Falasdinawa 90,000 Ne Su Ka Yi Sallar Juma’a A Masallacin Kudus
Published: 7th, March 2025 GMT
A yau Juma’ar farko ta watan Ramadan an kiyasta cewa adadin Falasdinawan da su ka halarci sallar juma’a a masallacin Kudus, sun kai 90,000,duk da cewa sojojin HKI sun hana wasu falasdinawan masu yawa isa masallacin.
“Yan sandan Sahayoniya sun rufe dukkanin hanyoyin da suke isa cikin masallacin, domin bincika takardun masu wucewa, saboda su hana samari da matasa majiya karfi shiga cikin masallacin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
INEC Ta Gudanar da Taron Masu Ruwa da Tsaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi na Babura/Garki
A wani ɓangare na shirin gudanar da zaɓen cike gurbi na Babura/Garki a Majalisar Tarayya, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) reshen Babura ta shirya muhimmin taron masu ruwa da tsaki domin tabbatar da sahihin zaɓe mai inganci da haɗin kai.
A jawabinsa yayin taron, jami’in zaɓe na ƙaramar hukumar Babura, Malam Hafiz Khalid, ya gabatar da cikakken jadawalin ayyukan zaɓen.
Ya jaddada muhimmancin haɗin kai da gaskiya a kowane mataki, yana mai bayyana zaɓen a matsayin aikin gama gari da ke buƙatar goyon bayan duk masu ruwa da tsaki.
Mahalarta taron sun bayar da shawarwari masu amfani tare da gabatar da muhimman tambayoyi da suka shafi inganta sahihanci da nasarar zaɓen.
Wasu daga cikin batutuwan da aka tattauna sun haɗa da shirye-shiryen kayayyakin aiki, tsaro, wayar da kan masu zaɓe, da sauransu.
An kammala taron da sabunta ƙudurorin haɗin guiwa daga dukkan mahalarta, wajen tabbatar da gudanar da zaɓen cike gurbi cikin lumana, ‘yanci, adalci, da sahihanci a yankin Babura/Garki.
Wakilin Rediyon Najeriya ya bayyana cewa, taron da aka gudanar a ofishin INEC na Babura, ya samu halartar masu ruwa da tsaki da suka haɗa da Hakimin Babura, jami’an tsaro, wakilan jam’iyyun siyasa, jami’ai daga Ƙungiyar Direbobin Ƙasa (NURTW), Ƙungiyar Masu Motocin Haya (NARTO), ƙungiyoyin farar hula (CBOs), da sauran jami’an INEC.
Usman Muhammad Zaria