Kazalika, masu sukar na ganin cewa, gwamnatin ta yi watsi da irin halin ƙuncin rayuwa da musamman
talakwan ƙasar, ke ci gaba da fuskanta, kamar dai, na ci gaba da hauhawan farashin kayan masarufi da
ƙarin kuɗin Man Fetur da ƙarin kuɗin wutar lantarki da ƙarancin albashin da ake biyan ma’aikata,
musamman na gwamnati, wanda a baya, ta yi alƙawarin lalubo masu da mafita.

Wannan batun na ƙarin albashin, tamkar dai wani cin zarafi wanda kuma abu ne, da ke tattare da hatsari.
Kusan tun lokacin da shugaba Bola Tinubu, ya ɗare Karagar shugabancin ƙasar, ya rage yawan kuɗaɗen
da ake kashewa, na gudanar da mulki, inda gwamtainsa, ta rage yawan ɗimbin tawagar da take kwasa, na
yin tafiye-tafiye, musamman zuwa ƙasashen duniya.
Amma batun na ƙarawa ƴ an siyasa masu riƙe da madafun ikon, a wannan yanayin da ƙasar ke a ciki,
tamkar mayar da Agogo baya ne.
Misali, gwamnatin har zuwa yau, ta gaza wajen cika ɗaukacin buƙatun ƙungiyoyin manyan makaratun
ƙasar wato ASU da kuma ASUP, inda kuma a gefe ɗaya, ƙungiyoyin ƙwarrun likitoci, suma suke ta kai
gwauro da mari, na neman gwamnatin, ta biya masu na su buƙatun
Saboda rashin biya masu buƙatun na su, suke tsunduma cikin yajin aiki na gargaɗi ko kuma gargaɗi.

Hakazalik, a yayin da ƙasar ke jigelon kashe kuɗaɗe, na gudanar da wasu ayyuka a ƙetare, amma a gife
ɗaya, an bar ma’aikata na karɓar mafi ƙarancin alabshin na Naira 70,000 kacal, inda wannan kuɗin, ba zai
iya kawar masu koda da ƙishirwarsu ba, duba da hauhawan kayan masarufi, da ake ci gaba da fuskanta a
ƙasar.

Akasarin ma’aikata a ƙasar, na ci gaba da kasance wa ne a cikin talauci, inda kuma sauran ƴ an siyasa, ke
ci gaba da yin wadaƙa.
Maimakon ƙarin albashin kamata yi Hukumar ta fara tunanin fara yiwa albashin ma’aikatan gwamnati
garanbawul da kuma inganta rayuwarsu.A yayin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar ƙaranci kuɗi tare da kuma yadda alummar ƙasarke ci gaba da
fitar da rai ga alƙawarin da gwamnatin shugaba Tinubu ta yi, na saita ƙasar, batun na yin ƙarin, a wannan
lokacin, wani abin dubawa ne.
Wannna Jaridar ta nuna takaicinta kan wannan batun, musamman duba da cewa, yunƙurin na Hukumar,
na ci gaba da fuskantar suka.

Bugu da ƙari, duba da cewa, Nijeriya kusan ta dogara ne kachokam, kan ciwao bashi daga ƙetare, domin
ci giɓin da take da shi, a cikin kasafin kuɗinta, wanda hakan ya saɓawa ƙa’ida, a saboda haka, batun na
ƙarin albashin ga ƴ an siyasa, tamkar zuba kuɗi ne, a inda bai kamata ba.
Ya zama wajibi, gwamnatin ta dakatar da wannan batun na ƙarin albashin ga ƴ an siyasa masu riƙe da
madafun iko, amma ta mayar da hankali, wajen gudanar da bin diddigin kashe kuɗaɗe wanda zai yi daidai
da, tsarin tattalin arzikin ƙasar, a zahirance da kuma gudanar da ƙa’idojin gudanar da aikin gwamnati.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Siyasa ƙarin albashin ƴ an siyasa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar

Daga Usman Muhammad Zaria 

 

Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.

Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.

Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.

Ya ce an tsara wannan asusu  ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.

Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.

Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin  ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.

Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a  wuraren.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda