Ma’aikatar kiwon lafiyar Falasdinawa ta sanar da cewa adadin shahidai a yankin na Gaza sun kai 50,669, yayin da wadanda su ka jikkata su ka kai 115,225.
Dangane da rahoton akan shahidan da ake samu a kowace rana kuwa,ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinawa ta ce, a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata an sami shahidai 60, wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 162.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, da akwai wani adadin na shahidai masu yawa da suke kwance a kasa, ba a iya daukarsu balle a yi musu jana’iza ba, saboda yawansu, da kuma wadu dubbai da suke a karkashin baraguzai na gidajen da makaman HKI su ka rusa da mutane a cikinsu.
A wani labarin daga Gaza, jiragen yakin HKI sun kai hari akan wata rumfa ta raba abinci ga Falasdinawa da suke fama a yunwa, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutane 3 a sansanin Khan-Yunus dake kudancin zirin Gaza.
Haka nan kuma sojojin na HKI sun kai hari akan gidajen mutane a cikin gain na Khan-Yunus da ya yi sanadiyyar shahadar muutm guda.
Wasu yankunan da ‘yan sahayoniyar su ka kai wa hare-hare sun hada Qaizan Abu Rashwan dake kudu masu yammacin Khan-Yunus, da Hayyuz-Zaitun da kudu maso gabashin Gaza, sai kuma titin Sakkah a wannan birni.
A gefe daya mutanen Gaza suna ci gaba da yin hijirar da aka tilasta su daga Hayyul-Shuja’iyyah, zuwa yammacin Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe Falasdinawa kusan 30 a wani sabon kisan kiyashin Isra’ila a Gaza
Bayanai daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 35 dane suka hada da kananan yara aka kashe a wanisabon kisan kiyashi na Isra’ila a zirin Gaza.
A cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, wadannan hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane 35 tare da jikkata 109 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Adadin wadanda sukayi shahada sakamakon yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a yankin da aka yi wa kawanya ya zarce 52,400.
Adadin wadanda suka jikkata kuma ya kai kusan 118,014 tun daga watan Oktoban 2023.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi gargadin barkewar ayyukan jin kai a Gaza.
Hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar da wani kakkausan gargadi game da matsalar jin kai da ke kara tabarbarewa a Gaza a dai dai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren bama-bamai da kuma killace fararen hula da ke fama da yunwa.
Tun cikin watan Maris ne Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya haramta kai kayan agaji zuwa Gaza, a wani mataki da ya ce na da nufin tursasa Hamas ta amince da tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra’ila.