Aminiya:
2025-09-17@23:27:54 GMT

Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Kano

Published: 28th, February 2025 GMT

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da Muƙaddashin Shugaban Ma’aikata kuma Babban Sakataren Tsare-Tsare, Salisu Mustapha, kan badaƙalar zaftare albashin ma’aikata ba bisa ƙa’ida ba.

An umarci Mustapha da ya sauka daga muƙaminsa na Babban Sakataren Tsare-Tsare a Ofishin Shugaban Ma’aikata domin ba da damar gudanar da bincike.

A gaban mijina Akpabio ya nemi kwanciya da ni —Sanata Natasha Buhari ya koma Kaduna da zama bayan shafe shekara 2 a Daura

Gwamna Abba ya amince da naɗa Malam Umar Muhammad Jalo, Muƙaddashin Babban Sakataren REPA, a matsayin Muƙaddashin Shugaban Ma’aikatan jihar har zuwa lokacin da za a kammala binciken lamarin.

Matakin gwamna ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da dama da ma’aikatan gwamnati suka yi kan rage albashi ba bisa ƙa’ida da kuma jinkirin biyan albashi a kan lokaci.

A martaninsa, ya jaddada matsayin gwamnatinsa na rashin amincewa da duk wani rashin gaskiya da suka shafi harkokin kuɗi.

Ya kuma yi alƙawarin cewa duk wanda aka samu da hannu a lamarin za a hukunta shi.

“Wannan gwamnati ba za ta lamunci duk wani zalunci a kan ma’aikata ba. Duk wanda aka kama yana wawure albashin ma’aikata za a hukunta shi ba tare da la’akari da muƙaminsa ba,” in ji Gwamna Abba.

Domin shawo kan matsalar, gwamnan ya kafa kwamitin mutum bakwai wanda Kwamishinan Raya Karkara, Abdulkadir Abdussalam, zak jagoranta.

Gwamnan ya bai wa kwamitin umarni da ya duba albashin ma’aikata daga watan Oktoban 2024 zuwa Fabrairun 2025 domin gano waɗanda abin ya shafa, tantance asarar kudade, da bayar da shawarwari kan matakin da ya dace a ɗauka.

An umarci kwamitin da kammala bincikensa cikin kwanaki bakwai tare da gabatar da cikakken rahoto.

An naɗa Salisu Mustapha a matsayin Muƙaddashin Shugaban Ma’aikatan jihar a farkon wannan wata bayan Shugaban Ma’aikata jihar, Abdullahi Musa, ya tafi hutun jinya zuwa ƙasar Indiya domin neman magani.

Gwamna Abba ya tabbatar wa ma’aikatan Jihar Kano cewa gwamnatinsa na da niyyar kasancewa adala, mai gaskiya, da kuma biyan albashi a kan lokaci.

Ya gargaɗi duk wani jami’in gwamnati da ke da hannu a badaƙalar kuɗi cewa zai fuskanci fushin doka.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas 
  • An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
  • NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
  • Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu
  • Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
  • Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara