HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Haruna Zago a Kano
Published: 13th, February 2025 GMT
An yi jana’izar fitaccen ɗan siyasar nan kuma Shugaban Hukumar Kwashe Shara na Jihar Kano (REMASAB), Alhaji Ahmadu Haruna Zago, a Ƙofar Kudu da ke Fadar Sarkin Kano.
Haruna Zago, ya rasu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, bayan fama da rashin lafiya.
Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Miƙa makaman ’yan bindigar Katsina ya bar baya da ƙuraDubban mutane ne suka halarci jana’izar fitaccen ɗan siyasar, daga ciki har da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, Sarkin Kano na 16, Mai Martaba Sanusi Lamido Sanusi.
Sauran jami’an gwamnatin Kano da manyan ’yan kasuwa na daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar marigayin.
Ga hotunan yadda jana’izar ta wakana:
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Haruna Zago Kwankwaso Rashin lafiya rasuwa Siyasa
এছাড়াও পড়ুন:
Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi
Har ila yau, majalisar ta amince da Naira biliyan 3.3 don ayyukan samar da ruwa da makamashi domin inganta samar da ruwa mai tsafta da aminci a cikin al’ummomin birane da karkara.
Daga cikin ayyukan samar da ruwan, an amince da gina tashar tace ruwa ta zamani a Taliwaiwai da ke ƙaramar hukumar Rano, da kuma biyan bashin kuɗin wutar lantarki da man fetur da ake bin hukumar ruwa ta jihar don ci gaba da ayyuka.
Wani ɓangare na kuɗaɗen zai kuma haɗa da biyan basussukan da kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) ke bi, siyan dizal (AGO) da man fetur (PMS) don ayyukan tashoshin tace ruwa, da kuma kula da kayayyakin da tashoshin ke bukata don samar da ruwa tsaftatacce.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA