HausaTv:
2025-07-12@16:08:26 GMT

 Kungiyar “ISWAP” Ta Kashe Sojojin Najeriya 20

Published: 27th, January 2025 GMT

A kalla sojojin Najeriya 20 ne su ka kwanta dama daga cikinsu har da kwamanda a wani hari da ake dangantawa kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP.

‘Yan ta’addar sun kai harin ne dai a  ranar Juma’ar da ta gabata a kan sansanin bataliya ta 146 dake Malam-Fatori a akan iyakar Najeriya da Nijar a jihar Borno.

Wani soja da ya tsira daga wannan harin ya fadi cewa harin ‘yan ta’addar ya dauki sa’oi 3, kuma sun je wurin ne a cikin manyan motoci tare da shammatar sojojin.

Kamfanin dillancin labarun Reuters wanda ya ambato sojan ya ce, maharan sun rika harbinsu ta kowace kusurwa, sai dai sun mayar da wuta.Haka nan kuma ya tabbatar da cewa an kashe kwamandnsu.

Mazaunan yankin da aka kai harin sun tabbatar da cewa maharan sun kone gine-gine masu yawa, da ya tilastawa mazauna yankin yin hijira.

Haka nan kuma an tabbatar da cewa har zuwa Asabar da dare an rika ganin maharan a cikin wannan yankin suka karakaina.

 Ita dai kungiyar “ISWAP” ta balle ne daga Bokoharam a 2016, kuma tana kai wa sojoji da jami’an tsaron Najeriya hare-hare.  A tsawon shekaru 15 na hare-haren ‘yan ta’adda a wannan yankin mutane kusan 40,000 ne su ka kwanta dama,wasu miliyan biyu kuwa su ka tarwatse.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Neja

Aƙalla mutum 13 ne suka rasu, ciki har da ɗan sanda da ’yan sa-kai guda uku, a wani hari da ’yan bindiga suka kai garin Mongoro da ke Ƙaramar Hukumar Mariga, a Jihar Neja.

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Laraba.

Ana zargin takalar faɗa tsakanin fadar Aminu Ado da Sanusi II ’Yan ƙabilar Ibo ne suka fi aikata laifi a Jihar Anambra ba Fulani ba — Gwamna Soludo

Mazauna garin Wamba, sun ce har yanzu suna cikin fargaba saboda ‘yan bindigar ba su bar yankin ba.

A ranar 24 ga watan Yuni, maharan sun kai hari wani sansanin sojoji da ke Kwanan-Dutse, inda suka kashe sojoji 17, tare da jikkata wasu 10.

A cewar wasu mazauna garuruwan, harin na baya-bayan nan ya faru ne a ranar Talata, inda ’yan bindigar suka zo da yawa kuma ɗauke da muggan makamai inda suka yi wa jami’an tsaro da ’yan sa-kai taron dangi.

Sun raunata mutane da dama.

Wani mazaunin yankin wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce jami’an tsaron sun yi ƙoƙari, amma alburusansu sun ƙare a yayin artabun, wanda hakan ya sa dole suka ja da baya.

Ya ce ana buƙatar gaggauta tallafa wa ’yan sa-kai a Mongoro saboda yankin na fama da hare-hare.

Wani mazaunin kuma ya ce an kashe mutum 13, ciki har da ’yan sa-kai, sannan ’yan bindigar sun lalata turakun sadarwa, wanda hakan ya haddasa matsalar sadarwa a yankin.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Mariga, Abbas Adamu Kasuwan-Garba, ya tabbatar da harin, amma ya ce ba a tabbatar da adadin waɗanda suka rasu ba tukuna.

Ya ƙara da cewa lamarin tsaro a yankin na ƙara taɓarɓarewa saboda yawan hare-haren da ake kai wa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar harin, amma ya ce har yanzu babu cikakken bayani.

Saboda tsoron kai hare-haren, manoma da dama a Mariga da Rijau sun daina zuwa gonaki, wasu kuma sun koma birane domin tsira da rayukansu.

Wani mazaunin yankin Rijau, mai suna Ibrahim Ayuba, ya ce mutane da yawa sun tsere daga ƙauyuka zuwa Rijau saboda tsoron kashe-kashe da sace-sacen da ke ƙaruwa a kullum.

A wani yunƙuri na shawo kan matsalar tsaro, Etsu Nupe kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar, ya buƙaci haɗin gwiwa da sabbin dabaru domin magance matsalar.

Ya bayyana haka ne yayin da Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Adamu Abdullahi Elleman, ya kai masa ziyara a fadarsa.

Kwamishinan, ya ce manufar ziyarar ita ce ƙarfafa haɗin kai tsakanin sarakuna, al’umma da jami’an tsaro wajen yaƙi da ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro.

Masani ya buƙaci kafa rundunar tsaron daji

Wani masani kan harkar tsaro, Auwal Bala Durumin Iya, ya buƙaci gwamnati ta bai wa ’yan sa-kai da jami’an tsaro makaman da suka fi ‘yan bindiga nagarta.

Ya kuma bayar da shawarar a kafa sabuwar rundunar tsaro domin kula da dazuka, wanda yawancin a can ake aikata laifuka.

Ya ce dole ne a horas da dakarun rundunar sosai, a ba su makamai irin su AK-47, sannan a cire siyasa wajen kula da harkar tsaro.

Ya ce idan aka daina siyasantar da harkar tsaro, aka mayar da hankali kan ƙwarewa, za a iya cimma nasara.

Ya kuma buƙaci gwamnati ta naɗa shugabanni nagari a hukumomin tsaro, tare da tallafa wa ’yan sa-kai da kuɗi da kayan aiki, inda ya yaba wa ƙoƙarinsu duk da cewa ba sa karɓar albashi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Associated Press: Harin Iran Akan Sansanin Amurka Dake Kasar Qatar Ya Lalata Wata Cibiyar Sadarwa
  • An Kashe Jami’in Sojan HKI A Gaza
  • Bafarawa Ya Kaddamar Da Kungiyar Hada Kan Arewa Da Samar Da Zaman lafiya A Kaduna 
  • Qalibof: Asarorin HKI A Yakin Kwanaki 12 Yafi Abinda Ta Bayyana
  • Sojoji sun kashe ’yan fashin daji masu yawan gaske a Zamfara
  • An kashe mutum ɗaya da ƙona gidaje sama da 100 a Taraba
  • Somaliya: Kungiyar Al-Shabab Ta Kai Wa Barikin Soja Hari A Birnin Magadishu
  • Bafarawa Ya Kaddamar Da Wata Kungiya Mai Suna “Arewa Cohesion Initiative” Don Maganin Kalubalen Da Yankin Arewa Ke Fuskanta
  • Sojoji sun tarwatsa matsugunin ’yan ta’adda da kashe wasu a Borno
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Neja