Karamar Hukumar Malam Madori Ta Gargadi Malaman Da Ba Sa Zuwa Aiki
Published: 3rd, March 2025 GMT
Karamar hukumar Malam Madori da ke jihar Jigawa, ta yi barazanar daukar matakin hukunta malaman makaranta da ba sa zuwa aiki.
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas ya bayyana haka a wata hira da manema labarai bayan raba kudi dubu hamsin a matsayin tallafin karatu ga dalibai ashirin da biyar a yankin.
A cewarsa, wani bincike da aka gudanar bayan hawansa karagar mulki, ya nuna cewa malaman makarantu da dama ba kasafai suke zuwa aiki ba.
Ya ce hakan na daga cikin dalilan tabarbarewar ilimi a yankin, wanda ke bukatar kulawar gaggawa.
Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas ya yi nuni da cewa, “Ilimi muhimmin abu ne a kowane fanni na rayuwar dan Adam, don haka ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wani malamin da ba ya zuwa makaranta”.
Ya yi nuni da cewa, akwai mutane da dama wadanda suka kammala karatu kuna ba su sami aiki ba, saboda haka za a iya daukarsu fomin maye gurbin wadanda ba sa son zuwa aiki.
Shugaban ya kuma shawarci matasan yankin da su sadaukar da kansu wajen samun ilimi mai inganci, domin cigaban rayuwarsu da kasa baki daya.
Ya kara da cewa, karamar hukumar karkashin jagorancinsa za ta ci gaba da bayar da tallafi ga ilimi, domin samar da ’ya’ya masu ilimi a nan gaba.
.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Wata Sabuwa: Malaman Jami’ar Tarayya A Kano Sun ƙi Amince Wa Da Zaɓen Sabon VC
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp