Tinubu zai tafi Faransa daga nan ya zarce Habasha
Published: 5th, February 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu a wannan Larabar zai bar Nijeriya zuwa ƙasar Faransa domin kai wata ziyara ta ƙashin kai.
Daga nan kuma Shugaba Tinubu zai wuce ƙasar Habasha inda zai halarci taron gamayyar ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU.
NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zaboMai bai wa Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga a shafinsa na X, ya ce Tinubu zai tafi Paris ɗin ne gabanin tafiyar da zai yi zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha domin taron ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU).
A lokacin taron da za a yi a birnin na Addis Ababa a farkon mako mai zuwa, Shugaba Tinubu zai gana da shugabannin ƙasashen Afirka domin taron ƙungiyar da za a gudanar daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Fabrairun 2025.
A yayin ziyararsa a Faransa, Tinubu zai gana da takwaran aikinsa na Faransa Emmanuel Macron.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Faransa
এছাড়াও পড়ুন:
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Ban da haka, shugaban na Sin ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen aiwatar da ra’ayin raya kasa na kirkiro sabbin fasahohi, da tabbatar da daidaito, da kare muhalli, da bude kofa, gami da haifar da alfanu ga kowa, ta yadda za a kafa wata al’ummar bai daya ta yankin Asiya da na tekun Pasifik.
Duk a wajen taron, yayin wani bikin mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, shugaba Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 33, wanda ake sa ran gudanar da shi a birnin Shenzhen na kasar Sin a watan Nuwamba na shekarar 2026. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA