2025-11-07@22:23:56 GMT
إجمالي نتائج البحث: 119
«ya faɗa cikin»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta naɗa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa a tsakanin...
Dakarun Sojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram tara, ciki har da ƙwararren mai haɗa wa ƙungiyar bama-bamai, Amirul Bumma a wani samame da suka kai a dajin Sambisa da ke Jihar Borno. Majiyoyi sun bayyana cewa sojojin sun kai farmakin ne a Ƙaramar Hukumar Bama, ƙarƙashin rundunar Operation Desert Sanity 4, bayan samun bayanan sirri. Dakatarwa: Har yanzu ni Sanata ce — Natasha Doyin Okupe: Tsohon kakakin shugaban ƙasa ya rasu Boko Haram sun yi ƙoƙarin tsayawa da su fafata, amma sojojin sun yi nasarar fatattakar su. Bayan kammala artabun, mayaƙan sun dawo wajen da gadajen asibiti domin kwashe waɗanda suka jikkata, wanda hakan ke nuna girman asarar da suka yi. Daga cikin waɗanda aka kashe akwai babban jagoran...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Shamsedeen Babatunde Ogunjimi a matsayin sabon Akanta Janar na Tarayya. Naɗin nasa, wanda aka amince da shi a yau Talata, zai fara aiki ne daga ranar 7 ga Maris 2025, ranar da Oluwatoyin Madehin zai yi ritaya. Muhimmancin ƙamshi a rayuwar mace An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a Ana iya tuna cewa, tun a watan Disambar da ya gabata ne aka bayyana Ogunjimi mai shekaru 57 a matsayin magajin Madehin. Daga baya wani aka naɗa wani kwamitin ƙwararru da zai tantance wanda ya haɗa da manyan daraktocin daga a ma’aikatun gwamnatin tarayya daban-daban. Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce kwamitin ya yi...
Bidiyon batsa ya ja wa wasu ’yan Tiktok biyu hukuncin ɗaurin shekara guda kowannensu a gidan yari bayan an gurfanar da su gaban kotu a Jihar Kano. Kotun Majiatare da ke Norman’s Land a Ƙaramar Hukumar Fagge ta yanke wasu ’yan Tiktok din hukunci ne bayan samun su da laifin saɓa wa dokokin Musulunci da kuma tsarin zamantakewar al’ummar jihar. ’Yan TikTok ɗin da suka haɗa da Ahmad Isa da Maryam Musa waɗanda dukansu ’yan unguwar Ladanai ne da ke yankin Hotoro ne. Sun gurfana a kotu ne bayan da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta cika hannunta da su. Jami’an tsaro sun hana jama’a kwasar mai bayan hatsarin tanka a Taraba Yadda Kano ta koma matattarar ’yan TikTok...
Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus. Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja Bayan murabus ɗin nata, nan take ’yan majalisar suka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar Obasa, a wani yanayi da ba a saba gani ba a siyasar Nijeriya. ’Yan majalisar sun yabi salon mulkinta da kuma jajircewarta a matsayin mace ta farko kakakin majalisa. Rahotonni sun ce ta sauka daga muƙamin ne bayan wata ganawa da manyan ’yan jam’iyyar APC...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tsadar rayuwa da ake ciki ya sa dole a yi tattalin kuɗin da ake kashewa. An saba a watan Ramadana ana yawan yin girke-girke da kayan buɗa-baki iri-iri, amma kuma wannan azumin ya zo cikin yanayi na matsin tattalin arziki. NAJERIYA A YAU: Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar Jiki DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya a Yau ya duba hanyoyin da za ku yi girke-girken da yawa yadda aka saba cikin sauki ba tare da kashe maƙudan kuɗaɗe ba. Domin sauke shirin, latsa nan
Samar da dabino zai samu sauyi mai mahimmanci a Jihar Jigawa bayan da wani kamfani daga kasar Saudiyya mai samar da dabino da gwamnatin jihar suka ƙulla yarjejeniya domin ƙara yawan amfanin gona. Ta wannan haɗin gwiwa za a kawo sababbin fasahohin zamani da irin dabino masu yawa don shigar da su cikin tsarin noma. Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin Akpabio Ƙungiya ta rage farashin kayan marmari saboda Azumin Ramadan A cewar bayanai daga Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), Saudiyya ita ce ƙasa ta biyu mafi girma wajen samar da dabino na duniya, inda take samar da tan miliyan 1.61 na dabino. Masar ita ce ƙasa mafi girma wajen samar da dabino, inda...
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027. El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark. Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa. “A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai. “Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa...
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027. El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark. Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa. “A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai. “Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita. Domin sauke shirin, latsa nan
“A binciken da ake yi, an gano dukkan kayayyakin da aka sace bayan an sayar da su kan kudi naira 80,000, kuma wadanda ake zargin sun amsa laifin aikata laifin.” PPRO ya kara da cewa, ‘yansanda na ci gaba da neman mutum na uku da ake zargi mai suna Ibrahim Danmariya, wanda ake kyautata zaton shi ne mai karbar kayan da aka sace. Abdullahi ya bukaci mazauna yankin da su lura kuma su kai rahoto ga ofishin ‘yansanda mafi kusa. “Muna kira ga jama’a da su bayar da bayanai masu amfani da za su kai ga kama wanda ake zargi da gudu. “Muna tabbatar wa jama’a cewa za a yi amfani da duk bayanan cikin sirri,” in ji Abdullahi.
Ranar Kafar Rediyo ta Duniya: Minista Ya Buƙaci Gidajen Rediyo Da Su Faɗakar Da Jama’a Kan Sauyin Yanayi
A takardar, wadda mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim, ya sa wa hannu, Idris ya ce: “Rediyo ko yaushe hanya ce ta samun ingantaccen bayani kuma abin dogaro ne ga al’umma, musamman a lokutan da ake fuskantar matsaloli. “A ‘yan shekarun nan, rediyo ya taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a kan sauyin yanayi da tasirin sa ga duniyar mu. Tare da faɗin isar sa da sauƙin samun sa, rediyo yana da ikon ilimantarwa da ƙarfafa mutane su ɗauki matakan da suka dace don yaƙi da sauyin yanayi.” Idris ya ambato jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron COP29 na Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sauyin Yanayi wanda aka gudanar a birnin Baku na...
Kamfanin Siminti na BUA ya raba magungunan cututtuka daban-daban na kimanin naira miliyan 35 a ƙananan asibitoci da ɗakin shan magani 16 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Wamakko a Sakkwato. Daraktan Kamfanin BUA, Injiniya Yusuf Halliru Binji, a wurin rabon tallafin maganin ya ce BUA ya ba da tallafi ga asibitoci da ɗakunan shan magani 16 a tsarin da yake da shi na sadaukarwa ga al’ummar da suke kusa da shi, a kowace shekara akan bayar da magani don saukaka samun magani ga jama’ar. Binji ta hannun Alhaji Sada Suleiman da ya wakilce shi ya ce kamfanin BUA a tsarinsa na rama alheri ya ɗauki wannan da muhimmanci domin ƙarfafa dangantaka. “Babu tantama dole mu bayyana farin ciki ga irin...
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya miƙa wa Majalisar Dokokin jihar sunayen zaɓaɓɓun kwamishinoni 16 domin tabbatarwa. Shugaban Majalisar, Danladi Jatau ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar da ya gudana ranar Litinin a birnin Lafiya. Atiku da Obasanjo suna ganawar sirri Ɗalibi ya kashe abokin karatunsu da gatari a Nasarawa Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin sabbin kwamishinonin da gwamnan ya zaɓa har da tsohon Shugaban Masu Rinjayen a majalisar dokokin jihar, Umar Tanko-Tunga da wani tsohon mamba a majalisar, Mohammed Agah-Muluku. Kakakin Majalisar ya buƙaci kowane ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun kwamishinonin da su gabatar da kwafi 30 na duk bayanansu daga yanzu zuwa ranar Alhamis tare neman su hallara a gaban majalsiar a ranar Litinin ta makon...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Kano. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yammacin ranar Asabar. Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja Ya yi wa kansa keji don daina shan sigari Sanarwar ta ce naɗin sabon Sakataren Gwamnatin zai fara aiki ne a hukumance daga ranar Litinin mai zuwa 10, ga Fabarairun 2025. Sanarwar ta ce an naɗa sabon Sakataren Gwamnatin wanda ya shafe sama da shekaru talatin yana aikin gwamnati la’akari da ƙwarewar aiki da yake da ita a hukumomi da ma’aikatu daban-daban na wajen ganin an cimma muradin gwamnati mai ci na ciyar da Jihar...
Majalisar wakilai ta umarci kwamitocin sadarwa da harkokin cikin gida da su binciki haɗa lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) da layukan waya ba tare da izini ba da kamfanonin sadarwa ke yi. Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da ‘yan majalisa Patrick Umoh da Julius Ihonvbere suka gabatar, inda aka buƙaci hukumar NCC ta ɗauki mataki kan duk wani kamfanin sadarwa da aka samu da laifi, tare da NIMC ta tabbatar da sahihancin haɗa bayanan NIN. Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya Trump Ya Hana Maza Masu Sauyin Jinsi Shiga Wasannin Mata Umoh ya ce wannan mataki na iya haifar da damuwa ga ‘yan ƙasa, tare da jefa su cikin hatsarin satar bayanai, da damfara,...
Gwamnati Ta Sake Haɗa Tubabbun Mayaƙan Boko Haram 5,000 Da Iyalansu
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami’an hukumar tsaron farin kaya daga jamhuriyar Nijar ne suka biyo wanda ake zargin ɗan bindigar ne a kan babbar hanyar Zurmi/Kauran Namoda a jihar Zamfara. Da yake duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin sojojin da gwamnatin jihar Zamfara wajen yaƙi da ‘yan bindiga. “Dole ne in yaba wa sojoji, DSS, da ‘yan sanda, musamman ma Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, bisa nasarar aiwatar da wannan gagarumin kame. “Ina so in jaddada cewa waɗannan nasarori da aka samu tare da wasu na daƙile ‘yan bindiga a jihar, sun samo asali ne daga haɗin kai da goyon bayan da gwamnatin jihar Zamfara ke baiwa ɗaukacin...
Ya ƙara da cewa, “Da har yanzu ina cikin wannan gwamnati, zan fadi gaskiya a cikin tarurruka na sirri, kuma idan ba a ɗauki mataki ba, zan yi magana a fili. Duk wanda ke shakkar haka, ya duba tarihin aikin gwamnati na tun daga 1998.” El-Rufai ya kuma soki wasu da ya kira “’yan amshin shata” a gwamnatin Tinubu, yana mai cewa suna amfani da kuɗaɗen tsaro don kare duk wani abu da gwamnati ke yi, ko da kuwa ba abin karewa bane. Ya buƙaci Bwala da ya tuna cewa “Alkawari na farko shi ne ga Allah da ƙasa, kafin wani mutum ko hukuma.”