Jami’an yan sanda a birnin Makka sun tsare wata Bafalasdiniya wacce ta baje Jakarta dauke da tutar kasarta Falasdinu tare da zarginta na bayyana wani abu na siyasa a lokacin aikin umran da take yi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Mint-Press yana cewa matar ta shiga masallacin haramin Ka’aba dauke da jakanta mai tutar falasdinu.

Kuma bayan sun kamata sun tsare, Bafalasdiniyar wacce har yanzun ba’a bayyana sunanta ba, ta ce masu tana ganin wasu masu aikin umra wadanda suke shigowa masallacin Ka’aba tare da tutocin kasashen su, daga cikinsu akwai yan kasashen Morocco, Turkiyya, da sauransu, don haka itama tana dauke da tutar kasarta ce Falasdinu don nuna daga inda ta fito.

Ya zuwa yanzu dai ba wanda ya san halin da take ciki. Amma ba wannan ne karon farko wanda Jami’an tsaron kasar Saudiyya suke tsare wadanda suke dauke da tutar Falasdinu a aikin hajji ko umra ba, tare da zarginsu da cewa suna hada addini da siyasa.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun sasanta rikicin asibitin AKTH da KEDCO

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta shiga tsakani don sasanta rikicin da ya ɓarke tsakanin Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO).

Rikicin ya samo asali ne daga katse wutar lantarki da asibitin ya zargi KEDCO da yi, inda ya ce hakan ya kawo cikas ga ayyukan lafiya masu muhimmanci a asibitin, ciki har da zargin mutuwar marasa lafiya.

Sasantawar da Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya jagoranta ta biyo bayan zarge-zargen cewa katsewar wutar ta haddasa mutuwar wasu marasa lafiya da ke kan na’urar taimakon numfashi a asibitin.

Sai dai KEDCO ya musanta zargin a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, yana mai cewa asibitin na kokarin bata sunansa ne kawai.

A cewar mai magana da yawun ‘yan sanda na Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, an gudanar da taron sasancin ne a hedikwatar ‘yan sandan Kano da ke Bompai, inda aka zauna da Shugaban asibitin, Farfesa Abdulrahman Abba Sheshe, da Shugaban KEDCO, Abubakar Shuaibu Jimeta.

Taron ya mayar da hankali ne kan warware tankiyar da kuma dawo da wutar lantarki ga asibitin, wanda ke ya fuskanci matsaloli sakamakon katse wutar.

Sanarwar ta ce, “Bangarorin biyu sun nuna godiya ga matakin gaggawa da ‘yan sanda suka dauka. KEDCO ya amince da dawo da wutar lantarki nan take, alamar cewa rikicin ya zo karshe.”

Kiyawa ya kara da cewa, “Rundunar ‘Yan Sanda ta jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da ci gaba da aiki ba tare da tangarda ba a bangaren kiwon lafiya.”

Sanarwar ta kuma ce kwamishinan ‘yan sanda ya yaba wa AKTH da KEDCO bisa hadin kai, tare da alkawarin ci gaba da goyon baya don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  • Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha
  • Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
  • An Karrama Farfesa Adamu Gwarzo Kan Gudummawarsa Ga Bunƙasa Ilimin Jami’a A Nijeriya
  • ’Yan sanda sun sasanta rikicin asibitin AKTH da KEDCO
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin
  • Ɗangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai 250  a Jami’ar Ilorin
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa