HausaTv:
2025-09-17@23:26:32 GMT

Hezbollah, ta yi tir da Isra’ila kan kisan gillar da aka wani babban jigonta

Published: 23rd, April 2025 GMT

Kungiyar Hezbollah, ta Lebanon ta yi tir da kakkausan lafazi da kisan da gillar da Isra’ila ta yi wani jigonta Sheikh Hussein Atoui, wanda ya yi shahada a ranar Talata, yayin wani hari da jiragen yakin Isra’ila a kusa da garin Damour na birnin Beirut.

Shugaban ofishin hulda da muslunci na kungiyar Hizbullah Sheikh Abdul Majid Ammar ya yi kakkausar suka dangane da kisan gillar dan gwagwarmayar, yana mai cewa abin takaici ne da makiya Isra’ila suka yi.

Sheikh Hussein Atoui shi ne shugaban Dakarun Al-Fajr, reshen Jamaa Islamiya (Kungiyar Musulunci) masu dauke da makamai, dake kawance da kungiyar Hamas.

Shugaban ofishin hulda da muslunci na kungiyar Hizbullah ya yi kira ga gwamnatin Lebanon da ta dauki matakai masu nagarta don kawo karshen ta’asar Isra’ila.

Babban jami’in kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya ce “Ya zama wajibi gwamnati ta wuce matsayin mai sa ido kawai, ta nisanci takaita kanta ga kalaman tofin Allah tsine ba tare da wani sakamako na hakika ba, sannan kuma ta dauki matakai masu tsanani, na gaggawa kuma masu tasiri a dukkan matakai da kuma hanyoyin da ake da su.”

A ‘yan watannin nan gwamnatin Isra’ila ta tsananta kashe-kashen da take yi a kasar Lebanon, inda ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a watan Nuwamban bara.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare

Fitattun dalibai akalla 12 ne  daga makarantun gwamnati suka samu guraben tallafin karatun sakandare  a ƙarƙashin Asusun Tallafin Karatu na Jihar Kwara (Kwara-ETF).

A wajen taron gabatarwa ga waɗanda suka fara cin moriyar shirin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa ci gaban harkar ilimi a Najeriya abu ne mai tsada kuma ya zama wajibi kowa ya bayar da gudummawarsa.

Ya roƙi masu masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen gina makarantu ko kuma su ɗauki nauyin daliban da suka nuna bajinta da jajircewa a harkar karatu.

A cewarsa, an zabo daliban 12 ne  sakamakon bajintar da suka nuna a matakai daban-daban na tantancewa da Kwara ETF ta gudanar.

Gwamnan ya bayyana cewa tallafin ya kunshi dukkan kuɗin da ake buƙata a karatun sakandaren daliban.

“Muna kira da jama’a su ba da gudummawa da kuma ɗaukar nauyin ɗalibai. Kada a bar wannan aiki ga gwamnati da iyaye kadai. Ilimantar da ‘ya’yanmu hakki ne da ya rataya a kanmu gaba ɗaya,” in ji Gwamna.

Ya yaba da tsarin zaɓen kuma ya taya waɗanda suka yi nasara murna.

A nata jawabin, Babbar Shugabar Kwara ETF, Oluwadamilola Amolegbe, ta ce daliban 12 sun fito ne daga cikin jerin ɗalibai 640 da aka fara tantancewa bisa cancanta.

Ta bayyana cewa tsarin zaɓen ya fara ne da rubuta jarabawa ga dukkan daliban firamare na aji shida da suka amfana da shirin KwaraLEARN na koyon fasahar zamani, har zuwa lokacin da aka kammala tantancewa.

 

Ali Muhammad Rabi’u 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  •  Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa  Kisan Kiyashi A Gaza
  • Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu
  • Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
  • Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan  
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
  • Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa