Kwana Daya Bayan Kwace Fadar Shugaban Kasa, Sojojin Sudan Sun Kwace Babban Bankin Kasar
Published: 22nd, March 2025 GMT
A ci gaba da shimfida ikonsu da suke yi a cikin birnin Khartum, sojojin Sudan sun kwace iko da babban bankin kasar, kwana daya bayan da su ka kori dakarun kai daukin gaggawa daga fadar shugaban kasa.
Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya nakalto majiyar sojojin Sudan tana cewa; A yau Asabar sun yi nasarar kwace iko da babban bankin kasar, tare kuma da shimfida ikonsu a cikin wasu yankunan na birnin Khartum.
Kakakin sojan kasar Sudan Nabil Abdullah, ya bayyana cewa; Mun rusa sojoji da kayan aikin abokan gaba. Haka nan kuma Abdullah ya sanar da kwace wasu ma’aikatu da suke a tsakiyar birnin Beirut da su ka kasace a karkashin ikon dakarun kai daukin gaggawa.
Ana zargin rundunar kai daukin gaggawa da tafka laifukan yaki a cikin yankunan da a baya su ka shimfida ikonsu a ciki, har da babban birnin kasar Khartum.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Holland Ta Hana MInistocin HKI Biyu Shiga Cikin Kasarta
A jiya Litinin ne dai gwamnatin kasar Holland ta sanar da hana wa minstocin tsaron kasa Itmir Bin Gafir, da na kudi, Bitsirael Smotrich shiga cikinta.
Kasar ta Holland ta zargi wadannan mutanen biyu da cewa suna ingiza sojojin HKI da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi da kuma fadada yawan matsugunan ‘yan sahayoniya a yankunan da aka ce nan ne za a kafa Daular Falasdinawa.
Haka nan kuma gwamnatin kasar ta Holland ta kira yi jakadan HKI a birnin Hauge domin gargadinsa akan yanayin da ake ciki a Gaza, da cewa babu yadda za a iya ci gaba da jurewa akansa, ko kare dalilin jefa yankin cikin wannan halin.”
Wannan matakin na kasar Holland ya zo ne gabanin wani taro da tarayyar turai za ta yi a yau Talata domin jingine aikin tare da HKI a fagen nazari da bincike na ilimi, saboda ta ki tsagaita wutar yaki a Gaza.
Tun da fari, Fira ministan kasar Holland Dick Schoof ya wallafa a sharin X cewa; A yayin taron da kasashen turai za su yi, Kasarsa za ta yi matsin lamba akan ganin an dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da HKI, haka nan kuma kakaba takunkumai akan shigar da kayanta na kasuwanci zuwa kasuwannin turai.
Fira ministan na kasar Holland ya ce, ya fada wa shugaban HKI Ishaq Herzog wannan matakin da suke son dauka ta hanyar tarayya turai.