Leadership News Hausa:
2025-05-01@04:27:24 GMT

Shugaban Pakistan: Ci Gaban Kasar Sin Al’amari Ne Mai Kyau

Published: 17th, February 2025 GMT

Shugaban Pakistan: Ci Gaban Kasar Sin Al’amari Ne Mai Kyau

Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin ta yi hira da shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari, dake ziyarar aiki a kasar Sin, a baya bayan nan a birnin Beijing. Yayin hirar, Zardari ya bayyana cewa, ci gaban kasar Sin al’amari ne mai kyau, kuma Sin ba ta taba zama mai mamaya ba.

Bisa ci gaban Sin cikin sauri, wasu kasashe suna daukarta a matsayin wata “barazana”.

Game da hakan, Zardari ya ce, a matsayin makwabciyar kasar Sin, kasar Pakistan ta san a ko da yaushe Sin ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, kila ne a ji tsoron sauran kasashen duniya, amma ba kasar Sin ba. (Safiyah Ma)

 

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya

Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya ta naɗa Sheikh Bashir Aliyu Umar a matsayin shugabanta bayan rasuwar Sheikh AbdulRasheed Hadiyyatullah.

Wata sanarwa da majalisar ta fitar a yau Laraba ta ce an amince da shuagabancin Dokta Bashir ne kai-tsaye saboda kasancewarsa mataimakin shugaba.

A ranar Litinin ne Sheikh Hadiyyatullah ya rasu yana da shekara 81 a Jihar Osun.

“Nan gaba za a sanar da mataimakin shugaban,” in ji sanarwar da Nafiu Baba Ahmed ya sanya wa hannu a matsayin sakataren majalisar.

Sheikh Bashir sanannen malami ne kuma shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Al-Furqan da ke Alu Avenue a Unguwar Nasarawa ta Jihar Kano.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Najeriya Wajen Yin Watsi Da Kariyar Cinikayya Da Yin Adawa Da Danniya Da Cin Zarafi
  • Kar A Mika Wuya Ga “Damisar Takarda”
  • Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya
  • Saudiya Ta Yi Allawadai Da Kissan Kiyashin Da HKI Take Yi A Gaza A Gaban Kutun ICJ
  • Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China
  • Har Yanzun Ana Zaman Dar-Dar A Burkina Faso Bayan Kokarin Juyin Mulkin Da Bai SamiNasara Ba
  • Shugaban Kungiyar Hizbullah Ya Abbaci Abubuwa 3 Wadanda Yakamata Kasar Ta Maida Hankali A Kansu
  • Shin Amurka Na Iya Komawa Kan Kadaminta A Matsayin Cibiyar Masana’antun Duniya?
  • Tawagar Jami’ai Da ‘Yan Kasuwar Ta Tunusiya Ta Gana Da Mataimakin Shugaban kasar Iran
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA