Sanata Katung ya damu kan yadda wasu ke ta’azzara ta’addanci a kudancin Kaduna
Published: 22nd, February 2025 GMT
Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna yankin ke taimaka wa miyagu wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci.
Da yake magana a taron manema labarai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kudancin Kaduna (SKJF) a Zonkwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Sanata Katung, ya jaddada cewa hukumomin tsaro na kara ɗaukar matakan daƙile matsalar a Kauru, Kachia da sauran yankunan da abin ya shafa.
Ya gargaɗi duk masu bai wa ’yan ta’adda mafaka ko goyon baya da su daina, domin hukuma za ta ɗauki matakin ladabtar da su.
Sanatan ya kuma bayyana aniyarsa ta horar da matasa a fannin fasahar zamani da ICT domin su samu ƙwarewa da damar gogayya a matakin ƙasa da ƙasa.
Har ila yau, ya yaba da ƙoƙarin shugabanni da masu ruwa da tsaki wajen samar da Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Kachia, wacce yanzu ke da reshe a garin Manchok.
Dangane da batun canza Asibitin Tunawa da Sir Patrick Ibrahim Yakowa da ke Kafanchan zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya, Katung, ya bayyana cewa ƙudirinsa yana jiran sauraron ra’ayoyi a Majalisar Dattawa.
Ya ƙara da cewa ƙudiri makamancinsa a Majalisar Wakilai ya riga ya kai matakin karatu na uku, kuma bayan amincewar Majalisar Dattawa, za a haɗa su don gabatar wa Shugaban Ƙasa domin ya rattaba hannu.
Bugu da ƙari, Sanatan ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta bai wa malaman kimiyya fifiko wajen ɗaukar sabbin malamai a makarantun sakandare domin inganta harkar ilimi.
A nasa ɓangaren, Shugaban SKJF, Ango Bally, ya ce taron manema labaran wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙungiyar na wayar da kan jama’a kan ayyukan Sanata Katung a Majalisar Dattawa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gargadi Sanata Marshal Majalisar Dattawa a Majalisar
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Sakkwato Ta Sayo Manyan Tan-tan 250 Na Sama Da Naira Biliyan 22
An shawarci gwamnatocin jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara da su kirkiro hanyoyi na wayar da kan al’umma dangane da shirye-shiryen tallafi da ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa domin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da tsaro a yankunansu.
Shugaban sashen kimiyyar zamantakewa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Chika Umar Aliyu, ne ya bayar da wannan shawara yayin gabatar da takarda a wajen taron shekara-shekara na kungiyar Nigerian Institute of Management reshen jihar Sokoto na shekarar 2025, wanda aka hada da gabatar da lambar yabo ga wadanda suka cancanta.
Farfesa Chika ya bayyana cewa, gwamnati tarayya na da shirye-shiryen tallafi da dama da suka hada da na noma, kasuwanci da kuma koyar da sana’o’in hannu domin kara habaka tattalin arzikin ‘yan Najeriya da rage zaman kashe wando, da tayar da hankali musamman matasa a yankin.
Ya jaddada cewa dole ne gwamnatocin jihohi su tallafa wa kokarin gwamnatin tarayya ta hanyar amfani da hukumominsu na jin dadin al’umma domin cimma burin shirye-shiryen.
A jawabinsa wajen taron, kwamishinan noma na jihar Sakkwato, Muhammad Tukur Alkali, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta sayo manyan Tan-tan na noma guda 250 da kayan aikin gona da darajarsu ta kai naira biliyan ashirin da biyu da miliyan dari daya (₦22.1bn), domin tabbatar da wadatar abinci.
A cewar Tukur Alkali, gwamnatin jihar ta hanyar shirye-shiryen inganta rayuwar al’umma, ta samar da sama da ayyukan yi 2,700 a bangaren noma, abin da ke da tasiri mai girma wajen bunkasa noma mai dorewa da ci gaban ababen more rayuwa a karkara.
Daga Nasir Malali