Fursunoni 12 sun tsere bayan fasa gidan yari a Kogi
Published: 24th, March 2025 GMT
Aƙalla fursunoni 12 ne suka tsere baya sun fasa wani gidan yari da ke garin Kotonkarfe a Jihar Kogi.
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Za mu farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu — Zulum Wasu manyan ’yan Nijeriya sun yi wa Gwamna Radda ta’aziyya a SaudiyyaMista Fanwo ya ƙara da cewa tuni sun sake kama fursuna ɗaya daga cikin waɗanda suke tsere ɗin.
Gwamnatin Kogi ta ce za ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da jami’an tsaro domin gano yadda fursunonin suka samu nasarar tserewa a safiyar ranar Litinin.
Kwamishinan ya bayyana lamarin da abin takaici, “sannan yadda fursunonin suka iya tserewa ba tare da barin wata alama ba abin tambaya ne.
“Dole a gudanar da bincike mai zurfi, sannan a kamo fursunonin da suka tsere, sannan a gano waɗanda suke da hannu,” in ji Fanwo.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gidan Yari Jihar Kogi
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA