Gwamnan Bauchi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Da Za Ta Daƙile Satar Yara A Bauchi
Published: 29th, January 2025 GMT
Bugu da ƙari, dokar za ta bai wa direbobin da ke jigilar fasinjoji damar kula da yanayin fasinjojin da za su ɗauka ta yadda in sun ga yara dole sai sun tantance wanene ya ɗaukosu kuma meye nasabarsu dukka da nufin daƙile satar yara da safararsu.
Sannan gwamnan ya kuma sanya hannu kan dokar da ta bai wa kamfanonin sadarwa (Telecom Service Providers) dama ta yadda ba za a cajesu ko kwabo ba, da nufin inganta lamarin yanar gizo da inganta kamfanonin sadarwa domin jama’a suke morar amfani da tauraruwar ɗan adam da nufin sauƙaƙa harkokin kasuwanci a jihar.
Gwamnan ya yi gargaɗin cewa duk wani direban da ya ƙi bin umarnin da aka sanya na sanya ido kan yaran da ake safararsu doka za ta hau kansa. Sannan, ya ce ba za su lamunci yadda ake sace yaran jihar ana kaisu kudu.
Ya bayar da misalin baya-bayan da aka ceto wasu yaran jihar su uku daga jihar Anambra bayan da wata mata ta sace su a wani gidan haya. Don haka ne ya nemi Sarakuna da masu unguwanni da su ƙara bada tasu gudunmawar domin cimma nasarar kare yara ƙanana a jihar.
এছাড়াও পড়ুন:
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
Yayin ganawarsa da firaministan Thailand, Shugaba Xi Jinping ya ce a shirye kasarsa take ta karfafa hadin gwiwa da Thailand kan dabarun samun ci gaba, tare kuma da gabatar da gogewarta na samun ci gaba a sabon zamani, kuma ya yi kira da a gaggauta gina layin dogo tsakanin Sin da Thailand da bunkasa hadin gwiwa a bangaren cinikin amfanin gona da tattalin arziki mai kiyaye muhalli da kuma kirkire kirkiren fasaha. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA