Za a Kashe Sama da Naira Biliyan 9 Wajen Gyran Asibitoci a Jigawa
Published: 28th, January 2025 GMT
A cim ma burin Gwamna Umar Namadi na ci gaban bil’adama a cikin ajandar mai dauke da abubuwa 12, majalisar zartaswar jihar Jigawa ta kafa wani kwamiti mai mambobi 10 domin samar da hanyoyin da za a bi wajen nemo masu hazaka domin karfafa kirkire-kirkire a tsakanin matasa masu tasowa a jihar.
Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana haka bayan taron majalisar da aka gudanar a Dutse.
Ya ce, kwamitin ya kunshi kwamishinonin lafiya, muhalli, kananan hukumomi yayin da kwamishinan ilimi mai zurfi zai zama shugaba.
Sauran mambobin sun hada da masu ba da shawara kan fasaha, ICT da tattalin arziki na dijital, ilimi mai zurfi, aikin gona, babban darakta na hukumar karfafa matasa da samar da aikin yi da kuma babban sakatare mai zaman kansa na gwamna.
Sagir Musa Ahmed ya ce, mai ba da shawara na musamman kan fasaha da kirkire-kirkire ne zai zama sakataren kwamitin.
Hakazalika majalisar ta ware wa kwamitin makonni 2 domin gabatar da rahotonsa.
Ya kara da cewa, matakin majalisar na da burin bunkasa al’adun kirkire-kirkire, kirkire-kirkire da kasuwanci a tsakanin ‘yan jihar musamman matasa kamar yadda ma’aikatar ilimi mai zurfi ta gabatar.
Ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da kaddamar da wani shiri na musamman na wayar da kan jama’a a matsayin “Gwamnati da Jama’a” a karkashin jagorancin Gwamna Malam Umar Namadi.
A cewarsa, za a kaddamar da shirin ne a dukkanin kananan hukumomin 27 da za a sanar da taron majalisar al’umma a kowace karamar hukumar domin tattaunawa kai tsaye da Gwamna da sauran jami’an gwamnati.
Ya yi nuni da cewa, gaba daya babban burin shi ne tabbatar da cewa al’ummar jihar ba wai kawai masu cin gajiyar ayyuka da shirye-shiryen gwamnati ba ne, har ma sun kasance masu taka rawar gani wajen tsara makomarsu da kuma sanin ayyukan da gwamnatin jihar ke ci gaba da gudanarwa da kuma shirye-shiryenta.
Kwamishinan ya ce majalisar zartaswar jihar ta amince da sake farfado da cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko guda 114 a fadin jihar.
Ya ce majalisar ta amince da sama da Naira Biliyan 9.7 don farfado da PHC a fadin kananan hukumomi 27 da ke jihar a karkashin gwamnatin.
KARSHE/USMAN MZ/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
’Yan bindiga sun sace Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Honarabul Samaila Bagudu, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bagudu.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun mamaye garin Bagudu ne da yammacin ranar Juma’a tare da yin harbe-harbe don tsorata al’umma.
Maharan sun yi awon gaba da ɗan majalisar ne a kan hanyarsa ta dawowa daga masallaci bayan ya an idar da sallah masallaci a garin na Bagudu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya ce an sanar da hukumomin tsaro, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da kuɓutar da Mataimakin Shugaban Majalisar.