Jagora: Tafarkin Imaman Ahlul Bayti ( A.S) Na Gwgawarmaya Ne Da Jajurcewa
Published: 24th, April 2025 GMT
Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi dangane da zagayowar ranar shahadar Imam Ja’afar Assadiq ( a.s) ya bayyana cewa: Tafarkin Imaman Ahlul-Bayti (a.s) ya kasance na gwgawarmaya da jajurcewa, kuma koyarwarsu ta ginu ne akan mandiki da kafa dalili.
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya ce; rayuwar Imam Ja’afar Assadiq ( A.
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya siffata mutanen Gaza da Lebanon da cewa suna tafiya ne akan wannan tafarki na Imaman shiriya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA
Shugaban hukumar makamshin Nujkliya ta MDD ya zanda da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi kan al-amuran da suka shafi shirin nukliyar kasar Iran da kuma tattaunawar da ake gudana tsakanin ta da Amurka.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a tattaunawa ta wayar tarho tsakanin jami’an guda biyu a jiya Lahadi, Grossi shugaban IAEA ya bayyana cewa ya ji dadin yadda JMI ta zabi tattaunawa da AMurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya. Ya kuma bayyana cewa hukumarsa a shirye take ta gabatar da duk wani taimakon da JMI take bukata a yayin tattaunawar.
A nashi bangaren Abbas Araqchi ya bayyana cewa kasar Iran a shirye take ta bada hadin kai ga hukumar ta IAEA kamar yadda yarjeniyar NPT take bukata da kuma dokokin kasa da kasa.
Abbas ya fada masa inda aka kai ya zuwa yanzu a tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, a biranen Mascat na kasar Omman da kuma Roma na kasar Italiya.
Ya zuwa yanzu dai kasashen biyu sun gudanar da taro har sau uku dangane da shirin Nukliyar kasar ta Iran, kuma bangarorin biyu sun bayyana amincewarsu da yadda tattaunawar take tafiya.