2025-06-23@03:22:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1824

«a kowace rana a watan»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suna da mugun nufi kan Iran da kasashen musulmi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila na da mugun nufi kan Iran da kasashen musulmi. A yayin wani jawabi da ta gabatar a wajen juyayin tunawa da rasuwar Imam Khumaini {r.a}, Pezeshkian ya ce: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta iya aikata wani aiki hauka da wauta ba, idan kasashen musulmi suka hada kansu. Pezeshkian ya kara da cewa: Wadanda ke da’awar kare hakkin bil’adama suna kare “haramtacciyar kasar Isra’ila” mai laifi, kuma suna ci gaba da adawa da shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Ya ci gaba da cewa: “Babu mutum...
    Sojojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurium a wani aiki na musamman na tallafawa al’ummar Gaza Sojojin Yemen sun sanar da kai wani gagaruminj hari kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye ta hanyar amfani da makami mai linzami kirar Falasdinu 2. Hari ya gudana daidai inda aka tsara shi, kuma ya haifar da firgici da ya kai ga miliyoyin yahudawan sahayoniyya gudu tare da shigewa maboyar karkashin kasa kamar burage. Har ila yau, harin ya dakatar da dukkan ayyukan filin jirgin, tare da hana wani jirgin dakon kaya na sojan Amurka sauka a filin jirgin sama na Ben Gurium a rana ta biyu a jere. A cikin wannan yanayi ne...
    Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya sanar da cewa, nan da kwanaki masu zuwa Iran za ta mayar da amsa kan shawarar da Amurka ta gabatar kan shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya. A cewarsa, shawara da Amurka ta gabatar tana bukatar zurfafa bincike. M. Araghchi, ya bayyana hakan ne ziyarar da yake a birnin Beirut, na kasar Lebanon inda ya jaddada cewa, amsar da Iran za ta mayar zata kasance bisa tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da manufofinmu da kuma kare muradun al’ummar Iran. Ya nanata cewa inganta makamashin Uranium tamkar “jan layi” ne ga Iran, yana mai cewa Tehran ba ta bukatar neman izini daga kowa don ci gaba da ayyukanta da suka dace da shari’a kuma...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bukaci hadin kan al’ummar kasar Lebanon wajen warware matsalolin kasar, yana mai kira da a yi shawarwarin kasa tsakanin dukkanin kungiyoyin siyasa domin cimma matsaya daya. Araghchi ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi a ranar Talata, da shugaban kasar Labanon, Joseph Aoun a birnin Beirut. Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada aniyar kasarsa na bunkasa alakarta da kasar Lebanon, bisa mutunta juna. Ya kuma sanar da cewa, kamfanonin Iran a shirye suke su marawa gwamnatin Lebanon baya a kokarinta na sake gina kasar. A nasa bangaren shugaba Aoun ya jaddada tsarin gwamnatinsa na bunkasa alaka da dukkan kasashen duniya tare da tabbatar da aniyar kasar Lebanon na...
    Cikin kwanaki uku na hutun bikin Dragon Boat na kasar Sin, an samu karuwar tafiye-tafiye zuwa ketare da suka kusa miliyan 5.91. Masu tafiye-tafiye sun karu matuka tun daga Asabar har jiya Litinin, inda aka samu karuwar kaso 2.7 bisa dari kan adadin da aka samu a bara. Alkaluman da hukumar lura da shige da ficen al’umma ta kasar Sin ta fitar a Talatar nan, sun nuna karuwar baki masu shigowa kasar Sin daga ketare, musamman wadanda suka ci gajiyar manufar nan ta kawar da bukatar biza. Albarkacin wannan manufa, adadin baki daga ketare da suka shigo kasar Sin yayin ranaku uku na bikin ya kai 231,000, adadin da ya karu da kaso 59.4 bisa dari kan na shekarar bara....
    “Bisa ga hakan ne, Gwamnan jihar, Dakta Nasir Idris ya bayar da wannan tallafin don gudanar da shagalin sallar cikin walwala da Jin dadi”.   Shugaban ya gode wa Gwamnan jihar kan wannan kokarin da yayi na tunanin a zakulo mata uku a kowace rumfar zabe a duk mazabun kananan hukumomin 21 na jihar don basu tallafin N30,000 don gudanar da shagalin sallar Eid-kabir, “muna masa godiya a madadin matan da suka ci gajiyar tallafin”.   Daga karshe, Zuru ya yi kira ga sauran shugabanni da su yi koyi da Gwamnatin jihar Kebbi kan tallafa wa al’umma a jihar musamman a irin wannan lokaci ga wannan lokaci da jama’a ke da bukatar yin layya. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Jaridar Guardian ta ta kasar Birtaniya ta bada labarin cewa, Hare-haren da sojojin HKI su ka kai kan wata makaranta, inda yan gudun hijira Falasdinawa suke samun mafaka da gangan suka yi shi, suna sane, kuma a halin yanzu suna Shirin kai wa wasu makarantun guda 4 hare-hare nan gaba. Jaridar ta kara da cewa: Isra’ila ta ayyana wasu Karin makarantu wadanda Falasdinawa suke samun mafaka a cikinsu domin kai musu hare-hare a nan gaba. A lokacinda HKI ta kasa ganin mayakan Hamas a fili sojojinta sun koma kan kissan Falasdinawa fararen hula, wadanda suke samun mafaka a makarantu. A cikin watanni da suka gabata sojojin mamayar sun kai hare-hare akan wasu gine-ginen 6 wadanda suka kasance makarantu ne, wadanda...
    Daya daga cikin manyan-manyan  jami’an gwamnatin tsohon shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya bayyana cewa: “Babu tantama gwamnatin HK Isra’ila ta tafka laifukan yaki a kan Falasdinawa a zirin Gaza da ta killace. Matthew Miller wanda ya yi aiki a matsayin kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka tun daga 2023 har zuwa karshen gwamnatin Joe Biden, ya fada wa tashar talabijin ta Sky News kan cewa; Isra’ilan ta tafka laifukan yaki. Da aka yi masa tambaya a kan yakin Gaza a fadar White House, Miller ya ce; An yi ta samun tsabani dangane da yakin, sabani manya-manya wani lokacin kuma kananan sabani, kan yadda za a kare dangantakar  Amurka da HK Isra’ila duk tare da abinda take aikatawa.”. Amma Miller ya...
    Ofishin shugaban kasar Turkiya, ya bayyana fatan cewa tattaunawar da ake yi a tsakanin Rasha da Ukiraniya a birnin Istanbul, za ta kai ga tsayar da tsagaita budewa juna wuta wanda kuma zai ga, kawo karshen yakin baki daya. Ofishin shugaban kasar Turkiya ya bayyana haka a yau Talata, ta kuma kara da  cewa,; Tattaunawar da aka gudanar a jiya Litinin a tsakanin Rasha da Ukiraniya a kuma fadar shugaban kasar Turkiyya dake birnin Istanbul tana cike da fata na tsayar da yakin. Kamfanin dilalncin labarun “Sputnik” na kasar rasha ya ambato majiyar fadar shugaban kasar ta Turkiya tana cewa; Shakka babu duk wata tattaunawa da bangarori za su zauna akan teburi, tana tattare da kyakkyawan fata, a dalilin haka,...
    Iftila’in ambaliyar ruwa a garin Mokwa a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja ta yi ajalin mutane sama da 200, yayin da wasu sama da 500 suka bata. Ambaliyar, wadda ita ce mafi muni a yankin cikin shekaru 60, ta shafi yankunan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ranar Laraba da ta gabata da daddare. Ɗaruruwan gidaje sun lalace, inda mutane da yawa suka rasa matsugunansu. Kafar yaɗa Labarai ta BBC ta ruwaito a ranar Litinin cewa yawan mutanen da suka mutu ya ƙaru zuwa sama da 200, kuma an dakatar da ayyukan ceto saboda hukumomi sun yanke ƙauna daga samun wasu da rai. Babbar Sallah: Farashin kayan miya ya yi tashin...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Dangantakar Iran da Lebanon tarihi ce, mai tushe, kuma ta ginu ne bisa mutunta juna Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana alakar da ke tsakaninta da kasar Lebanon a matsayin mai tarihi, mai tushe, kuma ta ginu ce bisa mutunta juna. Ya ce: “Kasashen biyu sun kuduri aniyar bunkasa wannan alakar. A jawabin da ya yi a filin jirgin sama na birnin Beirut, inda wakilin kakakin majalisar dokokin kasar Lebanon ya tarbe shi, Araqchi ya yi nuni da cewa ziyarar wani bangare ne na rangadin da yake yi a yankin bayan ziyarar da ya kai birnin Alkahira na Masar, kuma zai gana da jami’an kasar ta Lebanon. Ya kara da...
    Ministan harkokin wajen Iran ya soki rahoton hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya yayin ganawa da Grossi a birnin Alkahira Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya soki sabon rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan shirin makamashin nukiliyar kasar Iran yayin ganawarsa da babban darektan hukumar ta makamashin nukiliya ta duniya Rafa’el Grossi a birnin Alkahira. A yayin taron, wanda aka gudanar a babban birnin Masar bisa bukatar Grossi, Araqchi ya tunatar da hukumar ta IAEA da babban daraktan ta game da alhakin da ya rataya a wuyansu na gudanar da ayyukansu cikin kwarewa. Har ila yau ministan harkokin wajen na Iran ya soki zarge-zarge marasa tushe da ke kunshe cikin sabon rahoton hukumar ta IAEA...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Tsibiran guda uku na Tunb Babba da Tunb Karami da Abu Musa yankuna ne Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da ikirari da kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Fasha (PGCC) ta yi dangane da tsibiran Iran guda uku, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da tsaro da muradun kasar a cikin tsibiran guda uku. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya jaddada matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da yin watsi da ikirarin da ke kunshe a cikin bayanin karshe na taron ministocin harkokin wajen kasashen yankin tekun Fasha karo na...
    Sojojin mamayar Isra’ilan sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi a birnin Rafah, inda suka kashe mutane da dama a kusa da cibiyar rarraba kayan agaji Fararen hula 23 ne suka yi shahada yayin da wasu kusan 200 suka jikkata a yau Talata lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka bude wuta kan mai uwa da wabi wa fararen hula a kusa da wata cibiyar rarraba kayan agaji a birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza. Majiyoyin kiwon lafiya sun bayyana cewa: Shahidan sun fadi ne a lokacin da suke jiran agajin jin kai a titunan Rafah, lokacin da jirage masu saukar ungulu suka bude musu wuta. An tantance biyar daga cikin shahidan, yayin da wasu fiye da 20 kuma...
    Masu sayar da rago a jihar Zamfara sun nuna damuwarsu kan rashin samun ciniki gabanin bikin Eid-el-Kabir, duk da cewa ana samun dabbobi a kasuwanni.   Shugaban kungiyar masu sayar da dabbobi ta jihar Zamfara, Malam Saidu Ibrahim Gusau ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan rediyon Najeriya a Gusau.   Malam Gusau ya bayyana cewa, duk da cewa ana samun raguna da yawa, amma an samu karancin masu saye.   Sai dai ya bayyana fatan cewa lamarin zai iya gyaruwa yayin da bukukuwan Sallah ke kara gabatowa.   “Amma idan abubuwa sun ci gaba da haka, to gaskiya, akwai matsala ta gaske,”   “Har yanzu, na yi imani cewa da sauran kwanaki abubuwa za su iya canzawa, in...
    Dillalan rago a jihar Kano sun nuna damuwarsu kan rashin zuwan masaya da suke fuskanta duk da ‘yan kwanaki da suka rage ayi bukukuwan Sallah.   Ziyarar da aka kai kasuwar dabbobi ta Gandun Albasa ta nuna cewa, da yawa daga cikin masu sayar da kayayyaki sun shafe tsawon yini ba tare da yin cinikin komai ba, inda masu saye kadan ke zuwa sayen dabbobin hadaya.   Da yake zantawa da gidan rediyon Najeriya shugaban kasuwar dabbobi ta Gandun Albasa, Alhaji Yusuf Ahmed Muhammad ya bayyana cewa duk da cewa mutane na zuwa kasuwar domin tambayar farashin, amma a zahiri kadan ne ke saye.   Ya bayyana cewa yayin da wasu kwastomomi ke siyan kananan raguna da farashinsu ya kai...
    ’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa. A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan ke tafiya a kan babban titin zuwa Kontagora a Jihar Neja. A lokacin ’yan bindigar sun buƙaci kuɗin fansa Naira miliyan 10 daga iyalan mutumin, wanda tsohon ma’aikacin gwamnati ne. Ba su sako shi ba sai a ranar Litinin, bayan da suka karɓi ƙarin Naira miliyan 20 daga iyalansa, jimilla Naira miliyan 30 ke nan. A lokacin da suka yi garkuwa da ma’auratan sun buƙaci...
    ’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa. A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan ke tafiya a kan babban titin zuwa Kontagora a Jihar Neja. A lokacin ’yan bindigar sun buƙaci kuɗin fansa Naira miliyan 10 daga iyalan mutumin, wanda tsohon ma’aikacin gwamnati ne. Ba su sako shi ba sai a ranar Litinin, bayan da suka karɓi ƙarin Naira miliyan 20 daga iyalansa, jimilla Naira miliyan 30 ke nan. A lokacin da suka yi garkuwa da ma’auratan sun buƙaci...
    Ya ce an kai farmakin ne a kudancin yankin Mai-Galma a karamar hukumar Maru, domin dakile wani gagarumin farmaki da ‘yan bindiga suka shirya kai wa wasu al’ummomi.   Bayan harin ta sama, sai aka tura sojojin kasa domin bin sahun ‘yan ta’addan da aka tarwatsa.   “Sun tabbatar da lalata babura tare da kashe ‘yan ta’adda sama da 20.   “Abin takaici, a yayin harin ta sama, ‘yan banga biyu a yankin, an kuskure su yayin da wasu kuma suka samu raunuka,” inji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
     Ministan harkokin wajen Jamhuriyar musuluinci ta Iran wanda ya kai Ziyarar aiki kasar Masar ya bayyana cewa, cinikayya a tsakanin kasashen biyu za ta karu. Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya gabatar da taron manema labaru na hadin gwiwa da takwaransa na kasar Masar ya ce: “A bisa yarjejeniyar da bangarorin biyu su ka cimmawa za a kara girman kasuwancin da ake tsakanin Iran da Masar.” Abbas Aragchi ya godewa mai masaukinsa na Masar Badar Abdulatif, saboda tattaunawa mai muhimmanci da su ka yi.” Bugu da kari Abbas Arakci ya yi wa shugaban kasar Masar godiya saboda ganawa da ya yi da shi, yace: Wannan Shi ne ganawata ta hudu da shugaban da shi daga sheakarar da ta gabata’....
    Sabon fira ministan kasar Sudan Kamil Idris ya yi kira ga kasashen waje masu taimaka wa dakarun daukin gaggawa “RSF” da su kawo karshen taimakon da suke bawa masu aikata laifi.” Idris wanda yake jawabin bayan kama aiki a jiya ya ce; Jami’an tsaro da kuma mahukuntan kasar ta Sudan suna da cikakken goyon baya a kasar don kawo karsehn ‘yan tawaye, masu dauke da makamai.” Idris ya kuma ce; A shirye yake ya yi wa kasa aiki a cikin kekyawar anniyya da kwazo.” Gwamantin kasar Sudan dai tana zargin Hadaddiyar Daular Larabawa da taimaka wa dakarun kai daukin gaggawa “RFS” wacce ta dauki shekaru biyu tana fafatawa da sojojin kasar. Wasu daga cikin  kasashen da Sudan take  zargi da...
     Gwamnan Babban Bankin Iran ya wanda yake Ziyara a kasar China ya gabaatr da shawarar a kafa bankin hadin gwiwa a tsakanin kasashe mambobi a kungiyar Shangai. Muhammad Riza Farzin ya isa kasar ta China ne domin halartar taron gwamnonin manyan bankunan kasashen da suke mambobi a cikin wanann kungiya, domin yin nazarin hanyoyin aiki tare a tsakaninsu da kuma musayar kudade. Muhammad Riza Farzin ya kuma kara da cewa; Daga cikin ajandar taron kungiyar a China, akwai tattauna batun kafa bankin hadin gwiwa wanda daga cikin ayyukansa a akwai aiwatar da hada-hadar kudade da mu’amala a tsakanin Bankuna.” Gwamnan babban bankin na Iran ya bayyana cewa, wannan kungiyar tana da matukar muhimmanci, domin tana kunshe da kasashe goma daga...
    Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Fidan ya jaddada goyon bayan da kasarsa take bai wa tattaunawar da ake yi a tsakanin Rasha da Ukiraniya, ya kuma kara da cewa; Ana yin nazarin yadda za a gana, a kuma tattauna tsakanin shugabannin kasashen biyu.” Fidan ya kuma bayyana fatansa na ganin cewa tattaunawar da aka bude a yau ta kai ga haifar da daa mai ido. Haka nan kuma ya ce, kasarsa za ta yi duk abinda za ta iya, domin ganin cewa kasashen biyu sun kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu.  Kafar watsa labaru ta Axios; ta ambato majiyar Ukiraniya na cewa, Rasha ta gabatar da tsarin zaman lafiya wanda ya kunshi yadda za a kawo karshen yaki....
    Gwamnatin Kano ta ba makarantu hutun kwanaki goma domin bikin Babbar Sallah da za a yi ranar Juma’ar wannan makon. Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa makarantun za su fara hutun ne daga ranar Laraba, 4 ga watan nan na Yuni da muke ciki, zuwa ranar Lahadi, 15 ga wata. Sanarwar ta kuma bukaci iyaye da ’ya’yansu suke makarantun kwana da su je da wuri domin daukar yaran a ranar Laraba. Kwamishinan mai kula da ma’aikatar, Ali Makoda, ya kuma bukaci iyaye da su tabbata daliban sun dawo makaranta a kan kari bayan kare hutun Babbar Sallar. An lakaɗa wa Mataimakin Firinsifal duka saboda hana satar a jarabawa Uba ya harbe ɗansa har lahira...
    Rundunar ‘yansanda a jihar Gombe ta umurci rufe duk wata tashar sauka ko daukar fasinjoji a cikin garin Gombe ciki har da fitacciyar tashar Dadin Kowa, inda ta ce, tashar Ibrahim Hassan Dan-Kwambo ce kadai halastacciya.   Bugu da kari, motocin haya da ke dauke da amintaccen launin kala na gwamnati a cikin garin Gombe ne kadai suke da izinin zirga-zirgar daukar fasinjoji a birnin. Gwamnatin Jihar Gombe Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniya Domin Gina Mayankar Dabbobi Ma’aikatar Tsaron Kasar Sin Ta Maida Martani Game Da Munanan Kalaman Sakataren Tsaron Amurka Kan Kasar Sin Wannan umarni na kunshe ne acikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, a ranar...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Rahoton IAEA na nuna son kai kuma an shirya shi ne a karkashin tasirin wasu kasashe Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta fitar ya kunshi maimaici da wuce gona da iri, yana mai jaddada cewa, an shirya wannan rahoton ne karkashin tasirin wasu kasashen Turai. Ya bayyana takaicinsa kan yadda kasashen yammacin duniya ke cutar da martabar wata kungiya ta duniya ta hanyar siyasantar da ayyukanta. A farkon taron manema labarai na mako-mako, Baghaei ya yi la’akari da zagayowar ranar wafatin Imam Khumaini (Allah ya kara masa yarda) da shahidan juyin juya halin Musulunci. Ya kara da cewa: Ma’aikatar harkokin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da shugaban kasar Masar a birnin Alkahira Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi a yau Litinin. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakchi ya isa birnin Alkahira da yammacin jiya Lahadi domin tattaunawa da manyan jami’an kasar Masar. A yayin wannan ziyara, Araqchi ya gana da ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty da shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi inda suka tattauna batutuwan baya-bayan nan a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da ci gaban yankin, musamman batun kalubalantar laifukan haramtacciyar kasar Isra’ila, da kuma wasu batutuwan kasa da kasa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da Shirin ministan harkokin...
    Sojojin Yemen sun kai jerin hare-hare har sau 4 kan filin jirgin saman Ben Gurion tare da wasu wurare masu muhimmanci a cikin Isra’ila Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji masu tsanani guda hudu a kan filin jirgin sama na Lod, wanda aka fi sani da “Ben Gurion” a haramtacciyar kasar Isra’ila, da kuma wasu muhimman wurare a yankunan Jaffa, Ashdod da Umm al-Rashrash a cikin Palasdinu da aka mamaye. Rundunar sojin Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau cewa: Rundunarta ta kai wasu hare-haren soji masu inganci a kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makamai masu linzami. Dakarun sojin sun tabbatar da cewa: wannan...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula da suka yi tawaga zuwa wajen raba kayan agajin jin kai a garin Rafah Rahotonni sun bayyana cewa: A rana ta biyu a jere, sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan al’ummar zirin Gaza da ke fama da yunwa. Shafin yanar gizo na Falestine Today ya watsa rahoton cewa: A safiyar yau Litinin 2 ga watan Yunin shekara ta 2025, sojojin mamayar Isra’ila sun aiwatar da wani sabon laifi ta hanyar kai hare-hare kan Falasdinawa a kusa da cibiyar bada agajin Amurka da ke birnin Rafah. Ya zuwa yanzu dai wannan aika-aika ya yi sanadin shahadan Falasdinawa 3 tare da raunata wasu 60, ba a ma...
    Wani yaro ɗan shekara 15 ya rasa ransa bayan mahaifinsa ya harbe shi bisa kuskure, yana zaton biri ne. Wannan lamari mai ban tausayi ya faru ne a gonar magidancin inda shi da ɗan nasa suke aiki, a yankin Iye Ekiti da ke Ƙaramar Hukumar Ilejemeje ta Jihar Ekiti. Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ekiti,  Joseph Eribo, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau a Ado-Ekiti. Ya bayyana cewa manomin ya daɗe yana fama da hare-haren birai a gonarsa kuma ya kai bindiga domin kare amfanin gonarsa. Jirgin soji ya kashe ’yan sa-kai 20 da ke fatattakar ’yan bindiga a Zamfara An lakaɗa wa Mataimakin Firinsifal duka saboda hana satar a jarabawa Binciken farko ya nuna cewa mahaifin ya lura...
    A wani lokaci yau Litini ne ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi zai fara ziyarar kwanaki biyu a kasashen Masar da Lebanon. Yayin ziyarar Araghchi zai gana da manyan jami’an Masar da na Lebanon domin tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu dama rikicin yankin. Ziyarar Araghchi a Masar za ta gudana ne bisa gayyatar takwaransa na Masar Badr Abdelatty. Ana sa ran ministan harkokin wajen na Iran zai gana da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi, da takwaransa Badr Abdelatty, da kuma wasu masu fada a ji a fannin tattalin arzikin Masar. Da yake karin haske kan manufar ziyarar, mai kula da harkokin Iran a Alkahira ya ce, rikice-rikicen yankin da suka hada da hare-haren wuce gona da iri na...
    Kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun bayyana rashin jin dadinsu ga Isra’ila, kan hana su ziyartar yankunan Falasdinawa Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun bayyana rashin jin dadinsu ga gwamnatin Isra’ila, game da rashin amincewa da tawagar kungiyar kasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gabar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban Falasdinawa. A wani taron manema labarai, ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al Sa’ud, ya ce matakin da Isra’ila ta dauka kamar watsi ne da tayin zaman lafiya. A dai tsara a wannan Lahadi ne ministocin kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Jordan, Qatar, da Turkiyya, karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan za su isa birnin Ramallah domin ganawa...
    Iran ta gargadi kasashen yamma aka daukar duk wani irin mataki kan ta a daidai lokain da ake shirin gudanar da taron gwamnonin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya a mako mai zuwa. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya yi watsi da rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, yana mai gargadin daukar matakin da ya dace. Kazem Gharibabadi ya yi wadannan kalamai ne, bayan da hukumar ta IAEA ta yi zargi a cikin wani rahotonta na sirri ga kasashe mambobinta cewa Iran ta gaza bayar da rahoton ayyukanta na nukiliya a wasu wurare uku da ba a bayyana ba, tare...
    Jami’ai a Falasdinu sun ce akalla mutum 31 ne sukayi shahada sannan wasu sama da 150 sun jikkata, bayan wani hari da Isra’ila ta kai kusa da wurin rabon abinci a birnin Rafah. Dama shugaban hukumar MDD da ke kula da yan gudun hijirar Falasdinawa, Philippe Lazzarini, ya ce rabon kayan agajin ya zama tarkon mutuwa. Lamarin dai ya faru ne a kusa da wata cibiyar rarraba kayan abinci da gidauniyar agaji ta Gaza (GHF) ke gudanarwa, wani kamfani mai zaman kansa da ke samun goyon bayan Isra’ila da Amurka da kungiyoyin agaji na kasa da kasa suka yi suka. Kakakin kungiyar Hamas Sami Abu Zohri yayi Allah wadai da gwamnatin Isra’ila kan harin da ta aikata a rabon kayan...
     Mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da cewa a ranar hawan arfa na bana, za a fassara hudubar da za a yi da harsuna 34 daga cikinsu da akwai Hausa da filatanci. Wasu harsunan Afirka da za a fassara hudubar ta Arfa da su, sun hada yarabanci, Sawahili, Somali da kuma Amharic na kasar Habasha. A bisa sanarwar da kasar Saudiyya ta yi na ganin watan zulhijja, a ranar 27 ga watan Mayu, za a yi hawan Arfa a ranar 5 ga watan na Mayu.
    Sa’oi kadai da su ka gabata jiniyar gargadi ta kada a cikin garuruwa da sansanonin ‘yan share wuri zauna 300 a HKI saboda  makami mai linzami da mutane Yemen su ka harba.  Kafafen watsa labarun ‘yan sahayoniya sun ambaci cewa; an rufe filin saukar jiragen saman a “Ben Gorion” da kuma dakatar da kai da komowar jiragen sama. Kafafen watsa labarun na HKI sun ambaci cewa; Miliyoyin mutane ne su ka gudu zuwa Mabuya. Wannan sabon harin dai na sojojin Yemen yana zuwa ne a karkashin abinda sojojin na Yemen su ka kira, kakaba takunkumi na sama da ruwa akan HKI, tare da yin kira ga kamfanonin jiragen sama da na ruwa da su kauracewa zuwa wannan haramtacciyar kasa. Filin...
    Mataimakin shugaban kungiyar Iraniyawa masu bayar da kyautar gabban jikinsu ga mabukata, Umid Qabadi, ya bayyana cewa; A cikin shekaru 25 da su ka gabata, yadda ake kyautar gabban jiki domin yin dashe a duniya ya karu da kaso 70%, kuma Iran ce ta farko wajen yin dashen koda, har ma ana yi ma ta kirari da; Sarauniyar dashen koda.” A yayin wani taro na girmama masu bayar da kyautar gabban jikin nasu domin yi dashe ga mabukata a gundunar Qazwin, mataimakin shugaban kungiyar Umid Qabadi ya ce; Iran ce ta farko a duniya wajen yin dashen gabobi ga marasa lafiya mabukata. Qabadi ya yi ishara da wajabci ganin an bunkasa wannan al’ada ta bayar da gabobin jiki domin yin...
    Ya bayyana kamen na su biyo bayan kama wasu alhazai biyu – Ibrahim Umar Mustapha da Muhammad Siraj Shifado a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, da ke Kano a ranar Litinin 26 ga watan Mayu.   An kama mutanen biyu ne a lokacin da ake tantance fasinjojin jirgin na Ethiopian Airline ET 940 da zai tafi zuwa Jedda, ta kasar Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna da Grossi kan sabbin abubuwan da suka shafi tattaunawar nukiliyar Iran Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi da Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya Rafael Grossi sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka shafi tattaunawar nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakabawa Iran a wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho. A yayin tattaunawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan sabon ci gaban da aka samu a shawarwarin nukiliyar da kuma dage takunkumin. Sun kuma tattauna rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan Iran. Haka nan kuma yayin da yake ishara da yadda Iran ke ci gaba da ba da hadin kai ga hukumar ta IAEA, da aiwatar da...
    Iran ta gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da wasu kasashe Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’ar kasa da kasa Kazem Gharibabadi, ya gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA da wasu kasashen duniya kan ci gaba da bin tafarki maras kyau da suka yi a baya, yana mai jaddada cewa Iran za ta dauki natakin da ya dace daidai ayyukan da sauran bangarori suka dauka. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a na kasa da kasa ya mayar da martani a jiya Lahadi kan rahoton babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi kan wasu batutuwan kariya da suka shafi Jamhuriyar...
      Gwamna Yusuf wanda a halin yanzu yake kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin 2025, ya bayar da umarnin ware ranar Litinin 2 ga watan Yunin 2025 a matsayin ranar hutu domin bai wa al’ummar damar yin jimami tare da yi wa wadanda suka rasu addu’a.   Ya kuma yi kira ga limamai da daukacin al’umma a fadin jihar, da su yi addu’o’i na musamman ga wadanda abin ya shafa da kuma karfafa wa iyalansu da suka rasu.   Gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa, gwamnati na daukar matakan tallafawa wadanda suka jikkata da kuma iyalan wadanda abin ya shafa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
    Iran ta tabbatar da cewa ta samu shawarar da Amurka ta gabatar mata daga hannun kasar Oman game da shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya da ake tattaunawa a kai. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa Iran ta samu wani bangare na shawarwarin daga Amurka daga Oman mai shiga tsakani kan batun a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X. Ya karbi sakon ne daga hannun takwaransa na Oman Badr Albusaidi, wanda ya gudanar da wata gajeriyar ziyara a Tehran. Saidai ministan harkokin wajen Iran din bai bayyana abinda shawarwarin ke kunshe da ba, amma ya jaddada cewa za a duba su a kuma mayar da amsa wacce ta yi daidai da muradin...
    Bayanai na nuni da cewa gwamnatin Isra’ila ta hana tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da dama shiga gabar yammacin kogin Jordan da ta mamaye domin wani taro a birnin Ramallah. Isra’ila dai ta ce ba za ta amince da tawagar ministocin kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya su ziyarci yankin Isra’ila saboda ta lura hukumomin Falasdinawan na shirin yin amfani da ziyarar ne wajen farfado da kiran samar da kasar Falasdinawa. Wani jami’in Isra’ila ya shaidawa tashar talabijin ta CNN a ranar Juma’a cewa gwamnatin sahyoniyawan ba za ta hada kai da hukumar Falasdinu ta PA ba da ke neman karbar bakuncin tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya. Jami’in ya bayyana ziyarar a matsayin tsokana, yana mai...
    Iran ta soki sabon rahoton da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya fitar, tana mai cewa rahoto ne dake kunshe da tuhume-tuhume mara tushe kan shirin nukiliyar kasar. A wata tattaunawa ta wayar tarho da babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Tehran za ta mayar da martani ga duk wani matakin da bai dace ba daga kasashen Turai da Amurka. Faransa, Jamus da kuma Ingila, tare da goyon bayan Washington, suna son yin amfani da wannan rahoto don aiwatar da wani tsari da zai ba da damar maido da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran. A cikin rahoton nasa, Rafael Grossi ya bayyana...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa JMI ta gina shirinta na makamashin nukliya ne kan fahinta da kuma kundin tsarin mulkin kasar wanda yayi tir da mamaya da kuma babakere. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Asabar a hubbaren Imam Ruhullah Al-khomaini (q) wanda ya kafa JMI. Ministan da sauran manya-manyan ma’aikata a ma’aikatar harkokin wajen kasar sun je hubbaren Imam ne don jadda bai’a ko alkawali da shi kan tafiya a kan tafarkin da ya barsu a kai. A cikin wani wuri a Jawabinsa Ministan ya kara da cewa a cikin kundin tsarin mulkin JMI ya zo kan cewa Iran ba zata danne wata kasa...
    Kamfanin Barakat, mai samar da magunguna a nan JMI ya kaddamarda sabbin magunguna har 23 wanda kamfanin ya samar a cikin gida daga ciki har da riga kafi mai suna HPV. Kamfanin dilancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan ci gaban da kamfanin Barakat ya samu mataki ne mai girma a fagen samar da magungunan da kasar Iran take bukata a cikin gida. Kuma wannan zai bude kofar samar da magunguna ko riga kafi masu tsada da wuyan samu a duniya na cututtuka daji ko (cancer) a kasar. Ministan kiwon lafiya na JMI Mohammad Reza Zafarqandi, a jawabinda da ya gabatar a bikin gabatar da magungunan ya ce, gamayyar kamfanonin samar da magunguna na kasar Iran wato...
    A karon farko, rundunar tsaron Indiya ta tabbatar da cewa ta rasa wasu jiragen yaƙi a yayin arangama mai tsanani da suka fafata da Pakistan a farkon watan Mayu. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Babban Hafsan Tsaro na Indiya, Anil Chauhan, a taron Shangri-La Dialogue, babban taron tsaro na Asiya, a Singapore. Tun da farko, jami’an Indiya sun yi ta musanta duk wata asarar jiragen sama a cikin wannan arangama, wanda aka fara ne bayan wani hari da aka kai wa masu yawon bude ido a yankin Kashmir da Indiya ke mulka a watan Afrilu, wanda Indiya ta dora alhakinsa kan Pakistan. Ita kuwa Pakistan, ta yi ikirarin cewa ta harbo jiragen Indiya da dama, ciki har da...
    Shugaban hukumar bada agajin gaggawa a jihar Naija na tarayyar Najeriya NSEMA ya basa sanarwan cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwa a ranar Alhamis data gabata a karamar hukumar Mokwa ya kai 151 bayan an sake gano karin gawakin mutane 36. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto Abdullahi Arah yana cewa banda wadanda suka rasa rayukansu mutane 11 ne suka ji rauni. Sannan mutane 3018 suka kauracewa gidajensu sanadiyyar ambaliyar ruwa bayan ruwan sama na sa’oii masu yawa. Arah yace gidaje 503 ne suka rushe a jihar sannan wasu 265 suka lalace. Banda haka akwai gadoji biyu da hanyoyi biyu wadanda ruwan ya sharesu.
    Aƙalla mutum 20 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da tawagar Jihar Kano da ke dawowa daga gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa (NSF) da aka kammala a Jihar Ogun. Lamarin na ban tausayi ya faru ne a ranar Asabar a garin Dakatsalle, kimanin kilomita 50 daga Kano, yayin da tawagar ke gab da isa gida. Rahotannin farko daga masu bada agajin gaggawa da shaidun gani da ido sun nuna cewa waɗanda suka rasa rayukansu a hatsarin sun haɗa da ’yan wasa da ɗan jarida, ma’aikatan lafiya da jami’an gudanar da harkokin wasanni. Shugaban ƙungiyar marubutan wasanni ta Najeriya (SWAN) reshen Kano, Zahraddeen Saleh, ya tabbatar da wannan mummunan lamari. Ya kuma ƙara...
    Kyaftin din tawagar Super Eagles ta Nijeriya Ahmed Musa, ya auri matarsa ta 4, Asmau Moriki, a wani biki na sirri da aka gudanar a jihar Kano, Musa da amaryarshi Asmau sun zama mata da miji watanni kadan bayan haduwarsu, Musa ya bar sansanin tawagar Super Eagles dake birnin Landan domin ya halarci bikin wanda aka gudanar a birnin Kano. Dan wasan dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya shiga wasan da Nijeriya ta doke Ghana da ci 2-1 a minti 60 na wasan, Musa na daya daga cikin yan wasan da sukafi taka leda a tarihin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya inda kuma ya zamo wanda yafi jefawa Nijeriya kwallaye a gasar kofin Duniya a...
    Adadin mutanen da suka mutu a mummunar ibtila’in ambaliya a Jihar Neja ya karu zuwa mutum 151. Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ce ta sanar cewa mutane 11 sun jikkata, yayin da mutane 3,018 suka rasa matsuguninsu a ibtila’in na ƙaramar hukumar Mokwa a safiyar Asabar. Kakakin hukumar, Ibrahim Hussaini, ya bayyana cewa ambaliyar ta shafi gidaje 265 da kuma magidanta 503. Ya ƙara da cewa yankuna uku, da suka hada da Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, sun nutse sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka yi na tsawon sa’o’i da dare a ranar Laraba. Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a...
    Adadin mutanen da suka mutu a mummunar ibtila’in ambaliya a Jihar Neja ya karu zuwa mutum 151. Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ce ta sanar cewa mutane 11 sun jikkata, yayin da mutane 3,018 suka rasa matsuguninsu a ibtila’in na ƙaramar hukumar Mokwa a safiyar Asabar. Kakakin hukumar, Ibrahim Hussaini, ya bayyana cewa ambaliyar ta shafi gidaje 265 da kuma magidanta 503. Ya ƙara da cewa yankuna uku, da suka hada da Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, sun nutse sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka yi na tsawon sa’o’i da dare a ranar Laraba. Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a...
    Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya jaddada cewa: Ba za su taba yin watsi da ‘yancin su na mallakar makamashin nukiliya na zaman lafiya ba Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya jaddada cewa: Iran ba ta neman mallakar makamin nukiliya, kuma ba za ta yi watsi da hakkinta na amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya da lumana ba. Ya kara da cewa: Iran tana inganta sinadarin Uranium kuma za ta ci gaba da yin hakan domin bunkasa harkokin ci gaban kasarta musamman harkar lafiya, wutan lantarki, likitanci, noma da sauransu. Limamin Juma’ar Ayatullah Ahmad Khatami ya bayyana cewa: Hakika dogaro da...
    Mazauna Babban Birnin Tarayya za su fuskanci katsewar ruwan sha na tsawon makonni biyu, kamar yadda Hukumar Kula da Ruwa ta yankin ta sanar. Rashin ruwan, wanda ya fara ranar Juma’a, 30 ga Mayu, ana sa ran za ta ci gaba har zuwa ranar Juma’a, 13 ga Yuni. Matsalar ta samo asali ne daga ayyukan gyare-gyare da ake yi a tashoshin tace ruwa na madatsar ruwa ta Lower Usuma Dam. A cewar sanarwar da hukumar ta fitar, gyare-gyaren sun shafi muhimmin aikin haɗa kayan aikin lantarki da injiniya, wanda babban bangare ne na aikin inganta matatar. Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a kansa a Borno...
    Bangarorin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa sun kai hari kan sojojin mamaya a wani farmakin hadin gwiwa da suka kai a Khan Yunus Dakarun Sarayal-Quds bangaren sojin kungiyar Jihadul-Islami da kuma dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwagrmayar Musulunci ta Hamas sun tabbatar da cewa: Sun yi nasarar kashe sojojin mamayar Isra’ila tare da raunata wasu a farmakin hadin gwiwa da suka kai kan yankin “Unguwar Turawa” a kudu maso gabashin Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza. Dakarun Sarayal-Quds a cikin wani takaitaccen bayani da suka fitar sun bayyana cewa: Sun gudanar da wani farmakin hadin gwiwa tare da dakarun Al-Qassam kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da suka kutsa cikin yankin Unguwar Turawa a kudu maso gabashin Khan Yunus, bayan da...
    Dakarun gwagwarmayar kasar Yemen sun bayyana cewa: Za su mayar da jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila abin ba’a Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat, ya tabbatar da cewa: Tsaron sararin samaniyar sojojin kasar Yemen zai iya tunkarar jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da suke kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen. Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat ya shaidawa tashar talabijin ta Al-Mayadeen cewa: Kariyar tsaron sararin samaniyar sojojin Yemen za ta mayar da jirgin saman makiya ‘yan sahayoniyya abin izgili a cikin kwanaki masu zuwa. Al-Mashat ya jaddada cewa: Sojojin kasar Yemen za su iya tunkarar jiragen saman yakin yahudawan sahayoniyya ba tare da haifar da wata illa ga...
    Jami’ar Jos ce ta zama gwarzon gasar wasannin ma’aikatan jami’o’in Nijeriya karo na 14 (NUSSA), wadda Jami’ar Bayero da ke Kano ta karɓi bakuncinta. Jami’ar ta Jos ta lashe lambobin yabo guda 13, ciki har da Zinare 7, Azurfa 3 da Tagulla 3, wanda ya ba ta damar darewa saman teburin nasarori. A matsayi na biyu kuma, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria, ta samu nasarar lashe lambobin yabo 12 – zinare 6, azurfa 3 da tagulla 3. Jami’ar Tarayya ta Dutsinma ta zo ta uku da zinare 4, azurfa 4 da tagulla 5. Gasar Wasanni Ta Kasa Wata Hanya Ce Ta Hada Kan Matasan Nijeriya– Obasanjo Kyawawan Halayen Annabawa Da Ke Nuni Da Cikarsu (AS) Babban abin da ya dauki hankali...
    Shugaban na Faransa ya ce Faransa za ta iya sanya takunkumi ga gwamnatin Isra’ila matukar ba ta kawo karshen killace Gaza ba, inda kuma ya bukaci kasashen duniya da kada su jajirce wajen tunkarar matsalar karancin abinci a Gaza. A wani taron manema labarai a Singapore a ranar Juma’a, Macron ya ce dole ne Turawa su “tsaurara matsayinsu na hadin gwiwa” kan Isra’ila, “idan babu wani mataki da ya dace da yanayin jin kai, a cikin sa’o’i da kwanaki masu zuwa” a zirin Gaza. Macron ya ce, “Katange ayyukan jin kai yana haifar da yanayi mara kyau,” yayin taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Firaministan Singapore Lawrence Wong. Ya yi wadannan kalamai ne a daidai lokacin da gwamnatin...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kirayi babbar mai kula da harkokin kasar Ostiriya da ke birnin Tehran domin nuna rashin amincewa da zarge-zargen data danganta da na ‘’tsokana” da hukumar leken asirin cikin gidan kasar ta Turai ta yi dangane da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Shugaban ofishin sashen yammacin Turai na ma’aikatar harkokin wajen Iran Alireza Molaqadimi ya gayyaci Michaela Pacher a ranar Juma’a, inda ya nuna bacin ran kasar iran game da zarge-zargen. A cikin rahotonta na shekara-shekara kan barazanar da duniya ke fuskanta, hukumar leken asiri ta kasar Ostiriya (DSN) ta yi ikirari a ranar Litinin cewa Iran na ci gaba da aiwatar da shirin kera makaman nukiliya tare da fadada karfinta na makamai masu...
    Jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana agajin abinci ga Falasdinawa da ke fama da yunwa a yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama laifin yaki. “Muna ganin abinci dake jibge a kan iyakoki kuma ba a ba da izinin shigar da shi ba a lokacin da jama’a a gefen iyakar ke fama da yunwa, a yayin da muke jin ministocin Isra’ila suna cewa sun ayin hakan ne don matsa lamba kan al’ummar Gaza,” in ji Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher a wata hira a ranar Jumma’a. Irin wannan na a matsayin laifin yaki ne,” in ji shi. Baya ga hakan...
    Hukumar lura da sufurin jiragen kasa ta kasar Sin, ta yi hasashen samun adadin zirga-zirgar fasinjoji ta jiragen kasa sama miliyan 80.5, yayin kwanaki biyar na hutun bikin Duanwu ko bikin tseren kwale kwale na bana. An fara samun dandazon matafiya ta jiragen kasa a kasar Sin tun daga yau Juma’a, kwana guda gabanin kwanakin hutun uku, yayin da ake sa ran kaiwa kololuwar yawan matafiyan a gobe Asabar, inda ake hasashen adadin zirga-zirgar zai kai kusan miliyan 18.3. Alkaluma daga kamfanin 12306, mai samar da hidimar yankar tikitin jiragen kasa na kasar Sin, sun nuna wuraren da matafiya suka fi yankar tikitin zuwa, wadanda suka hada da biranen Beijing, da Shanghai, da Guangzhou, da Chengdu, da Hangzhou. Sauran su...
    Wani mutum mai suna Adamu Muhammed Tenimu ya suma bayan da samu labarin cewa matarsa ​​ta haifi jarirai ’yan uku a asibitin koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Lokoja babban birnin Jihar Kogi ranar Juma’a. Shaidu sun ce, mutumin da ya ji cewa matarsa ​​ta haifi ‘ya’ya mata uku, sai ya faɗi ya suma a harabar asibitin nan take. Zazzaɓin Lassa da sanƙarau ya kashe mutum 366 a jihohi 24 – NCDC Shekaru 6: Don amfanin matasa mun inganta ilimi da noma — Gwamna Buni  Jami’an asibitin da masu jajantawa sun yi wa mutumin agaji inda cikin gaggawa aka samu ya farfaɗo. Jim kaɗan da farfaɗowarsa, Muhammed, wanda aka ce ya kasance mai neman aikin yi na tsawon shekaru, ya ce...
    Babbar jami’a a hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Shen Haiping, ta ce a shekarun baya bayan nan koshin lafiyar yaran kasar Sin na kara inganta. Jami’ar wadda ta bayyana hakan ga wani taron manema labarai a yau, ta ce a shekarar 2024, alkaluman mace-macen jarirai a kasar ya ragu zuwa jariri hudu cikin duk jarirai 1000, yayin da na yara ‘yan kasa da shekaru biyar ya ragu zuwa yara 5.6 cikin duk yara 1,000, adadin da ya yi kasa sosai cikin jerin kasashen duniya, dake rukunin masu al’ummun dake sama-sama a matsakaicin samun kudin shiga.   Shen Haiping ta kara da cewa, idan aka nazarci wadannan alkaluma, za a ga cewa cikin sama da shekaru goma da suka gabata,...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Makaman nukiliya ba su da gurbi a cikin akidar Jamhuriyar Musulunci ta Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da haƙƙin da doka ta tanada ba ta fannin inganta sinadarin uranium, domin inganta harkar kiwon lafiya, aikin gona da masana’antu, yana mai jaddada cewa: makaman nukiliya ba su da gurbi a cikin koyarwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yayin ziyarar da ya kai masarautar Oman, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, a wata hira da gidan talabijin na kasar, ya yi bayani kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu, da kuma muradun yankin da na kasa da kasa na Iran da Oman, da kuma muhimman batutuwan...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi tsokaci kan hasashe game da kusancin cimma yarjejeniyar nukiliyar da ke gudanarwa tsakanin Amurka da Iran Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Hanyar diflomasiyya tana bukatar a dage dukkan takunkumai da aka kakabawa Iran da kuma mutunta hakkin mallakar makamashin nukiliyar Iran, yana mai cewa: Hanyar cimma yarjejeniya ta ta’allaka ne ta kan teburin tattaunawa, ba ta hanyar kafafen yada labarai ba. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya fada a jiya Alhamis cewa: Kafafen yada labarai na yada jita-jita game da yarjejeniyar da ake shirin kullawa tsakanin Iran da Amurka. Araqchi ya ci gaba da yin tsokaci a shafinsa na Twitter a dandalin Twitter, inda ya ce: “Muna shakkar...
    Mai ba da shawara ga jagoran juyin juya halin Musulunci ya mayar da martani ga barazanar shugaban kasar Amurka kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran Ali Shamkhani mashawarcin Jagoran juyin juya halin Musulunci a fagen siyasa ya jaddada cewa: Iran kasa ce mai cin gashin kanta mai tsayayyen tsarin tsaro, al’umma masu tsayin daka, da jajayen layi. Ya jaddada cewa, “tattaunawa hanya ce ta ci gaba da kuma kiyaye moriyar kasa da mutunci, ba kayan aiki na tilastawa ko mika wuya ba.” Shamkhani ya rubuta a shafinsa na dandalin X cewa: “Burin isa ga cibiyoyin nukiliyar Iran da kuma ‘tarwatsa su’ ba komai ba ne illa mafarki da shugabannin Amurka da suka gabata sun kasance sun yi has ashen hakan. Ya...
    A tsawon kwanaki 602 a jere, sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa a yankin Zirin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da yakin da suke yi na kisan kiyashi a zirin Gaza, inda suka sake kaddamar da wani sabon yaki kan Gaza bayan tsagaita bude wuta. Hakan ya biyo bayan sauya ra’ayi da Fira ministan gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, bisa la’akari da goyon bayan siyasa da na soji da Amurka ke ba shi, a cikin shiru da kasashen duniya suka yi da kuma gazawar da ba a taba gani ba daga kungiyoyin kasa da kasa. Kafofin yada labaran Falasdinu sun ruwaito cewa: Sojojin...
    Wani masanin tattalin arziki, Ademola Adigun, ya ce, duk da janye tallafin mai, sashin mai a Nijeriya ba ya tafiya kan ka’ida. Ya yi bayanin cewa kawai an rage biyan tallafin ne amma ba wai an daina biya gaba daya ba, kuma babu gasa tsakanin ‘yan kasuwa wanda shi ma na haifar da nakasu.  Adigun ya soki tsarin sayar da danyen mai a kan kudin naira domin zabar da masu saye, ta yadda za a samar da lamari kamar na ‘ya’yan mowa da bora, da ke iya korar ‘yan kasuwa masu zaman kansu, lamarin da ya tilasta wa kusan gidajen mai 5,000 rufewa.      Adigun, duk da ya nuna farin ciki kan yadda masu zuba hannun jari suke nuna sha’awar zuba...
    Wasu mutum 12 ’yan gida daya da almajirai sama da 50 na cikin mutanen da suka rasu a ambaliyar ruwan da ta afka wa yankin Tiffin Maza da Anguwan Hausawa na karamar hukumar Mokwa a jihar Neja a ranar Laraba. Ambaliyar, wacce ta biyo bayan wani mamakon ruwan sama da aka tafka a daren na Laraba, ta kuma lalata dukiyoyi da dama, yayin da har yanzu ake ci gaba da neman wasu mutanen da suka bace. Garin Mokwa dai ya shahara da zama wani zango na direbobin manyan motoci, wanda hakan ya sa garin ya zama daya daga cikin mafiya hada-hadar mutane a jihar ta Neja. NAHCON ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin 2025 Ambaliyar ruwa ta kashe sama da...
    Kasar Brazil ta jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya A yayin ganawarsa da sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran, mataimaki na musamman ga shugaban kasar Brazil ya sanar da cewa kasarsa tana goyon bayan ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na yin amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya da kuma aiwatar da shirin inganta sinadarin Uranium don bunkasa harkokin ilimi cikin gida ta hanyar fasahar makamashin nukiliya. A yayin ganawar tasu, Ali Akbar Ahmadian, sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran, da mataimaki na musamman ga shugaban kasar Brazil Celso Amorim, sun jaddada muhimmancin ci gaba da gudanar da hadin gwiwa da tuntubar juna tsakanin kasashen biyu masu cin gashin...
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Suna gudanar da kyakkyawar tattaunawa da Iran Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Amurka na tattaunawa da Iran sosai kan Shirin makamashin nukiliyarta. Donald Trump ya fada a ranar Laraba cewa:  “Ya damu da abin da ke faruwa a Ukraine, kuma bai sani ba ko Putin na son kawo karshen yakin,” a cewar gidan talabijin na Al Jazeera. Dangane da tattaunawar da aka yi da Iran, Trump ya ce: “Suna tattaunawa mai kyau da Iran.” Trump ya ce: Dole ne bangarorin Gaza su amince da takardar da Steve Witkoff wakilin Amurka na musamman a yankin Gabas ta Tsakiya ya gabatar.
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Suna gudanar da kyakkyawar tattaunawa da Iran Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Amurka na tattaunawa da Iran sosai kan Shirin makamashin nukiliyarta. Donald Trump ya fada a ranar Laraba cewa:  “Ya damu da abin da ke faruwa a Ukraine, kuma bai sani ba ko Putin na son kawo karshen yakin,” a cewar gidan talabijin na Al Jazeera. Dangane da tattaunawar da aka yi da Iran, Trump ya ce: “Suna tattaunawa mai kyau da Iran.” Trump ya ce: Dole ne bangarorin Gaza su amince da takardar da Steve Witkoff wakilin Amurka na musamman a yankin Gabas ta Tsakiya ya gabatar.
    Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Bureij da ke kudancin Zirin Gaza Falasdinawa fararen hula 23 ne suka shahada tare da jikkata wani adadi masu yawa a wani sabon kisan kiyashi da sojojin gwamnatin mamayar Isra’ila suka yi a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Bureij da ke kudancin zirin Gaza. Rahotonni sun bayyana cewa: sojojin mamayar sun kai hare-hare ne ta hanyar jiragen saman kan gidajen jama’a, ciki har da gidan iyalan Al-Qarnawi da ke gabashin sansanin. Haka hare-haren sun yi sanadiyyar shahadar wani Bafalasdine a yankin Qizan al-Najjar da ke kudancin Khan Yunus. Sannan jami’an ceto sun gano gawar wani Bafalasdine a wani gidan da aka...
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran ya gana da ministan harkokin cikin gida da kuma gwamnonin Larduna, inda ya basu shawarar amfanin da kekyawar yanayin da kasar take ciki don ciyar da kasar Gaba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jagoran yana cewa, a halin yanzu kasar Iran bata fuskantan watai annoba kamar CoviD19, ko matsalar tsaro a cikin gida da sauran wanda zai hanasu aiki. Ko kuma yake bukatar kudade masu yawa don warwaresu. Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa kasar Iran a halin yanzu bata fuskantar wata matsala, don haka ya bukaci Gwamnonin lardun su yi amfani da wannan damar don amfani da matasan kasar wadanda suka yi karatu don bukasa...
    Jihar Gombe ta rattaba hannu kan kwangilar sama da biliyan 48 don aikin kula da Makarantar ‘yan mata ta Mega dake Doma da kuma zaizayar kasa   Baya ga sanya hannu kan kwangilar, an kuma bayar da cak don biyan diyya ga mazauna yankin mai nisan mita 10 da ke kan hanyar aikin.   Da yake jawabi a wurin rattaba hannu kan kwangilar a hukumance a Hayin Missau Bogo, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana matakin a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da muhallin Gombe da kuma kare makomar jama’a.   A cewarsa aikin ba wai kawai zai shawo kan zaizayar kasa ba ne zai dawo da fata ga al’ummomin da abin ya shafa.   Alh. Inuwa Yahaya wanda ya...
    A ranar 23 ga Mayu, 2025, jam’iyyar APC ta bayyana Tinubu a hukumance a matsayin dan takararta guda daya tilo don zaben 2027, duk da fuskantar sauyin ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban. Buhari ya jinjina wa kokarin Tinubu wajen rage talauci da hauhawar farashin kayayyaki, yana mai kira ga fannoni masu zaman kansu da daukacin ‘yan ƙasa da su ba da gudunmawarsu. Ya kammala da cewa: “Ina taya Shugaba Tinubu murnar cikar shekaru biyu a ofishi. Allah ya ci gaba da ba ka hikima da tausayi wajen jagoranci. Mu kuma mu rage tsammaninmu daga gwamnati.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
    A wani lamari mai ban al’ajabi, a daren jiya dalibai a jihar Taraba sun zana jarrabawar kammala karatunsu na Ingilishi na WAEC da karfe 8:25 na dare, sama da sa’o’i 12 da fara sa’o’i 8:00 na safe.   Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa jinkirin ya haifar da rudani da damuwa a tsakanin iyaye da masu kula da su, wadanda ke nuna shakku kan dalilan dage jarabawar da ba a taba ganin irinsa ba.   Lamarin dai ya yi matukar tayar da hankali idan aka yi la’akari da matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a yankin. Ba tare da wani bayani a hukumance daga WAEC ba, dalibai da iyaye suna mamakin abin da ya jawo tsaikon da kuma...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Harin da “Isra’ila” ta kai wa filin saukar jiragen saman Sanaa, manufarsa  ita ce yin matsin lamba akan matsayarmu ta taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta.” Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kara da cewa;  Komai girman hare-haren da Isra’ilan za ta kai ba zai yi tasiri akan matsayarmu ta taimakawa Gaza ba,sannan kuma ya kara da cewa; Abinda Isra’ila makiya ke son yi, shi ne a kyale ta yi yadda take so da Falasdinawa ba tare da an mayar mata da martani ba daga kowace kasa ta musulmi.” Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma ce; Matsayar da kasar Yemen take dauka na taimakawa Falasdinawa, matsaya ce ta addini.” Haka...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i, ya sanar a marecen jiya Laraba cewa, Iran za ta iya dakatar da tace sanadarin Uranium a karkashin yarjejniyar da za a iya kullawa da Amurka. Kakakin ma’ikatar harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Dr. Baka’i ya yi watsi da labarin da kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya watsa na yiyuwar dakatar da tace sanadarin “Uranium’ yana mai kara da cewa; zai ci gaba babu kakkautawa, kuma ba abinda za ma za a yi tayi ba.” Kamfanin dillancin labarun ” Mehr” na Iran ya ambato Baka’i yana cewa; labarin na Reuters, ba komai ba ne sai farfaganda ake maimaitawa, da kuma an sha kore gaskiyarta. Kamfanin dillancin labarun na “Reuters’ kamar yadda...
    Jaridar Vadiot Ahranot ta HKI  ta buga labarin dake cewa; Shugaban kasar Chile Gabriel Boric ya bayar da umarni a janye jami’an diplomasiyyarsa kasarsa masu kula da alakar soja daga ofishin jakadancin kasar tasa a Tel Aviv. Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Chile ta wallafa wani sako a shafinta na “Internet” cewa; Ofishin jakadancin nata ya sanar  da mahukunta wannan haramtacciyar cewa sun janye jami’an diplomasiyyar biyu. Kasar ta Chile ta bayyana dalilinta na yin haka da cewa, shi ne yanayin da mutane Gaza suke ciki ta fuskar jin kai ta tabarbarewar harkokin rayuwa saboda yakin da Isra’ila take yi. Haka nan kuma kin amincewar “Isra’ila” da a shigar da kayan agaji cikin yankin na zirin Gaza. Ita dai kasar...
    Babbbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke wa fitacciyar ’yar Tiktok, Murja Ibrahim wacce aka fi sani da Murja Kunya hukunicn daurin watanni shida a kurkuku. Alƙalin kotun Mai Shari’a Simon Amobida ya kuma ba wa Murja zabin biyan tarar Naira dubu 50. Ya ce saboda yawan mabiyanta a shafinta na Tiktok, an nada ta jakadiyar EFCC da Babban Bankin Najeriya (CBN) wajen wayar da kan mutane kan illar wulakanta Naira a dokar Najeriya. Sojoji sun halaka mayakan ISWAP da dama a Born Bashin da ake bin Najeriya zai koma tiriliyan 162 EFCC ce dai ta maka Murja a kotun, bisa zarginta da wulakanta Naira, bayan bullar wani bidiyo da ta ɗauka tana rawa tana yi wa kanta liƙi...
    Kunngiyar Tarayyar Turai, ta ce ba ta gamsu da sabon tsaron raba kayan agajin jin kai da Amurka da Isra’ila ke shirin aiwatarwa a Gaza. Babbar jami’ar diflomasiyyar kungiyar, Kaja Kallas, ta bayyana cewa Tarayyar Turai ba ta goyon bayan sabon tsarin raba agajin jin kai da Amurka da Isra’ila ke kokarin aiwatarwa wanda ke kaucewa hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji. Kallas, ta kuma bayyana cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa a Gaza sun wuce abun da suke bukata wajen yakar Hamas, a yayin da adadin wadanda suka rasa rayukansu ke ci gaba da karuwa. Tun bayan da Isra’ila ta dawo da yaki a watan Maris bayan ruguza  yarjejeniyar tsagaita wuta da ta cimma...
    Ministan harkokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa Iran ba za ta amince da duk wata tattaunawa kan dakatar da shirinta na inganta makamashin Uranium gaba daya ba. Ya bayyana hakan ne a gefen ziyarar da shugaban kasar ya kai kasar Oman, inda ya jaddada cewa, bai kamata tattaunawa da Amurka za ta hada da batun ba wanda Tehran ba za a amince da shi ba. Araghchi ya ce, ana ci gaba da tattaunawa da Amurka, amma batun tace uranium shi ne ya kasance babban abin da ake samun sabani. Ya kuma kara da cewa, an yi shawarwari da ministan harkokin wajen Oman game da shirya wani sabon zagaye na shawarwari tsakanin Iran da Amurka. Ministan ya...
    Gwamna Uba Sani ya amsa da cewa gwamnati ta kashe sama da Naira biliyan 100 cikin watanni shida don magance matsalar ƙarancin ruwa a faɗin jihar, tare da alƙawarin cewa za a maye gurbin dukkan kayan aikin da suka lalace. Ya ƙara da cewa an riga an kashe sama da Naira miliyan 400 wajen gyara da maye gurbin bututun ruwa da aka lalata, kuma kafin ƙarshen shekara Kaduna za ta fara samun ruwa ba tare da katsewa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majiyoyin labarai a kasar Yemen sun bayyana cewa HKI ta kai hare-hare a kan tashar Jiragen sama a birnin San’aa inda a wannan karon suka lalata hanyar tashin jiragen sama a tashar. Tashar talabijan ta Al-manar ta kasar Lebanon ta kanalto majiyar HKI tana tabbatar da wannan labarin. Tashar radio ta HKI ta nakalto ministan yakin HKI Yasra’il Katz yana tabbatar da wannan labarin ya kuma kara da cewa hare-haren ta sama sun wargaza wani bangare na tashar jiragen sama na birnin, sannan ya lalata jirgin sama tilo wanda ya rage a tasahr jiragen. Hakama tasha ta 12 ta HKI ta nakalto Katz yana cewa jiragen yaki fiye da 10 ne suka yi aikin hare-hare a kan tashar jirage na...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi ya tir da kalaman jakadan Burtaniya a Washington,  Peter Mandelson, wanda yayi kira ga Amurka kada ta taba barin Iran ta tashe makamashin Uranium a cikin kasar. Ministan ya kara da cewa Mandelson yana son ya karkatar da tattaunawan da Iran take da Amurka. Ya kuma kara da  cewa Iran ce take sanar da kasashen turai yadda tattaunawa tsakanin Amurka da ita ke tafiya, tun Amurka ta waresu daga tattaunawar. Yace, idan har haka ne tunanin kasar Burtaniya wacce take cikin kasashen da suka sanyawa yarjeniyar JCPOA hannu, yana ganin mai yuwa Iran ta dakatar da sanar da su abubuwan da ke tafiya a tattaunawar. Ya zuwa zagaye har 5 wadanda Amurka da...
    Idan har Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da bukatar Shugaban Kasa Bola Tinubu ta neman sake ciyo sabon bashi, jimillar bashin da ake bin Najeriya a yanzu zai koma Naira tiriliyan 162. A ranar Talata ce shugaban ya aike wa Majalisar Wakilai takardar neman ta sahale masa ya ciyo bashin, wacce shugaban majalisar, Abbas Tajuddeen ya karanta a zauren majalisar. Abbas ya ce rancen na 2025–2026, ya kunshi Dala biliyan 21.5 (kimanin Naira tiriliyan 34) da Yuro biliyan 2.2 (kimanin Naira tiriliyan 3.96) da Yen na Japan biliyan 15 (kimanin Naira biliyan 164.7) da kuma Yuro miliyan 65 (kimanin Naira biliyan 116.79) a matsayin tallafi. Tinubu zai ciyo bashin Naira tiriliyan 39 daga kasashen waje Kotu ta ci su...
    Gwamnatin kasar Ireland ta yi doka a jiya Talata wacce ta hana a shigar da duk wasu kaya da aka kera a matsugunan  ‘yan share wuri zauna da a karkashin dokokin kasa da kasa ake daukarsu a matsayin haramtattu. Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Ireland ya fada wa kamfanin dillancin labaurn Faransa cewa; Gwamnati ta amince da a ci gaba da yin wasu dokokin da hana mu’amalar kasuwanci da matsugunan ‘yan share wuri zauna da ba su bisa doka, domin an yi su ne akan kasar Falasdinawa.” Daga cikin kayayyakin da Majalisar dokokin ta Ireland ta haramta, da akwai ‘ya’yan marmari da itatuwa. Ministan harkokin wajen Ireland Simon Harris ya fada wa ‘yan jarida cewa, yana fatan ganin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Akaci ya bayyana cewa; Idan har kasar Birtaniya tana ci gaba a kiran Iran ta dakatar da tace sanadarin uranium a cikin kasarta, to kuwa Iran din za ta yanke tattaunawar da take yi da ita. Ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya rubuta a shaifnsa na hanyar sadarwa ta jama’a cewa: Iran ta tuntubi Birtaniya ne da kyakkyawar manufa,haka nan sauran kasashen turai da aka yi yarjejeniyar Nukiliya da su, duk da cewa, Amurka ba ta son su shiga cikin tattaunawar.” Arakci ya kuma ce; Idan har matsayar Birtaniya shi ne ta ga an daina tace sanadarin uranium baki daya a cikin Iran, wanda hakan  keta yarjejeniyar da ita kanta tana...
    Shuganan Kasa Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Wakilai takardar neman amincewarta domin ya ciyo bashin jimillar kudi Naira tiriliyan 39 daga kasasahen waje domin aiwatar da wasu ayyuka. A wasiku ukun da ya aike wa majalisar, wadanda shugabanta, Abbas Tajudeen, ya karanta a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya nemi goyon bayan majalisa domin ciyo bashin daga kasashen waje a shekarar 2025–2026. Ya ce rancen na 2025–2026, ya kunshi Dala biliyan 21.5 (kimanin Naira tiriliyan 34) da Yuro biliyan 2.2 (kimanin Naira tiriliyan 3.96) da Yen na Japan biliyan 15 (kimanin Naira biliyan 164.7) da kuma Yuro miliyan 65 (kimanin Naira biliyan 116.79) a matsayin tallafi. Yana kuma neman cin bashin cikin gida ta hanyar bayar da takardun lamuni na...
    Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira ga aiwatar da matakai da za su zamo misali na bude kofa, da raya hadin gwiwa, da dunkule mabanbantan wayewar kai tsakanin Sin da ASEAN da GCC. Li Qiang, ya bayyana hakan ne a Talatar nan, cikin jawabinsa ga bikin kaddamar da dandalin Sin da ASEAN da GCC, wanda aka bude a birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar Malaysia. Li, ya kuma yi kira ga sassan uku da su samar da wani salo na yin komai a bude tsakanin shiyyoyi, duba da cewa adadin al’ummunsu, da darajar tattalin arzikin da suke da shi ya kai rubu’in na duniya baki daya. Don haka dinkewar kasuwannin sassan 3, zai samar da babban fage na...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Dole ne a dauki kwararan matakai don dakatar da laifukan da ake yi a Gaza A yayin ganawarsa da fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif da tawagarsa a yammacin yau, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada wajabcin gudanar da ayyukan hadin gwiwa da inganci tsakanin kasashen Iran da Pakistan domin dakile laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa a Gaza. A farkon taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana matsayin Pakistan na musamman a duniyar Musulunci, inda ya bayyana jin dadinsa da kawo karshen yakin da ake yi tsakanin Pakistan da Indiya, tare da bayyana fatansa na warware sabanin da ke tsakanin kasashen biyu ta hanyar lumana. Haka...
    Kafin tashinsa zuwa kasar Oman shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna neman kyakkyawar dangantaka da maƙwabtansu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar kafin ya tashi daga filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Tehran zuwa birnin Muscat a yammacin yau Talata cewa: Makasudin ziyarar tasa zuwa kasar Oman ita ce kulla kyakkyawar alaka da kasashe makwabta, kuma alaka tsakaninsu tana bunkasa kowace rana. Shugaba Pezeshkian da yake zantawa da manema labarai a filin tashi da saukar jiragen sama na Mehrabad ya bayyana cewa: A halin yanzu yawan ciniki tsakanin Iran da Oman ya kai dalar Amurka biliyan 2.3, yana mai jaddada bukatar ci gaba da karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Shugaba Pezeshkian ya ce: Zai gudanar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran ba za ta daina sarrafa sinadarin Uranium a kowane hali ba Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya tabbatar a wata hira da tashar CNN ta Amurka cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da hakkinta na tace sinadarin Uranium a kowane hali ba. A yayin da yake mayar da martani game da kyakkyawan fata na shugaban Amurka Donald Trump game da shawarwarin nukiliyar da aka yi tsakanin gwamnatinsa da Iran da kuma yadda yake kallon ci gaban da aka cimma, Baqa’i ya ce: Idan manufar Amurka ita ce tabbatar da cewa shirin makamashin nukiliyar Iran ba zata yi amfani da shi wajen karfin soji ba, to yana ganin...
    Hukumomin Kasar Saudiyya sun sanar da ganin jinjirin watan Zulhajji a ranar Talata, wanda ke nuna cewa ranar Laraba 28 ga Mayu, 2025, ita ce 1 ga watan Zulhajji, 1446 Bayan Hijira. Hakan yana nufin Alhzai za su yi Tsayuwar Arfa ranar Alhamis, a yi Babbar Sallah ranar Juma’a na mako mai zuwaa yi
    Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe Naira miliyan dari da hamsin da ɗaya da dubu dari takwas da sittin da uku (N151,863,895.97) domin sake gina wani masallaci da wani matashi ya cinna wa wuta a yayin da jama’a ke tsaka da sallar Asuba a cikin jam’i a Tiga Gadan da ke Karamar Hukumar Gezawa, a watan Mayun bara. Aikin sabunta masallacin ya kunshi gina makarantar Islamiyya tare da ofis da bandaki da kuma rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana tare da tankin ruwa na sama. Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Wayya, ya sanar amincewar sake gina masallacin ya biyo bayan alkawarin da Gwamna Abba Kabir ya yi a lokacin da ya...
    Babbar Kotun Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda cinna wuta a wani masallaci a kauyen Gadan, Karamar Hukumar Gezawa, yayin da jama’a ke tsaka da jam’in sallar asuba a ranar 15 ga Mayu, 2024. Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 23 tare da raunana wasu. An samu Shafi’u da laifuka hudu, ciki har da kisan kai da kuma barna ta hanyar gobara. Baya ga hukuncin kisa, alkali ya ba da umarnin a yi masa bulala 150, tare da biya tarar N1,500, sannan kuma a kwace babur dinsa mai kafa uku, inda za a sayar, a yi amfani da kudin da aka samu wajen gyaran masallacin da ya lalace. Yayin shari’ar, masu...
    ’Yan sanda sun tsare wata matar aure kan zargin ta da kashe kishiyarta a Ƙaramar Hukumar Daura da ke Jihar Katsina. Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Katsina, DSP Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa matar ta yi wa uwargidarta kisan gilla ne bayan wata hatsaniya da aka samu a tsakaninsu, wanda ya ƙazance har ya kai ga kisa. Amaryar, mai shekara 23 a duniya, ta yi wa uwargida wannan aika-aika ne ranar Lahadi a unguwar Sabon Gari, daura da Makaranta Firamare ta Daɗi. DSP Abubakar Aliyu, ya ce a ranar ce bayan mijinsu ya dawo daga kasuwa ya kai ƙara Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Daura cewa ya iske uwar gidansa kwance a cikin jini. An yanke...