Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya: Jigon Ziyarar Xi A Kudu Maso Gabashin Asiya
Published: 22nd, April 2025 GMT
Kasar Cambodiya ce zangon ziyararsa ta karshe. Inda kasashen biyu suka amince da gina al’umma kyakkyawar makomar bai daya a sabon zamani, wanda kamar yadda bangarorin biyu suka jaddada, ya dace da muhimman muradun jama’ar kasashen biyu. La’akari da kalubalan da ake fuskanta a tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, kasar Sin ta taka rawa wajen samar da zaman lafiya a duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra
A wani taro wanda ya hada ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI da kuma mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara, bangarorin biyu sun tabbatar da cewa an kammala aikin shimfida layin dogo tsakanin garin Shalamcheh na kasar Iran da kuma birnin Basra a kasar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gwamnatocin kasashen biyu na fadar haka, sun kuma jaddada muhimmancin layin dogon da kuma samar da kasuwar babu kudaden fito a kan iyakokin kasashen biyu.
Labarin ya kara da cewa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu ya zuwa yanzu ya kai dalar Amurka biliyon $11a ko wace shekara kuma anan saran nan gaba zai iyakaruwa zuwa dalar Amurka biliyon $25.
Rahmatollah Akrami, ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI, da kuma Hazem Majid Naji Al-Khalidi mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara sun jaddada muhimmancin kammala layin dogo tsakanin kasashen biyu, da kuma kasuwar ba kudaden fito tsakanin kasashen biyu. Da kuma fatan zasu yi kokarin amfanar juna gwagwadon abinda zasu iya.