na duniya tare da bangarori daban daban. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar, ta yi tir da harin na Isra’ila akan Iran tare da bayyana cewa, ya haifar da rikici a tsakanin bangarorin biyu da kuma musayar harba makamai masu linzami. Gwamnatin ta Najeriya ta nuna bakin cikinta akan abinda ya faru, tare da kuma da yin kiran a tsagaita wutar yaki da gaggawa, da kai zuciya nesa. Har ila yau, sanarwar ma’aikatar harkokin wajen ta Nigeria wacce kakakinta Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya rattabawa hannu a yau Asabar,14 ga watan Yuni 2025, ta jaddada cewa; yaki ba zai maye gurbin tattaunawa ba, kuma hanyar diplomasiyya ce za ta kai ga samar da zaman lafiya mai dorewa, girmama juna da aiki da dokokin kasa...
Mai magana da yawun hukumar da take kula da filin saukar jiragen sama ta Ben Gorion ta sanar a yau Asabar cewa an rufe filin saukar jiragen saman har zuwa wani lokaci a nan gaba, bayan da aka dauke dukkanin jiragen sama zuwa kasashen Cyprus, Greece da kuma Amurka. Mai Magana da yawun hukumar filin saukar jiragen saman na Ben Gorion Lisa Daiper ta bayyana ce; Babu wani lokaci takamaimai da aka tsayar domin sake bude filin saukar jiragen saman na Ben Gorion.” A gefe daya jaridar “Maariv’ ta bayyana cewa; An dauke dukkanin jiragen sama zuwa filayen jiragen saman a kasashen turai. Haka nan kuma ta kara da cewa; An dauki 14 daga cikin jiragen saman na HKI zuwa...
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda ya tattauna ta wayar tarho da jami’ar harkokin waje ta tarayyar turai ya bayyana cewa, ci gaba da tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka ba shi da wata ma’ana, kamata ya yi jami’an tarayyar turai din su yi Allawadai da wuce gona da irin HKI akan Iran. Da safiyar yau Asabar ne dai jami’ar diplomasiyyar ta turai Kaja Kallas ta kira yi minsitan harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci inda su ka tattauna halin da ake ciki a yammacin Asiya da ya hada da harin da HKI ta kawo wa Iran. Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana harin na HKI da cewa, wuce gona da iri ne da...
Na’urorin kakkabo jiragen sama na Iran sun kakkabo jirgin sama na HKI samfurin F-35 a yammacin kasar, wanda shi ne karo na uku a cikin sa’oi 24. Kamfanin dillancin labarun Tasnim ya nakalto majiyar tsaro na cewa; dakarun kare samaniyar jamhuriyar musulunci sun harbo jirgin sama samfurin F-35,kuma matukinsa ya fito ta hanyar amfani da lemar ceto. Bayan wani lokaci daga faduwar jrigin da kuma fitowar matukinsa daga ciki, sojojin kasa na jamhuriyar musulunci ta Iran sun kama shi. A jiya Juma’a ma dai daakrun kare sararin samaniyar jamhuriyar musulunci ta Iran, sun kakkabo jiragen saman na ‘yan sahayoniya wadanda kirar Amurka ne, kuma daya daga cikin jiragen yakin da take alfahari da su. Shi dai jirgin yakin na Amurka...
Ma’aikatar Gona da tsaron abinci ta ƙasa ta dakatar da shirinta na gudanar da addu’a da azumi na kwanaki uku, bayan martani mai zafi daga jama’a. Tun da farko, an tsara addu’ar ne domin neman taimakon Ubangiji wajen tabbatar da tsaron (wadataccen) abinci a Nijeriya. Wata takarda da ta bayyana ga jama’a, wadda Daraktar Gudanarwa ta Ma’aikatar, Mrs. Adedayo Modupe O., ta sanya wa hannu, ta gayyaci daraktoci da sauran manyan ma’aikata domin halartar wannan taron addu’a a shalƙwatar ma’aikatar a Abuja, a ranakun 16, 23 da 30 ga Yuni, 2025. Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Addu’ar Kwana 3 Don Samun Isasshen Abinci Wani Gidan Gona A Jihar Ogun Zai Fitar Da Tarwada Ta Kimanin Naira Biliyan Shida A 2025...
Bugu da kari, akwai kuma masu kiwon Tarwada a gonar da sama da su 600, wadanda aka rage yawan adadinsu daga 1,327 zuwa 600, bayan bullar cutar annobar Korona, saboda kalubalen ci gaba da gudanar da sauran ayyukan gonar. A shekarar 2024, masu kiwon Tarwadar a gonar; sun samar da Tarwadar da yawanta ya kai kimanin tan 1,700, wadda kuma aka kiyasata cewa; kudinta ya kai na Naira biliyan 4.5. Wannan ba karamin ci gaba ba ne, musamman duba da cewa; gonar ta kasance abin koyi ga sauran kungiyoyin da ke kiwon Tarwada a daukacin fadin wannan kasa. Bisa wannan nasarori da gonar ta samar, hakan ya nuna yadda take ci gaba da samun yabo daga kasashen duniya, cikin masu...
Ya yabawa hukumar bisa yadda ta aiwatar da dokar da ta ba da damar, ‘Dokar Ci Gaban Man Fetur da Gas ta Nijeriya (NOGICD) ta 2010. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kwamandan sararin samaniya na dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Janar Amir Ali Haji Zadeh yana cikin wadanda su ka yi shahada sanadiyyar harin da sojojin HKI su ka kawo wa da asubahin yau Juma’a. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto majiyar juyin juya halin musulunci ta Iran tana tabbatar da shahadar Janar Amir Ali Haji Zadeh.
Yayin taron shekara-shekara na tattaunawar CBD na shekarar 2025 da aka rufe a yau Juma’a 13 ga wata, mashawarci kana kwararre a hukumar kasuwancin kasar Sin ta kasar Birtaniya, kuma shugaban cibiyar bunkasa kasuwanci tsakanin Birtaniya da Sin mista John Mclean, ya bayyana yayin da yake hira da wakilin CMG cewa, kasuwar kasar Sin tana cike da damammaki, don haka dole ne ya shiga a dama da shi a cikinta. A ganinsa, yayin da ake tinkarar tashe-tashen hankula da rashin tabbaci a duniya, babbar baiwar da Sin take da ita, da muhalli mai aminci da bude kofa ga kowa, sun samarwa kamfanonin Birtaniya da ma duniya baki daya damammaki. Tun bayan kafuwarsa a shekarar 2000 zuwa yanzu, taron ya kasance...
Ya ce Jihar Kurus Ribas ita ce ta farko a yankin kudu da ta shiga a dama da ita a harkar noman alkama, lamarin da ke nuni da gayar nasara wajen samar da abinci a kowani sassa na kasar nan. Kyari ya kara da cewa shirin rabar da takin zamani ya taimaka wajen bunkasa samar da shinkafa zuwa tan 58,000, lamarin da ya bai wa gwamnatin tarayya sanya tallafi a bangaren rabar da shinkafa ga jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa. Ministan ya ce akwai bukatar kare masu amfani da kuma kayan da ake nomawa, “kaso 80 cikin 100 na abincinmu manoman cikin gida ne suka samar da su.” A daidai gabar da ake hasashen adadin ‘yan Nijeriya zai kai...
Lamarin ya ci gaba da raguwa har zuwa 2024, inda yawan kudaden da ake kashewa a yawon ketare ya fadi da kaso 14 a matakin shekara-shekara zuwa dala biliyan 2.66. Hakan na nuni da cewa ‘yan Nijeriya sun rage kashe kudaden da suke kashewa kan safarar jiragen sama da dala biliyan 1.12 ko kuma kashi 30 cikin dari a cikin shekaru biyun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya umurci jami’an tsaro su gaggauta kai dauki ba tare da bata lokaci ba don tabbatar da an gurfanar da masu laifin a gaban kuliya, yana mai jaddada cewa za a hukunta duk wanda aka samu dauke da muggan makamai ko kuma aka samu yana da hannu wajen aikata laifuka. “Ga iyalai da ‘yan uwa da masoyan marigayi Ahmed, ina mika sakon ta’aziyyata, da na gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, kuma muna jimami tare da ku, ina ba ku tabbacin za a yi adalci. “Ina kuma kira ga jami’an tsaro su kara kaimi wajen tattara bayanan sirri da kuma sintiri kan tituna, musamman a wuraren da ke fuskantar irin wadannan laifuka. Jama’armu sun cancanci tafiya cikin walwala ba tare da...
A cewar Bawa, gwamnatocin da a karkashinsu aka wawashe dukiyar kasa, su ne na Mulkin Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo (daga 1999 zuwa 2006), sai Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua (daga 2007 zuwa 2009), kazalika a mulkin Shugaba Goodluck Jonathan daga (2010 zuwa 2014), sai kuma mulkin Muhammadu Buhari (daga 2015 zuwa 2023). Wadannan bayanai na kunshe cikin littafin, ‘The Shadow Of Loot and Loss – Uncobering Nigeria’s Petrol Subsidy Fraud,’ wanda tsohon sarkin yaki da cin hanci da rashawa ya rubuta. Alkaluman da Bawa ya bayyana daga cikin gwamnatocin hudu, shugaba Buhari ne ke kan gaba wajen biyan tallafin da ake ta cece-kuce akai na Naira tiriliyan 11, sai kuma na Jonathan wanda ya kashe Naira tiriliyan 3.9. Gwamnatin...
Da yake nasa jawabin, Sangare ya ce, Nijar na bin manufar Sin daya tak a duniya, kuma tana ba da fifiko ga hadin gwiwarta da kasar Sin, da mayar da hankali sosai kan harkokin tsaro, kana tana son kara amincewa da juna, da ci gaba da yin shawarwari bisa mutunta juna a tsakaninsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa: Sabon Tunani Don Wanzar Da Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya
A wannan lokaci da wasu sassa ke kafa shingaye, GCI na gina gadoji. Manufar na kuma karfafa gwiwar tattaunawa, da gudanar da shawarwari tsakanin sassan duniya masu bambance-bambance, ta yadda za a kafa managarcin tsarin hadin kan bil’adama mai dorewa. GCI da ranar tattaunawa tsakanin wayewar kan kasa da kasa ta MDD, za su kara zamewa duniya muhimman manufofi na “tafiya tare a tsira tare”!(Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Baya ga haka, Sojojin sun kashe ƙarin ‘yan ta’adda goma da suka taru kusa da wani gidan mai a Danjibga, waɗanda ake zargin sun kasance cikin wata tawagar da Dogo Sule ya tara domin kitsa hari. Manjo Janar Kangye ya jaddada cewa rundunar Soji za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma gaba ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Manjo Janar Hussain Salami ya fada a yau Alhamis cewa; Abokan gaba suna yi mana barazana da yaki, sannan ya tabbatar da cewa a shirye suke su fuskanci duk abinda zai faru. Manjo janar Salami wanda ya gabatar da jawabi ga taron dakarun sa-kai na “Basiji a nan Tehran ya kuma kara da cewa; Babu wani wuri komai zurfi da nisansa a HKI da ba mu tsinkayowa, idan kuwa aka ba mu umarni to za su yi nasara, mu Sanya abokin gaba ya yi nadama. A gefe daya ministan tsaron Iran ya bayyana cewa; Duk wani hari da ake tunanin kawo wa Iran, to kuwa zai fuskanci mayar da martani mai...
Jami’in tafiyar da sha’anin Mulki a yankin Cape ya fada a jiya Laraba cewa; An sami karuwar wadanda su ka rasa rayukansu ya karu zuwa 49. Shugaban tafiyar da sha’anin Mulki a yankin na garin Cape, Oscar Mobyan ya bayyana haka ne a wani taron manema labaru,kamar yadda kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto. Wasu yankuna na kasar ta Afirka Ta Kudu sun fuskanci saukar ruwa kamar da bakin kwarya, haka nan kuma saukar kankara, da hakan ya sa aka shiga cikin yanayin sanyi mai tsanani da kuma yankewar wutar lantarki a wasu yankunan. Ambaliyar ruwan da aka samu a kusa da wata makaranta ya ja motar da take dauke da dalibai 13, da hakan ya yi sanadiyyar rasuwarsu. Tuni...
A cewarsa, gobarar na iya kasancewa ta samo asali ne daga wani gini da ke bayan gidan man. Rahotanni sun nuna cewa gobarar na iya tashi ne daga tankunan mai da ke ƙasa, kafin ta bazu zuwa cikin gidan man gaba ɗaya. Hukumar kashe gobara ta jihar ta yi gaggawar killace wajen domin hana cunkoso da tabbatar da tsaron jama’a yayin aikin kashe gobarar. Mai magana da yawun hukumar kashe gobarar, Shakiru Amodu, ya tabbatar da cewa an samu nasarar kashe gobarar kafin ta bazu zuwa gidajen da ke kusa. Kafin ƙarfe 6 na yamma, jami’an agajin gaggawa sun shawo kan lamarin gaba ɗaya, tare da killace yankin da abin ya shafa domin kaucewa wata barazana. Daga kanmu, magana...

Ministan Tsaro Na Kasar Iran ya bada Labarin Gwajin Wani Sabom Makami Mai Limzami Mai Daukar abubuwan Fashewa Har Ton Biyu
Ministan tsaro na kasar Iran ya bayyana cewa sojojin kasar sun yi gwajin wani makami mai linzami wanda yake iya daukar abubuwan fashewa hart un biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Burgediya Janar Amir Nasirzade yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa . wannan gwajin sako ne ga gwamnatin Amurka da kawayenta. Idan wani ya dora mana yaki sai sun fi mu shan wahali. Don tare da wadannan shirye shiryen da kuke na kare kammu sai mun kori amurka daga yankin nan. Yace iran tana cikin fushi kan abinda yake faruwa a Gaza don haka duk wata dama da ta samu zata maida martanin da ya dace. Ministan ya bayyana haka ne a jiya Laraba...
Ya ce ya fahimci haka ne bayan kallon wani shiri a talabijin inda ya ga wasu mutane na nuna rashin jin daɗi. Wike ya ce wannan baƙin ciki na su shi ne ke ba shi ƙwarin gwiwa. “Na ji wani irin abu a zuciyata, sai na kunna talabijin. A nan ne na gano cewa wasu na cikin baƙin ciki saboda abubuwan alheri da ake yi,” in ji shi. Ya ƙara da cewa: “Yanzu da na gane suna cikin baƙin ciki, zan ci gaba da sanya musu ƙarin ciwon zuciya. Farin cikinmu na ƙaruwa ne da jin haushinsu. Wannan shi ne sabon aikina na ci gaba da sa musu hawan jini.” Wike ya yi raha da cewa yayin da suke cikin...
Wani ɗan ƙasar Indiya, Harpal Singh, ya rasa ransa bayan katangar rumbun ajiya ta kamfanin ATCO da ke Zariya ta rushe a kansa ranar Talata. Mutumin dai daya ne daga cikin ma’aikatan kamfanin da ke unguwar Cikaji a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna. Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa Alhazai Ana shirin mayar da rantsar da Shugaban Nijeriya zauren majalisa Wani ma’aikacin kamfanin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyanawa Aminiya cewa Ba’indiyen ya gamu da ajalinsa ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren Talata, bayan tashin guguwa gabanin a fara ruwan sama. Ma’aikacin ya ce sai dai ba a san musabbabin rushewar katangar ba, sakamakon lokacin da lamarin ya faru ba lokacin...
Aƙalla jihohi 11 na Najeriya sun kashe sama da Naira biliyan 6.2 wajen tallafa wa Alhazansu domin sauƙaƙa musu wajen zama a ƙasar Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin 2025. Wannan tallafi ya haɗa da kuɗi, jakunkunan tafiya, da kuma sayen raguna na hadaya domin sallar Layya. Tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka cikin shekaru uku masu zuwa — Bankin Duniya Dalilin da babu abin da gwamnatin NNPP ta taɓuka a Kano — APC Gwamnatin Jihar Sakkwato ce ta fi kowa bayar da tallafi mafi yawa, inda Gwamna Ahmed Aliyu, ya bai wa kowane daga cikin alhazai 3,200 na jihar Riyal 1,000 (kimanin Naira 450,000). A Kano kuwa, kowane alhaji daga cikin alhazai 3,345 sun samu kyautar Riyal 50. Gwamnatin Jihar...
Binciken ya nuna cewa, mutum biyu daga cikin wadanda ake zargin ma’aikatan Dangote ne kai tsaye, yayin da sauran ke aiki da kamfanonin da ke da alaka da safarar mai daga matatar Dangote zuwa wuraren ajiya na kamfanin da ke Ibese da Obajana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Sake Tunzura Iran Shirin Makamashin Nukiliyarta Zai Fuskanci Martani
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Sake kunna ‘hanyar tayar da hankali’ zai gamu da martani mai ƙarfi na Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Fitar da kudiri kan Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta yi ba zai shafi kudurin al’ummar Iran ba ko kuma ci gaban shirinta na makamashin nukiliya na zaman lafiya. A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Iran a yammacin ranar Talata, Baqa’i ya yi la’akari da dukkanin rahotanni da kudurorin da suka shafi siyasa. Ya kuma kara da cewa Iran ba ta keta hurumin da ya rataya a wuyanta ba, kuma kasashen yammacin turai suna dora barazanarsu ne kan...
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da takwarorinsa na kasashen Afrika da suka zo kasar Sin domin halartar taron ministoci masu jagorantar aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin a taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika. Wang Yi wanda kuma mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya tattauna jiya Talata a Changsha, babban birnin lardin Hunan, da ministocin da suka hada da Musalia Mudavadi na Kenya da Yassine Fall ta Senegal da Mahmoud Thabit Kombo na Tanzania da Selma Ashipala-Musavyi ta Namibia da Phenyo Butale na Botswana da kuma Tete Antonio na Angola. Da yake ganawa da Musalia Mudavadi na Kenya, Wang Yi ya ce a shirye Sin take ta hada hannu da...

Shugabannin Sin Da Kongo (Brazaville) Sun Aike Da Wasikun Taya Murna Ga Taron Ministocin Kula Da Aiwatar Da Sakamakon Taron FOCAC
Yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Kongo Brazaville Denis Sassou Nguesso, sun aike da wasiku na taya murna ga taron ministocin kula da harkokin da suka shafi aiwatar da sakamakon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wato FOCAC, inda suka taya murnar bude taron. Cikin sakonsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, a halin yanzu, yanayin kasa da kasa ya cika da sauye-sauye da hargitsi. Kuma kasar Sin ta dage wajen samar da sabbin damammaki ga duniya tare da sabbin nasarorin da aka samu na zamanantarwa iri ta kasar Sin, da samar da sabon kuzari ga kawayen kasashe masu tasowa na duniya kamar kasashen Afirka ta hanyar shiga a dama da su a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ƙara da cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe zaɓe shi kaɗai. “Ku bai wa Kudu tikitin, ku ga sakamako. Amma idan PDP ta ci gaba da tafiya a kan wannan kuskure, to, za ta fuskanci babbar matsala a 2027,” Yusuf ya bayyana. Ya kuma bayyana cewa Atiku Abubakar ba ɗa jam’iyyar PDP ba ne a yanzu, yana tare da wata sabuwar tafiyar haɗin gwiwa ta siyasa. Yusuf ya ɗora alhakin faɗuwar jam’iyyar a zaɓen 2023 kan rashin kyakkyawan shugabanci da kuma rabon tikiti ba bisa ƙa’ida ba. Ya ce rikicin cikin gida da kuma gazawar PDP wajen kulawa da ‘yan Kudu ne suka sa jam’iyyar ta faɗi. Ya kuma nuna takaicinsa game da sauya sheƙar Gwamnan...
Amma har zuwa yanzu, babu cikakken bayani daga Gwamnatin Tarayya. A watan Mayun 2025 ne Tinubu ya miƙa buƙatar samun amincewar majalisa domin karɓar rancen Dala biliyan 21 daga ƙasashen waje, ciki har da Dala biliyan biyar daga Aramco. Rahoton Reuters bai bayyana sunayen bankunan da za su taimaka ba, amma majiyoyi sun ce ɗaya daga cikin bankunan na nahiyar Afrika ne, sauran kuma daga Gabas ta Tsakiya. Idan aka cimma yarjejeniyar, wannan zai zama mafi girma daga cikin bashin da Nijeriya ta taɓa karɓa a irin wannan hanya daga Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
Akpabio ya shigar da buƙatu a gaban kotun inda ya nemi ƙarin lokaci don ɗaukaka ƙara a kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar 10 ga watan Maris, 2025. Wannan shari’a ta haɗa da Sanata Natasha da ke ƙarar Sakataren Majalisar Tarayya da wasu mutane uku kan dakatar da ita. Haka kuma, Akpabio ya nemi kotu ta ba shi izini ya ɗaukaka ƙara da kuma dakatar da ci gaba da sauraron shari’ar a Babbar Kotun har sai an yanke hukunci a kotun ɗaukaka ƙara. Sai dai yanzu da aka janye ƙorafe-ƙorafen kuma kotu ta yi watsi da su, hakan na nufin waɗannan bukatu na Akpabio ba za su ci gaba da sauraron su a...
Iran ta bada sanarwan cewa ta sharia matakan da zata dauka kan hukuma IAEA mau kula da makamashin nukliya ta duniya idan ta samar da kudurin yin allawadai ko kuma rashin bada ahadin kai ga hukumar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ik Baghae yana fadara haka a jiya Talata . Ya kuma kara da cewa martani da zata mayar tare da hadin kai da hukumar makamashin nukliya ta kasar wato ko Atomic Energy Organization of Iran (AEOI). Baghae yayi allawadai da rahoton da Daraktan hukumar IAEA Rafael Grossi ya bayar dangane da shirin Nukliyar kasar kafin taron gwamnonin hukumar. Yace wannan a fili ya nuna cewa hukumar AIEA tana aiki...

Wang Yi Ya Gabatar Da Jawabi Albarkacin “Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa” Karo Na Farko Na MDD
Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gabatar da jawabi ta bidiyo a gun bikin “Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa” karo na farko na MDD yau Talata. Wang Yi ya bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shirin raya al’adu na duniya, inda ya ba da shawarar raya dabi’u na bai daya na dukkan bil’adama, da dora muhimmanci kan gado da kirkire-kirkire na wayewar kai, da karfafa mu’amala da hadin gwiwar al’adu tsakanin kasa da kasa, wadanda muhimmin kokari ne da kasar Sin ta yi don inganta tattaunawa tsakanin wayewar kai. A shekarar 2024, babban taron MDD karo na 78, ya amince...
Gwamnan ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Neja kan mummunar barnar da ambaliyar ruwan ta yi, na salwantar da rayuka da barnata dukiya da dama. Gwamna Umar Bago na jihar Neja, ya yabawa takwaransa na Borno bisa wannan ziyarar da kuma bayar da gudunmawar, inda ya ce lokaci ya yi da za a nuna soyayya ga juna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Da safiyar yau Talata ne dai sojojin HKI su ka kai wani hari a garin “Aytas-sha’ab’ dake kudancin Lebanon da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutane biyu. Kafafen watsa labarun Lebanon sun ambaci cewa, mutanen biyu da su ka yi shahada sun hada da wani makiyayi da dansa da suke kiwon dabbobinsu a burtalin dake kan iyaka da Falasdinu dake karkashin mamaya. A jiya Litinin ma dai wani jirgin sama maras matuki na ‘yan sahayoniyar, ya kai hari a garin Nabadhiyyah. Har ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan ko harin na jiya ya yi sanadiyyar shahadar wasu ko jikkata. Sai dai kuma gobara ta tashi a cikin motar da ‘yan sahayoniyar su ka kai wa harin na jiya. Daga...
“Mun bi tsarin mulki kuma mun ƙi rashin adalci. Da PDP ta yi haka, ba za ta fuskanci wannan matsala ba.” Taron ya haɗa da tsoffin gwamnonin jihohi Samuel Ortom (Benue) da Okezie Ikpeazu (Abia), da sauran shugabannin jam’iyyar. Wike ya soki shugabannin PDP saboda sanya son rai fiye da haɗin kan jam’iyyar. Ya ce jam’iyyar sai ta koma tubalinta na asali don samun ci gaba. “Wasu shugabanni suna karkatar da dokoki don amfanin kansu,” in ji Wike, yana ambaton yadda gwamnan Taraba ya tsaya takarar gwamna ba tare da ya yi murabus a matsayinsa na shugaban jam’iyyar ba. “Dole ne a daina wannan.” Tsohon Gwamna Ortom ya yarda da maganar Wike, ya amince cewa PDP ta yi manyan kurakurai....
A bara ne dai dam ɗin Alo ta cika da ruwa har wani ɓangare ya buɗe, lamarin da ya haddasa mummunar ambaliya a Maiduguri, inda aka rasa rayuka da dukiyoyi da dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani kamfanin kera kayakin aikin likita mai zaman kansa a nan Tehran ya gabatar da wata na’ura mai aikin tiyata wanda kuma aka dora masa kayan aiki na zamani. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gabatara da wannan na’urar a kasuwar baje kolin kayakin aikin likita karo na 26TH wanda ke gudana a nan birnin Tehran. Labarin ya kara da cewa samar da kayalin aikin likita wadanda suke tafiya da zamani, ya zama dole ne bayanda aka haka sayarwa kasar Iran irinsu daga waje. Wannan hanin ya sa a dole daga cikin gida kwararru suka fara samar da kayakin aikin likita na zamani, don wadatar da asbitocin kasar daga sayan na waje, har ma tana...
Ma’aikatar kiwon lafiya na kasar Iran ta bayyana cewa kasar a halin ayanzu tana daga cikin kasashe uku na gaba a kan abinda ya shafi samun isasshen abinci mai lafiya da kuma wadatacce a cikin kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan kiwon lafiya Muhammad Reza Zafarkandi yana fadar haka a jiya litinin a taron raya ranar abinci da duniya wanda aka gudanar a dakin taro na hukumar gidajen radio da talabijin a nan birnin Tehran. Ministan ya kara da cewa, samun abinci mai gina jiki da kuma bada sinadaran da jiki yake bukata yana daga cikin abubuwan da suke bada lafiya ga jiki. Har’ila yau wannan yana kwantar da hankalin mutanen ko wace kasa wacce...
Tun daga yau Litinin 9 ga watan Yuni, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar bai wa ’yan wasu kasashe iznin shiga cikin kasar ba tare da takardar biza ba, ciki har da Saudiyya, da Oman, da Kuwait, da Bahrain. Kawo yanzu, adadin kasashen da kasar Sin ta bai wa jama’arsu izinin shiga cikin kasar ba tare da takardar biza ba, ya habaka zuwa 47. Tun daga ranar 9 ga watan Yunin shekara ta 2025, zuwa ranar 8 ga watan Yunin shekara ta 2026, mutanen dake da takardar fasfo daga kasashen Saudiyya, da Oman, da Kuwait, da kuma Bahrain, idan suna so su shigo kasar Sin don yin kasuwanci, ko yawon bude ido, ko ziyartar iyalai da abokansu, ko kuma...
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Litinin 9 ga wata sun nuna cewa, a watan Mayun bana, ma’aunin farashin kayayyakin masarufi, watau CPI na kasar, ya ragu da kaso 0.1 bisa dari, bisa na makamancin lokacin bara, kuma farashin makamashi ya zama babban dalilin da ya haifar da raguwar. Kana, ma’aunin farashin sarrafa kaya na cikin gida, watau PPI shi ma ya ragu da kaso 3.3 bisa dari, bisa na makamancin lokacin bara, kuma adadin ya ragu da kaso 0.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na watan Afrilun bana. Duk da cewa ma’aunin CPI na watan Mayu ya ragu kadan, amma farashin kayayyaki a wasu bangarori ya canza, al’amarin da ya shaida rawar da...
Jiragen ruwan wadanda aka bai wa sunan: “Jajurcewa” za su tashi ne daga Tunisiya jim kadan bayan da sojojin HKI su ka hana wani jirgin ruwan dake dauke da masu fafutuka daga kasashen turai,isa gabar ruwan Gaza. Jirgin ruwan na ” Jajurcewa’ zai bi ta ruwan Libiya, sannan Masar daga can kuma ya nufi gabar ruwan Gaza. Jiragen ruwan dai suna dauke da masu fafutuka 7,000 daga kasashen Tunisiya, Moroko, Aljariya, Murtaniya, da Libiya. Kwamitin kasa da kasa domin karya killace Gaza, wanda ya shirya wannan tafiyar, ya kuma yi wani kiran ga ‘yan fafutuka a duniya da su shirya wasu tafiye-tafiyen ta ruwa zuwa Gaza, domin kawo karshen killace yankin da aka yi tun 2007.

Ministan Harkokin Kiwon Lafiya Na Iran Ya Bukaci A Yawaita Sayar Da Kayakin Likita Zuwa Kasashen Waje
Minitan kiwon lafiya na kasar Iran ya bukaci kamfanonin da suke kera kayalin kiwon lafiya da kuma aikin likita so kara yawan kayakin da ake sayarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Reza Zafarkhan yana wannan kiran a jawabin da ya gabatar a taron bude kasuwar baje koli na kayalin aikin likita da kuma kiwon lafiya a nan Tehran. Ministan ya kara da ce wa duk tare da mummunan takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka ta dorawa kasar wannan bai hana ta ci gaba a fannonin ilmi masu yaw aba. Wanda ya kaita kasa da wasu manya-manyan kasashen duniya a wasu fagagen. Ministan ya bukaci kamfanonin kera kayakin likita da kiwon...
Wadanda suka shirya jirgin agaji zuwa Gaza mai suna Madleen sun bada sanarwan cewa HKI kai farmaki kan jirgin a safiyar yau Litinin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jami’an tsaron HKI sun kaiwa jirgin Madleen hare-hare a safiyar yau Litinin kafin iasar Jirgin agajin zuwa gabar tekun Medeterania a gaza. Labarin ya kara da cewa Thiago Avila, dan rajin kare hakkin bil’adama daga kasar Brazil a cikin Jirgin ya bayyana cewa sojojin yahudawan sun yiwa jirgin kofar rago . Y ace sojojin ruwa na HKI sun kaiwa jirgin agaji ” Madleen farmakai. Jirgi wanda yake kokarin keta kofar ragon da HKI ta yi wa Gaza tun shekara 2006. Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan...
Minitan kiwon lafiya na kasar Iran ya bukaci kamfanonin da suke kera kayalin kiwon lafiya da kuma aikin likita so kara yawan kayakin da ake sayarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Reza Zafarkhan yana wannan kiran a jawabin da ya gabatar a taron bude kasuwar baje koli na kayalin aikin likita da kuma kiwon lafiya a nan Tehran. Ministan ya kara da ce wa duk tare da mummunan takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka ta dorawa kasar wannan bai hana ta ci gaba a fannonin ilmi masu yaw aba. Wanda ya kaita kasa da wasu manya-manyan kasashen duniya a wasu fagagen. Ministan ya bukaci kamfanonin kera kayakin likita da kiwon...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani babban jami’in soja, Laftanar Commodore M. Buba, ya rasa ransa bayan da wani ɓarawon waya ya soka masa wuƙa a ƙirji. Lamarin ya faru ne a gadar Kawo, lokacin da jami’in ya tsaya domin gyara tayar motarsa da ta fashe yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Jaji, inda yake karatu a Makarantar Horas da Sojoji ta Armed Forces Command and Staff College (AFCSC). Matawalle ya yi wa Gwamna Lawal da wasu tayin shiga APC Gwamnatin Tarayya na shirin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta Shaidu sun bayyana cewa yayin da jami’in ke cikin gyara tayar, sai wani mutum ya zo ya buƙaci ya ba shi wayarsa. Jami’in soja ya ƙi bayar da wayar, inda ɓarawon ya ciro...
Kamfanin sojojin haya na Rasha, Wagner, ya sanar da janyewarsa daga kasar Mali, abin da ya kawo kƙarshen fiye da shekaru uku na ayyukansa a wannan kasa ta Yammacin Afirka. “Mun taimaka wa ‘yan kishin kasa wajen gina wata rundunar sojoji mai karfi da tsari, wacce za ta iya kare kasarsu. Dukkan manyan biranen yankin sun koma karkashin ikon mahukuntan da ke da ikon tafiyar da harkoki a kasar,” in ji Wagner. Kasar Mali, da ke yankin Sahel, ta sha fama da hare-haren ‘yan tawaye tun daga shekarar 2012, kuma sojojin dake mulki a kasar sun nemi taimakon Rasha bayan sun katse dangantaka da Faransa da sauran abokan hulda. A farkon wannan shekarar, kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar, da...
Jimillar fursunoni: 80,879 Adadin cibiyoyin gyaran hali: 256 Kashi na rijista da aka kammala: 74% Umar ya jaddada cewa sauran fursunonin da ba a yi wa rijistar ba za a cigaba da yi musu, kuma an kafa duk wasu hanyoyi da za su tabbatar da nasarar kammala aikin cikin sauki. Hukumar ta bayyana wannan aikin a matsayin wani muhimmin mataki na inganta tsarin dijital, da sake gyaran rayuwa, da shigar da fursunoni cikin tsarin ƙasa. Ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da sahihancin bayanansu daga hukumomin da suka dace kafin wallafawa domin kaucewa yaɗa bayanan da za su iya dagula fahimtar jama’a ko rage ƙwarin gwuiwar al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
Ma’aikatar cinikayya ta Sin, ta ce kasar ta amince da bukatar samar da lasisin rika fitar da wasu nau’o’in ma’adinai na “rare earth”, da abubuwan da ake sarrafawa da su zuwa ketare, duba da karin bukatar su da masana’antun sarrafa mutum-mutumin inji, da ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi ke yi. Kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ya ce abubuwan da ake sarrafawa da ma’adinan “rare earth”, na da amfani a sassa biyu, wato ko dai na ayyukan soji, ko na amfani a abubuwan bukatu na fararen hula, don haka kayyade fitar da su ya dace da matakan da aka amince da su tsakanin sassan kasa da kasa. Kazalika, jami’in ya jaddada cewa, kayyadewar na da nufin kyautata matakan tsaron...
A masana’antar Nollywood dake Kudancin Nijeriya, manyan masu kudinsu, sarakuna, hukumomi da gwamnatoci na iyakar kokarinsu wajen ganin masana’antar ta cigaba, ta hanyoyi daban daban da suka hada da kayan aiki, wajen daukar fim, fadada ilimi, tallace tallace da sauran tallafi da masana’antar ke bukata, a wasu lokutan ma akan daukesu har kasashen Turai wajen koyon aiki da kuma tallata hajarsu ga manyan dillalan fim a Duniya wanda ta wannan hanyar sai su samu manyan kudade. T Y ya cigaba da cewa idan ana maganar masana’antar Kannywood ba haka abin yake ba, domin kuwa a nan yankin sai mai shirya fim ya nemi gida ko kamfanin da zai shirya fim din sa ya rasa, hakan zai sa ya je ya...
Daga cikin sinadaran akwai: ‘Hydrokuinone, corticosteroids/hydrocortisone, Mercury’ ko kuma sunaye kamar haka: ‘calomel, mercuric, mercurous, ko mercurio’. Idan mutum ya duba takardar da ke like a jikin mazubin man da ya siya, domin ganin bayanan sinadaran da ya kunsa, zai ga wadannan a jiki. A kula, kada a sake a zabi duk wani man shafawar da ke dauke da daya daga cikin sinadaran da aka ambata a sama. Daga cikin haduran amfani da wadannan sinadarai sun hada da: 1- Kodewar fata tare da bayyanar launin shudi-shudi ko kore-kore a fata. 2. Saurin tsufa ko yanƙwanewar fata. 3. Sirancewar fata, wato kaurin fata zai rika raguwa sannu a hankali. 4. Bayyanar jijiyoyin jini a kasan fata, wadanda da ba a...
Daya daga cikin shuwagabannin Falasdinawa ya yi shahada sanadiyyar hare-haren da sojojin HKI suka kai kan zirin gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Asa’d Abu Sharia shi ne baban sakataren kungiyar ‘Dakarun Palastinewa”. Wacce aka kafa a shekara ta 2001 M. Kungiyar kanta ta tabbatar da wannan labarin ta kuma bayyana cewa ya dade yana shugabantar wannan kungiyar sannan a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ya shiga cikin yakin da aka fara kan HKI kuma dakarunsa sun kama yahudawa da dama suka shigo da su su gaza. Banda haka shi ne yake jagorantar bangaren soje na kungiyarsa. Sau da dama ya jagoranci Falasdinawa a yaki da yahudawan a Gaza. Sannan kungiyar tana...
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya nanata matsayin Taiwan da jaddada manufar Sin daya tak a duniya yayin tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot a jiya Jumma’a. Ya kuma bayyana adawar Sin da shigar kungiyar tsaro ta NATO cikin harkokin yankin Asiya da Pasifik. Wang Yi wanda mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya nanata cewa, batun da ya shafi Taiwan, batu ne na cikin gidan Sin da ya shafi ’yancin kasar da iko kan yankunanta, wanda ya bambanta da batun kasar Ukraine. Ya ce Sin na daukar amincewa da manufar kasar daya tak da Faransa ta yi da muhimmanci, kuma tana fatan ganin hakan a aikace. Bugu da kari, ministan ya...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta wallafa tsokacinta kan rahoton babban darartan Hukumar IAEA ga kwamitin gwamnonin hukumar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da ra’ayoyinta da tsokacinta kan sabon rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) ya gabatar ga kwamitin gwamnonin hukumar ta IAEA a ranar 24- wannan shekara ta 2025. A cewar cibiyar diflomasiyya da ta yada labarai ta hukumar makamashin nukiliya ta Iran, an fitar da bayanin mai taken “Sa ido da Tabbatarwa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da kudurin kwamitin tsaro mai lamba 2231 (2015)” a ranar 31 ga Mayu, 2025. Bayanin ya fayyace cewa: Rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa...
Kasar Rasha ta kai wasu gagaruman hare-haren jiragen saman yaki marasa matuka ciki kan birnin Kharkiv na kasar Ukraine Rasha ta kai wadannan gagaruman hare-haren ne ta hanyar amfani da jiragen saman marasa matuka ciki kan birnin Kharkiv na gabashin Ukraine. Magajin garin Kharkiv ya ce: Hare-haren da jiragen saman Rasha suka kai a tsakiyar birnin sun haddasa gobara da barna sosai. Takaddama tsakanin Rasha da Ukraine na kara kamari a kasa duk da ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu ke yi. Mjiyar sojin Ukraine ta amince cewa: Sojojin Rasha sun kaddamar da gagaruman hare-hare kan birnin Kharkiv da ke gabashin kasar Ukraine ne, lamarin da ya haifar da fashe-fashe a birnin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da...
A jawabinsa a wajen taron kaddamar da tsarin tattaunawa kan shirin yin amfani da fashar zamani na samar da yin rjitsar ta manoman kasar (NDFR), wadda aka gudanar a babban birnin tarayyar Abuja, Babban Sakatare a Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci, Dakta Marcus Ogunbiyi, ya bayyana cewa; sabon tsarin zai taimaka matuka, wajen rage duk wani matsayi da manoman kasar suke ciki, musamman manoman da ba su mallaki wata gona ba. “Za mu tabbatar mun yi rijistar sunayen manoman kasar da kuma gonakinsu, sannan kuma ba wai kawai yin rijistar ba, har da irin nau’in amfanin da suke nomawa da kuma nau’in irin kasar da ke gonakin nasu,” in ji Marcus. Dakta Marcus ya kara da cewa,...
Sojojin Rasha sun kai hare-hare mafi muni akan cibiyoyin soja da muhimman cibiyoyi a kasar Ukiraniya da su ka hada da birnin Kiev. Sojojin na Rasha sun yi amfani da kamamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki masu kai harin kunar bakin wake da su ka haddasa tashin gobara. Jami’in tafiyar da sha’anin Mulki a birnin Kharikiev ya bayyana cewa; A kalla mutane 10 su ka jikkata a bisa kididdigar farko. Ita kuwa rundunar sojan saman kasar ta Ukiraniya ta sanar da cewa; an yi amfani da makamai masu linzami samfurin “Cruise” wajen kai harin. Su ma sojojin na Rasha sun sanar da cewa, sun kai wa Ukiraniya hare-hare akan sansanonin soja da kuma muhimman cibiyoyin kasar ta hanyar...
A rana ta biyu tabukuwan babbar salla, sojojin HKI suna ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyasahi da kuma rusa matsugunansu a yankin Gaza. A yau Asabar kadai gwamman Falasdinawa ne su ka yi shahada a cikin sansanonin da Falasdinawa suke gudun hijira a cikinsu. An sami shahidai 5 da kuma wasu mutane biyu da su ka jikkata a kusa da cibiyar rana kayan agaji a yammacin Rafah dake kudancin zirin Gaza. A yammacin birnin Khan-Yunus kuwa wasu Faladinawa 12 ne su ka yi shahada, yayin da wasu 40 su ka jikkata saboda harin da ‘yan sayahoniyar su ka kai wa sansaninsu. A arewacin Khan-Yunus kuwa, sojojin mamayar sun ruguza gidajen Falasdinawa da dama. A kusa da cibiyar kiwon...
Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta bayyana cewa; Matakin da Amurka ta dauka na kakaba takunkumin shiga Amurka akan wasu ‘yan kasa da kuma wasu kasashen musulmi yana nuni da yadda Amurkan take adawa da musulmi. Haka nan kuma ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta ce; Daukin matakin hana wasu mutane yin tafiya saboda kasar da su ka fito, ko addininsu yana nuni ne da yadda Amekin take jin fifiko da kuma nuna wariya. A karshe ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta yi kira ga MDD da sauran cibiyoyin kasa da kasa na shari’a da su dauki mataki karara kuma a fili akan abinda Amurka ta yi, da ya sabawa duk wani ma’auni na ‘yan adamtaka. A ranar...
A shekarar da ta gabata, kamfanin Dangote ya biya haraji N450 biliyan – wanda ya fi dukkan bankunan Nijeriya suka hada jarin harajin da suka biya. Wannan shiri na gina hanyoyi yana cikin shirye-shiryen gwamnati na ba da rangwamen haraji domin inganta kayayyakin more rayuwa a kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp