Leadership News Hausa:
2025-08-02@04:26:03 GMT

Yadda Ake Fitar Da Zakkar Fidda Kai Da Sallar Idi

Published: 28th, March 2025 GMT

Yadda Ake Fitar Da Zakkar Fidda Kai Da Sallar Idi

Yadda Ake Ba Da Ita

Ana ba da ita kafin a fita zuwa Sallar Idi ko kafin Ranar Sallah da kwana daya ko biyu. Abin da ake bayarwa shi ne Muddan Nabiyy (mudun awo ne dan madaidaici wanda za a iya auna shi da cikin tafukan hannun mutum mai matsakaicin tsawo) guda hudu a kan kowane mutum. Ana fitarwa daga dukkan nau’in abinci, kamar mu a nan mu ce shinkafa, masara, doya, dawa, dauro, cukwi, nono da duk dai abin da galibin mutane suke amfani da shi a matsayin abinci.

Malaman kasar Maroko wadda kasa ce ta Malaman Musulunci kuma ‘yan’uwanmu ne Malikawa; sun yi fatawa cewa ya halasta a ba da kudi a madadin abinci a Zakkar. Za a kimanta kudin adadin Muddan Nabiyy hudu da za a fitar sai a ba da. Wannan ya halasta.

Idan mutum ya yi nazarin hikimar ba da Zakkar, wato wadata talakawa da miskinai don kar a gan su suna bara saboda rashin abincin da za su ci a Ranar Sallah, wannan kudin da za a ba su sai ya fi musu dadi a kan tsabar abincin. Domin wani idan ka bashi hatsin watakila ba zai iya nikowa ba, toh ka ga shi a wurinsa kudin zai fi masa amfani fiye da dawa ko masara. dan dama-dama shinkafa ko doya wanda duk za a iya dafawa ba sai an nika ba. Amma fa a lura, kowane irin abinci mutum ya bayar ya yi. Saboda amfanin kudin ne ya sa muka kawo wadannan bayanan.

An fi so a ba da Zakkar ga mutanen kirki daga cikin talakawa ko wadanda suke da almajirai a hannunsu wadanda idan an ba su ba za su je bara ba a ranar. Ita Shari’a ba ta so a ga kaskancin mutum a wannan ranar, so ake kowa ya nuna girman Musulunci, kodayake wasu ‘yan’uwa ba za su yarda ba, duk abin da aka ba su ba za su iya hakura ba sai sun fita bara. Toh amma kuma kar wannan ya sa a ce ba za a ba su ba.

Idan mutum ya fitar da Zakkar sai ya kasance babu miskinai a kusa da shi da zai ba su, to ya dauka ya kai wurin da suke ya ba su, kar ya ce ai tunda babu miskinai a kusa da shi shikenan ba sai ya ba da ba.

Fa’ida: hatta kafirin da ake zaune da shi in talaka ne za a iya ba shi Zakkar don ya wadata a wannan ranar. So ake dan Adam ya zama ya wadata saboda albarkar ranar ta Sallah.

Sallar Idi

Sallar Idin Shan Ruwa (karamar Sallah) da Sallar Idin Layya (Babbar Sallah kamar yadda galibin Hausawa ke cewa), an shar’anta su a Musulunci a shekarar farko da yin Hijirar Annabi (SAW) daga Makka zuwa Madina. Kuma Annabi (SAW) ya dauwama a kansu (yana aikatawa). Ya hori maza da mata da yara da manya su fita zuwa gare su, ma’ana su je Masallacin Idi.

Ana so a yi wanka, a sa turare, a sanya mafi kyan tufafi da mutum yake da shi. A Sallar Idin Shan Ruwa, ana so a ci abinci kafin a fita zuwa Masallaci koda dabino ne ko shayi. Ana so a dan jinkirta ta kadan; savanin Sallar Idin Layya da aka fi so a jinkirta cin abinci har sai an dawo. Idan mutum ya samu ikon yin Layya; ana so ya bude baki da naman Layyar sannan an fi so a gaggauta yin ta domin a dawo gida a yi Layya.

Ba a yin Sallar Idi (duka biyun) a Rufaffen Masallaci sai dai in akwai lalura kamar ta ruwan sama. A wajen gari ake fita yin SallarIdodin biyu ko kuma duk filin da aka samu. Annabi (SAW) bai tava yin Sallar Idi a Rufaffen Masallaci ba sai sau daya saboda ruwan sama kamar yadda Hakim ya ruwaito Hadisin.

Ana so a canja hanyar da aka je Masallacin Idi wajen dawowa amma ba dole ba ne. Ana so a yi Sallar Idin Shan Ruwa kamar da misalin karfe bakwai da rabi na safe (7:30am), Sallar Layya kuma kamar da misalin karfe bakwai na safe (7:00am). Amma ko sun kai karfe goma sha daya na rana babu laifi, duk lokacin yin su ne.

Ba a yin Kiran Sallah ko Ikamah ko cewa “a tashi a yi sallah”. Da zarar Sarki ko wanda ya tsaya a matsayinsa ya iso filin masallaci sai a mike a shiga Sallah. A raka’ar farko; bayan Kabbarar Harama sai a kara Kabbara shida, sun zama bakwai kenan. A raka’a ta biyu; bayan Kabbarar Tasowa daga Sujuda sai a kara Kabbara biyar, sun zama shida kenan. Ba a yin Nafila kafin Sallar Idi (duka biyu) kuma ba a yi a bayanta. Liman zai yi huduba bayan an yi sallama, wanda yake so zai zauna ya ji wanda wani uzuri ya kama shi sai ya tashi ya tafi ba tare da ya yi magana (surutai) ba.

Ana so a yi wasanni, da kade-kade, da wake-wake, da ciye-ciye, da nishadi, da ziyarori, da yi wa juna murnar Idi. Ana so a yi kallon wasannin ko rawar da ake yi, duk ya halatta a wannan ranar. Wannan shi ne Musulunci sassauka kamar yadda Annabi (SAW) ya fada, Tirmizhi da Ibn Majah da Baihaki suka fitar.

Allah ya sa mu kammala Azumi lafiya, mu yi Sallah lafiya, ya hore wa dukkan Musulmi abin da za a yi hidimomin Sallah da shi, Allah ya karva mana ibadunmu kuma ya karve mu da falalarsa albarkar Annabi (SAW).

 

‎Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil aziym.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Dausayin Musulunci Sallar Idin

এছাড়াও পড়ুন:

Taɓarɓarewar Tarbiyyar Matasa A Arewa: Ƙalubalen Da Ke Gaban Iyaye Da Shugabanni

Sai dai girma, kima da ɗaukakar da matasa ke da ita ga al’umma ta ja baya ƙasa sosai a bisa ga yadda rayuwarsu ke iyo da ninƙaya a kogin  zubar da mutunci ta hanyar aiwatar da abubuwan da ke da alamar ayar tambaya.

Matasa da dama a yau ba su ganin kowa da gashi, ba su girmama kowa, ba su ganin mutuncin kowa, ba su daraja kowa ballantana har a tsawata masu ko a ba su shawara da ɗora su kan hanyar yadda za su daidaita rayuwar su daga gurɓatacciyar hanya zuwa madaidaiciyar hanya.

Abin takaici ne da matuƙar damuwa yadda matasa suka gurɓata rayuwarsu mamakon amfani da lokaci da damar da suke da ita amma sai suka zaɓi biyewa ruɗin abokai da son zuciya wajen aikata abubuwan da ba su kamata ba.

Al’ummar Arewacin ƙasar nan da aka shaida da tarbiya, kamun- kai, mutunci da sanin ya kamata, a yau an wayi gari sun ɗauki gurɓatattun halayen da suka mayar da su marasa tarbiya. 

Rashin kulawar iyaye, malamai, shugabanni da dukkanin masu da tsaki ga sanya idanu ga yadda ƴaƴansu ke gudanar da rayuwar su babbar matsala ce mai zaman kan ta da ta taimaka wajen gurɓacewar rayuwar matasa.

Iyaye da dama na sakaci wajen kulawar musamman ga tarbiyar ƴaƴansu ta hanyar rashin saka idanu sosai ga yadda ƴaƴan ke gudanar da rayuwar su, abokan da suke hulɗa, wuraren da suke zuwa, binciken wayoyin su, suturar da suke saka wa da sauransu.

Idan da iyaye suna bayar da cikakkiyar kulawa ga kula da tarbiyar ƴaƴansu ta hanyar bin diddigin su a kai- a- kai da zai yi wahala a riƙa kuka a yau a yadda tarbiyar matasa ta sukurkurce.

Matasan Arewa a yau sun zama abin nunawa a bisa ga yadda tarbiyar su ta yi faɗuwar baƙar tasa, lamariin da al’ummar yankin ke kuka da kokawa musamman bisa ga rashin sanin makomar rayuwar matasa a shekaru masu zuwa.

A halin yanzu tarbiyar matasa maza da mata na fuskantar mummunar barazana da ke buƙatar iyaye, shugabanni, malamai da dukkanin masu ruwa da tsaki su tashi tsaye domin yi wa tufkar hanci tun kafin a makara wajen shawo kan bahaguwar matsalar.

Canjin zamani, kwaikwayon ɗabi’un rayuwar Turawa da kwaɗayi sun taka kuma suna ci-gaba da taka muhimmiyar rawa wajen gurɓacewar tarbiyar matasa a wannan zamanin.

Karuwanci, hulɗa da abokan banza, sharholiya da baɗala, shaye- shayen kayen maye, amfani da kafafen sada zumunta na zamani, kallon fina- finan banza, wayoyin hannu, ƙungiyoyin asiri, neman jinsi tsakanin mata da maza a baƙaƙen ɗabi’un namiji da namiji da mace da mace da sauran ayyukan fitsara lamba ɗaya abubuwa ne da ke tsunduma matasa a kogin da- na- sani 

Haka ma jahilci, talauci, kwaɗayi da neman abin duniya ido rufe da sauransu matsaloli ne da idan matasa ba su tashi tsaye haiƙan suka yaƙe su ba, to za su kai su su baro a lokacin da za su fahimci sun makaro sun makaro.

Bugu da ƙari kafafen sada zumunta na soshiyal midiya na kan gaba-gaba wajen bayar da gagarumar gudunmuwa wajen gurɓata tarbiyar matasa ta yadda matasa maza da mata ke aiwatar da abubuwan da tamkar ba su da mafaɗi.

Shigar banza ta hanyar tallata tsiraici, furta kalaman da ko kare ba zai ci ba, karuwancin yanar gizo, kalwanci tsakanin mata da maza abubuwa ne da matasa a yau ke cin karen su ba babbaka a dandalin soshiyal midiya.

Shafukan soshiyal midiya a yau a cike kuma a gurɓace suke da shafukan karuwai, ƴan daudu, ƴan luwaɗi da ƴan maɗigo waɗanda a fili suke tallata hajar su ga abokan harka wanda hakan babbar illa ce kuma babban ƙalubale ga tarbiyar matasa.

Haka ma yadda al’ummar Arewa ke gudanar da bukukuwan aure a wannan zamanin ya nuna a fili irin girman lalacewar da tarbiya ta yi a yankin a bisa ga yadda mata ke baje- kolin tsiraicin su a shigar banza wadda amarya ke jagoran ta.

Baƙuwar al’adar ranar ƙauyawa da aka fito da ita wadda a wajen bukukuwa a Arewa rana ce ta musamman da ƴan mata ke shigar fitsara da raye- rayen baɗala tamkar a ƙasar arna lamari ne da tuni gwamnatoci a Arewa suka fara ɗaukar mataki.

Gwamnatin Kano ta kasance ta farko wajen haramta ranar ƙauyawa a bukukuwan da al’ummar jihar ke yi a bisa ga illa, baɗala da matsalolin da ranar ke haifarwa musamman zubar da mutunci da darajar kyawawan al’adun ƙasar Hausa.

Bugu da ƙari sabuwar ɗabi’ar ‘saka hannu’ da matasa ƴan manyan makarantu ke yi a bisa ga murnar kammala karatu babbar matsala ce ga tarbiyar matasa. Matasan maza da mata kan yi rubutun saka hannu da maka a riguna da hijaban ƴan mata a ranar da suka kammala karatu tare da taɓa ƙirji da sauran sassan jikin matan.

Sabon salon na saka hannu a yanzu ya ɓulla har a makarantun sakandire wanda hakan babbar matsala ce da wasu gwamnatocin suka hango suka kuma haramta ɗabi’ar bakiɗaya a makarantu.

A bisa ga wannan matsalar da illarta, kwanan nan a wannan watan na Yuli gwamnatocin jihohin Sakkwato da Yobe suka bayar da sanarwar haramta murnar ‘saka hannu’ a dukkanin makarantun sakandire a jihohin biyu, matakin da ya samu yabo daga al’ummar ciki da wajen jihohin tare da kira ga sauran jihohi da su yi koyi.

Jama’a da dama na ganin gurɓatacciyar rayuwar da matasa suka ɗauka a matsayin wayewa a wannan zamanin muddin ba a samu nasarar shawo kan ta ba, to illar da za ta haifar ga manyan gobe da ke tasowa ba ƙarama ba ce.

Binciken LEAɗERSHIP HAUSA ya nuna ƴan siyasa na da kaso mai yawa na gurɓacewar rayuwar matasa a dalilin saka su aikata mabambantan ayyukan assha da suka zama silar rasa martabar su.

ƴan siyasa da dama a yau suna amfani da matasa wajen saka su a harkokin bangar siyasa, ba su kuɗin maye ko kayan maye, figar gashin kazar wannan da fashin ƙwan kazar wancan, tayar da hayaniya a wajen taron waccan jam’iyyar, ƙone ofishin ɗaya jam’iyyar da ma illata abokan adawa.

Abin damuwa ne yadda jam’iyyun siyasa a ƙasar nan ke ƙarfafa  harkokin bangar siyasa a dukkanin tarukan yekuwar neman zaɓen su a inda a kan ga matasa cike da motoci da babura a cikin shigar banza ɗauke da kowane iirin nau’i na miyagun makamai

A cewar Mainasara Giɗaɗo “yan siyasar da ke amfani da matasa wajen bangar siyasa gabanin zaɓe, galibi bayan samun nasara su kan watsar da matasan a kondon shara ba tare da assasa shiraruwan tallafawa rayuwarsu ba wanda ya kamata matasan su yi wa kan su karatun ta- natsu ta hanyar ƙauracewa waɗanda ba su damu da inganta rayuwar su ba.”

Ya ce “Matasa da dama a yau waɗanda ya kamata su himmatu wajen neman ilimi da aiki da shi tare da gudanar da sana’o’i nagari, sun banzantar da lokacin su ga shiga sabgogin da suke zubar da kima da mutuncin su ga al’umma.”

A yau matasan ƴan mata sun dabaibaye rayuwarsu da rashin tarbiya, sharholiya da baɗala da mayar da fitsara tamkar wani ado na musamman lamarin da ya zama babban ƙalubale gare su wajen samun mazaje nagari.

Masu fashin baƙin lamurran yau da kullum kan bayyana cewar kasuwar kamilallun ƴan mata nagari waɗanda suka nesanta kan su da ayyukan baɗala da abota da ƙawayen banza ta fi tashi a sauƙin neman aure akasin ƴan matan da suka yi wa kan su baƙin fentin fitsara da ke kasa samun mazaje cikin sauƙi.

A gidan aure rahotanni sun nuna yadda ƴan mata da dama ke kasa sauke nauyin gida da ya rataya a wuyansu domin galibin matasan wannan zamanin a bayyane suke bayyanawa mazaje su ba za su iya yi masu girki ba ballantana gudanar da wasu aikace- aikacen gida da suka wajaba wanda duka rashin tarbiya ne ya haddasa hakan.

A ra’ayin wani matashi, Ayuba Bello Okimo ya bayyana cewar rayuwar matasa ta na cikin babban ƙalubale a kan yadda suka tsunduma a harkokin zubar da mutunci.

Ya ce “Tabbas rayuwar matasa ta na cikin babban ƙalubale domin matasa sun tsunduma a harkokin banza da shaye- shaye gadan gadan wanda yayi tasiri wajen gurɓacewar tarbiyar matasa.”

“Wannan matsalar a yanzu har ta kai matasa na ganin matashin da ba ya yi bai waye ba, kazalika matasa a wannan lokacin suna son kuɗi ta kowane hali da son yin rayuwa mai kyau amma sai dai ba sa son neman na kai da aikin wahala, don haka lallai- lallai akwai ƙalubale sosai.”

Ya ce “ɗukkan al’ummar da Allah ya arzirta su da matasa a na cewa sun yi dace domin duk abin da ya tunkaro su za su nuna ƙarfi da zarra irin ta matasa domin cinma nasara. Tabbas Arewacin Nijeriya Allah ya albarkace mu da matasa, amma sai dai kash waɗannan matasan maimakon su kasance matasa wadanda za a yi alfahari da su sai suka kasance waɗanda ake kuka da su, sabo da an riga da an gurɓata tunani da hankalinsu, ta hanyar ayyukan banza da shaye- shaye.”

“Wasu daga cikin azzaluman shugabanni waɗanda ba sa kishin matasan ballantana son ci-gabansu, su ke saya musu kayan shaye shaye suna sha domin kawar da hankalinsu domin aiwatar da ayyukan da suka ɗora su a kai a lokacin da  su kuma ƴayansu suna makarantun ƙwarai a ciki da wajen ƙasa suna karatu.”

Ya ce wajibi ne matasa su yi wa kan su faɗa su yi karatun ta- natsu domin ceto goben su ta yadda za a yi alfahari da su ko bayan rai ya yi halinsa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Limamin Sallar Juma’a Ya Ce; Iran Zata Mayar Da Isra’ila Kufai Idan Ta Sake Kai Hari Kan Kasarta
  • An ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kebbi
  • Nijeriya Na Asarar Kusan Naira Tiriliyan 17.9 Duk Shekara Sakamakon Cutar Hanta — Gwamnati
  • Taɓarɓarewar Tarbiyyar Matasa A Arewa: Ƙalubalen Da Ke Gaban Iyaye Da Shugabanni
  • Zargin Da Wasu ’Yan Siyasar Amurka Ke Yi Wa Sin Na Fitar Da Hajoji Fiye Da Kima Ya Sabawa Hujjoji Na Hakika
  • Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa
  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
  • Wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu saboda ɗan Kudu ne — Onanuga
  • Wasan Kwallon Mutum-Mutumi Ya Nuna Yadda Sin Ta Shirya Wa Karbar Bakuncin Wasanninsu Na Duniya
  • Yadda ’yan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina