Shamkhani : Iran Za Ta Kare Shirinta Na Nukiliya Na Zaman lafiya Da Dukkan Karfinta
Published: 4th, February 2025 GMT
Babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa Iran za ta yi amfani da dukkan karfinta wajen kare shirinta na nukiliya cikin lumana.
A yayin wata ziyara da ya kai wani baje kolin da ke nuna sabbin nasarorin da aka samu a masana’antar nukiliya a hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI) a ranar Litinin din nan, Ali Shamkhani ya sake nanata gaskiyar shirin nukiliyar Iran da kuma yadda kasar ke bin ka’idojin kasa da kasa.
“Iran ba ta taba neman makaman nukiliya ba kuma ba za ta taba yin hakan ba,” in ji shi. “Duk da haka, tana kare hakkinta da dukkan karfinta.”
Shamkhani ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kuduri aniyar kare muradun al’ummar Iran daga wuce gona da iri na manyan kasashen duniya, wadanda suka yi watsi da alkawuran da suka dauka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Dubban Mutanen Burkina Faso Sun Yi Gangamin Nuna Goyon Bayan Shugaban Kasa Ibrahim Traore
Kwanaki kadan bayan wani furuci daga babban jami’in sojan Amurka a Afirka akan shugaban kasar ta Burkina, dubban mutanen kasar sun yi gangami na nuna goyon bayan Kaftin Ibrahim Traore
Gangamin na mutanen kasar Burkina Faso, ya biyo bayan maganganun da su ka fito daga kwamandan sojojin Amurka a Afirka Janar Michael Langley wanda ya zargi sojojin dake Mulki da amfani da ma’adanan kasar saboda kashin kansu maimakon yi wa mutane aiki.
Mahalarta gangamin sun daga kwalaye dake dauke da rubutun yin tir da furucin jami’in sojan na Amurka da kuma nuna goyon baya ga shugaban kasar.
Daga cikin mahalarta gangamin da akwai fitaccen mawakin kasar, Ocibi Joan,wanda ya siffata jami’in sojan Amurkan da dabbar daji mai cin mutane yana mai yin kira a gare shi da kasarsa da su daina yin karya.
Haka nan kuma ya kara da cewa: ” Mutanen Burkina ba su fada da kowa,amma a lokaci daya, ba za su bar masu wawason dukiyar kasarsu ba.”
Wani mutum da ya halarci gangamin Haruna Sawadogo ya fada wa manema labaru cewa, idan suna son ganin bayan Kaftin Traore ne, to su fara ta kan mutanen kasar.
Hakan nan kuma jaddada cewa ba za su bari abinda ya faru da Thoms Sankara ya faru dakanar Troare ba.