NAJERIYA A YAU: Mene ne Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Kundin Tsarin Mulkin Najeriya?
Published: 22nd, April 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Ko kun san tanadin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya yi game da Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa da ayyukansa da alhakin da ya rataya a wuyansa?
Kundin na tsarin mulkin ƙasa shi ne dai kundin dokoki mafi ƙarfi a Najeriya wanda ya ƙunshi tanade-tanade a kan dukkan al’amuran da suka shafi alhakin da ya rataya a wuyan shugabanni da ma al’ummar ƙasa.
Kuma kamar yadda ya tanadi yadda ake gudanar da dukkan al’amuran ƙasa, haka ya ayyana ƙarfin ikon da kowane shugaba yake da shi, da iyakarsa da ma yadda zai iya miƙa wannan ƙarfin iko ga wani don gudanar da ayyukansa.
NAJERIYA A YAU: Me ya sa matsalar tsaro “ta gagari gwamnati” a Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan RiƙoShin wanne aiki takamaimai kundin tsarin mulki ya bai wa Mataimakin Shugaban Ƙasa?
Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Da Benin Da Thailand Za Su Aiwatar Da Matakan Saukaka Tantance Kaya Na Kwastam
Babbar hukumar kwastam ta Sin ta fitar da sanarwar a yau Talata cewa, shirin amincewa da juna na tsarin “Masu gudanar da kamfanoni da aka ba su izni” wato AEO a takaice tsakanin Sin da Benin da Thailand zai fara aiki a hukumance daga ranar 1 ga watan Agustan shekarar 2025.
Bayan aiwatar da wannan tsarin amincewa da juna, za a ba da dama tsakanin kwastam na Sin da na Benin, da kuma kwastam na Sin da na Thailand, don su amince da juna a karkashin AEO.
Bugu da kari, yayin da ake tantance kayayyakin da ake shigowa da su daga waje a wurin kwastam, za a saukaka wa kamfanonin dake karkashin tsarin AEO wasu abubuwa, kamar rage yawan matakan dubawa, da ba su fifiko kan ayyukan kwastam, da kuma kebe musu jami’an hulda na kwastam da sauran matakai na samun sauki.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp