Shugaban Majalisar Kasar Iraki Ya Kawo Ziyarar Aiki Iran
Published: 3rd, February 2025 GMT
Da marecen jiya Lahadi ne dai shugaban Majalisar dokokin Iran Mahmud Mashahadani ya iso Tehran domin fara ziyarar aiki da zai gana da jami’an gwamnatin kasar.
Mataimakin shugaban Majalisar Shawarar musulunci ta Iran Hamid Ridha Haji Babbayi da kuma shugaban kwamitin kawancen majalisun kasashen biyu ne su ka tarbi Mashhadani a filin saukar jiragen sama na “Mehrbad”
.উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Uganda Ta Sanar Da Kawo Karshen Ebola Da Ta Barke A Kasar
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Uganda ta sanar da cewa, an kawo karshen Ebola da ta bulla a kasar bayan da aka dauki kwanaki 42 ba tare da an sami mutum daya wanda ya sake kamuwa da ita ba.
A wani bayani da ya fito daga hukumar kiwon lafiya ta duniya ( WHO), ta bayyana cewa, a lokacin bullar cutar an gabatar da mutane 14 masu dauke da ita, an tabbatar da 12 daga cikinsu, sai wasu biyu da ba a same ta a tare da su ba.”
Haka nan kuma hukumar lafiyar ta ce, an sami mutuwar mutane 4 daga cikin wadanda su ka kamu da cutar ta Ebola, wasu mutane 10 kuma sun warke.”
Watanni 9 da su ka gabata ne dai aka tabbatar da bullar cutar a birnin Kamfala bayan da wani mutum da yake dauke da ita ya rasu.
Dajukan da kasar ta Uganda take da su, suna a matsayin matattarar cutar ta Ebola ce, wacce a karon farko ta bulla a cikin kasar a 2000.
A yankin yammacin Afirka cutar Ebola ta kashe fiye da mutane 11,000 a tsakanin 2013 zuwa 2016.