Jam’iyyar NNPP Daya INEC Ta Amince Da Ita – Shugaban Jam’iyyar
Published: 7th, February 2025 GMT
Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dakta Ajuji Ahmed, ya tabbatar da shugabancinsa, inda ya yi watsi da ikirarin wani bangare na jam’iyyar, inda ya bayyana cewa shi ne wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta amince da shi. Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja ranar Juma’a, Ahmed ya tabbatar da cewa, jam’iyyar na nan a karkashin shugabancinsa da kuma kwamitin ayyuka na kasa (NWC) da aka kaddamar a shekarar 2022.
এছাড়াও পড়ুন:
Har Yanzun Ana Zaman Dar-Dar A Burkina Faso Bayan Kokarin Juyin Mulkin Da Bai SamiNasara Ba
Ana ci ga ba da zaman dar-dar a kasar Burkina faso, bayan da shugaban kasa mai ci Ibrahim traure ya sake tsallaka rijiya da baya, a wani kokarin juyin mulki wanda bai sami nasara ba a makon da ya gabata.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ya nakalto radiyo Faransa RFI yana fadar cewa an bankado juyin mulkin ne bayan da dukkan bakin da aka gayyata a ranar 22 ga watan Afrilu zuwa wani taro sun kasa halattan taron. Wanda ya nuna shakku kan abinda aka kulla a cikin taron.
Labarin ya kara da cewa a cikin yan kwanaki masu zuwa mutanen kasar zasu fito zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga shugaban Traore.
Har’ila yau ana gudanar da bincike a cikin barikokin sojojin kasar a birnin Wagadugu a kokarin gano wadanda suke adawa da gwamnatin Traore, sannan suke aiki wa kasashen yamma musamman kasar Faransa wajen ganin bayan shugaba Ibrahim Traore.
Kafin haka dai an nakalto ministan tsaron kasar ta Burkina faso Muhammada Sana ya na wani bayani a tashar talabijin na kasar, kan cewa kafin su gano shirin juyin mulki sun satar maganar wayar tarho tsakanin wani babban sojan kasar da shugaban wata kungiyar ta’addaci wanda aka shirya za su kashe shugaba Traore.