2025-11-23@11:05:41 GMT
إجمالي نتائج البحث: 205

«shari ar kananan yara»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Hukumar Kula da Hanyoyi da Sufuri ta Jihar Kano (KAROTA), ta ware Naira miliyan 250 domin gyaran wasu motocin aiki guda biyar. Haka kuma, hukumar ta kashe Naira miliyan 250 domin sayen sabbin motoci domin amfanin da su. Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai An kashe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani a Sweden Kwamishinan Tsare-Tsare da Kasafin Kuɗi na Jihar, Musa Sulaiman Shanono ne, ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan kasafin kuɗin shekarar 2025 da aka amince da shi. Ya bayyana cewa ingantaccen tsarin sufuri yana da matuƙar muhimmanci ga bunƙasa tattalin arziƙi da ci gaban al’umma. Ya kuma ce gwamnatin jihar na ƙoƙarin inganta kayan sufuri domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da kayayyaki a...
    Bugu da ƙari, dokar za ta bai wa direbobin da ke jigilar fasinjoji damar kula da yanayin fasinjojin da za su ɗauka ta yadda in sun ga yara dole sai sun tantance wanene ya ɗaukosu kuma meye nasabarsu dukka da nufin daƙile satar yara da safararsu.   Sannan gwamnan ya kuma sanya hannu kan dokar da ta bai wa kamfanonin sadarwa (Telecom Service Providers) dama ta yadda ba za a cajesu ko kwabo ba, da nufin inganta lamarin yanar gizo da inganta kamfanonin sadarwa domin jama’a suke morar amfani da tauraruwar ɗan adam da nufin sauƙaƙa harkokin kasuwanci a jihar.   Gwamnan ya yi gargaɗin cewa duk wani direban da ya ƙi bin umarnin da aka sanya na sanya ido...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare,  da...
    Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai  miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
    Majalisar dokokin jihar Jigawa ta jaddada aniyar ta na hada kai da ofishin kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF domin samun nasarar aiwatar da tsare-tsare da za su inganta rayuwar yara da marasa galihu a jihar.   Mataimakin kakakin majalisar, Alhaji Sani Isyaku Abubakar, ya bada wannan tabbacin lokacin da ya karbi bakuncin tawagar ofishin UNICEF na Kano karkashin jagorancin Hajiya Fatima Adamu.   Ya lura cewa irin wannan haɗin gwiwa tsakanin majalisa, Action Against Hunger da Save the Children International sun haifar da sakamako mai kyau ta hanyar tallafawa matakan majalisa ta hanyar fasaha da ba da shawara don tsara manufofin da sauran tsare-tsaren a Jigawa.   Alhaji Sani Isyaku Abubakar ya bada tabbacin ci gaba...