HOTUNA: Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 4, shanu 15 da awaki 20 a Neja
Published: 4th, February 2025 GMT
Mutum huɗu sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu 13 suka jikkata a sanadiyyar wani mummunan hatsari da ya auku a hanyar Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja.
Aminiya ta ruwaito cewa hatsarin ya rutsa da tireloli uku waɗanda suka yi karo da juna ’yar tazarar mitoci ƙalilan zuwa garin Agaie.
Mai gari ya tsere bayan mazauna sun cinna wa gidansa wuta a Kano NCDC ta tsaurara matakan shige da fice a Nijeriya saboda fargabar EbolaWani mazaunin yankin, Baba Yakubu ya bayyana cewa ɗaya daga cikin tirelolin da lamarin ya shafa ta ɗauko lodin dabbobi da suka haɗa da shanu da awaki
Shi ma Darekta Janar na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullah Baba Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa an miƙa waɗanda hatsarin ya rutsa da su zuwa Babban Asibitin Agaie domin samun kulawa.
Ya alaƙanta faruwar lamarin da saɓa wa ka’idar tuƙi a yayin da ɗaya daga cikin tirelolin ta yi ƙoƙarin ƙetare wadda ke gabanta ba bisa ka’ida ba.
Ya ce hatsarin ya yi ajalin mutum huɗu — biyu da suka mutu nan take, sai kuma wasu biyun da suka ce ga garinku nan bayan an miƙa su asibiti.
Kazalika, ya ce shanu kimanin 15 da fiye da awaki 20 sun mutu a dalikin hatsarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: awaki Hatsari Jihar Neja
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi ritaya a matakin jiha da kananan hukumomi.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.
A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.
Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.
Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.