Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 112
Published: 23rd, April 2025 GMT
112-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissiso da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan, ko kum littafin mathnawi na maulana Jalaluddeen rumi.
///… Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-hassan limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), kuma da na farko ga Fatimah diyar manzon All..(s), sannan jikansa na farko.
A cikin shirimmu da ya gabata mun kawo maku yadda Abuzar a Alghifari babban sahabin manzon All..(s) wanda ya kasance daga cikin mutane na farko da suka musulunta a Makka, sannan ya kuma garinsu giffar yana kiran mutane zuwa ga addinin musulunci har zuwa lokacinda manzon All..(s) yayi hijira, zuwa Madina sai shi ma yayi hijira. Banda haka, manzon All..(s) ya yabeshi a cikin hadisai da dama saboda tsoron All..ta zuhudu da kuma sanin addini.
Amma a lokacinda Uthman bin Affan ya zama khalifa ya kuma dora danginsa Banu Umayya a kan al-ummar musulmi suna azabtar da shi suna kuma kwasar kudaden jama’a suna kashewa kansu, ya fuskanci matsaloli da sahabban manzon All..(s) da dama daga ciki har da Abuzar Alghiffari, wanda ya ci gaba da sukar khalifa da kuma danginsa, har sai da ya kore shi daga madina zuwa Sham da farko, sannan ya sake dawo da shi Madina a cikin mummunan hali, amma Abuzar bai dandara ba, ya ci gaba da sukansu har sai da wata rana, Khalifa yayi tambaya a kan al-amuran addini sai wani bayahude wanda bai dade da musulunct ba, ya bada amsa kuma ba dai dai ba, sai Abuzar ya tashi a kasansa, sai Khalifa kuma ya tashi a kan Abuzar yana masa tsawa, daga karshe ya sake korarsa daga Madina karo na biyu, amma a wannan karon ya kore shi zuwa wani daji inda babu mutane, kuma yace zai zauna a wurin har sai ya mutunu.
Munji yadda ya umurci Marwan dan hakam, ya bashi guzuri ya koma can inda ba zai ga wani ba, kuma ba wanda zai ganshi. Sai Marwan ya ajiye shi a wani wuri kafin ya kammala hada masa guzuri, sannan khalifa ya fadawa Marwan ya fitar da shi cikin kaskanci daga Madina sannan kada ya bar kuma ya yi magana da shi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin watanni shidan farko na bana, an kafa sabbin kamfanoni 30,014 na masu zuba jari daga kasashen waje a babban yankin kasar Sin, wanda ya nuna karuwar hakan da kashi 11.7 cikin dari a mizanin duk shekara.
Kazalika, bayanai sun nuna cewa, saka hannun jari daga kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya ya karu da kaso 8.8 cikin dari a tsakanin lokacin.
Har ila yau, jarin da aka zuba daga kasar Switzerland ya karu da kaso 68.6, na Japan ya karu da kashi 59.1, na Birtaniya ya karu da kaso 37.6, sai kuma na Jamus da ya karu da kashi 6.3, kana wanda aka zuba daga Jamhuriyar Koriya kuma ya karu da kashi 2.7 bisa dari. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp