A wurin mu Malikawa, mun dauki watannin nan guda uku a matsayin lokacin Hajji, wasu kuma sun ce a’a, daga kwana goman farkon nan na Zhul-hijja, lokacin ya kare, to amma kuma idan aka yi la’akari za a ga cewa akwai sauran ibadodin Hajjin da suka shige wadannan kwanakin goma irin su Jifa da ake dawowa Mina a yi bayan Sallar Idi da Dawafin bankwana.

Shi ya sa Malikawa muka dauki watannin ukun baki daya a matsayin lokacin Hajji. Kuma Ibn Hazan ya goyi bayan haka, don ba za a dauki wata biyu da kwana goma a ce musu watanni uku ba.

 

Kamar yadda bayani ya gabata, Hajji ba a ko ina ake daura haramar yin sa ba, yana da wuraren da Shari’a ta kebance don yin harama da shi. Duk wanda zai yi Hajji ko Umura, bai halasta gare shi ya tsallaka wadannan wuraren ba tare da ya yi harama ba.

 

Manzon Allah (SAW) ya sanya wa ko wadanne mutane wurin da za su yi harama (Mikati). Ya sanya wa mutanen Madina Zhal-hulaifa ya zama wurin haramarsu. A yanzu ana kiran wurin da sunan Abaru Ali. Haka nan sauran mutanen duniya da suka fara wucewa Madina ziyarar Annabi (SAW) daga ko ina a duniya, idan za su dawo Makka yin Hajji ko Umura su ma a nan Zhal-hulaifa za su yi harama. Ba za su ce sai sun koma Mikatinsu ba da aka sanya musu. Wurin yana nan daga Arewacin Madina kuma tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 450 ne, kusan shi ne mafi tsawo daga Makka a cikin sauran wuraren haramar Hajji.

 

Annabi (SAW) ya kafa wa mutanen Sham (Siriya) da sauran kasashe irin su Palasdin da Urdun wurin da ake kira Juhufa ya zama wurin haramarsu. Wurin yana nan a arewa-maso-yammacin Makka kusa da Radiga wadda Hausawa suke kira da Radinga. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 187. Amma tunda ruwa ya shafe Juhufa a halin yanzu, Radiga ce ta zama wurin haramar su mutanen Sham da Misra da sauran wadanda suka bi ta wajen, ita kuma tsakaninta da Makka tafiyar kilomita 204. Muma mutanen Nijeriya nan ne Mikatinmu da sauran mutanen kasashen da za su bi wurin, kamar na Yammacin Afirka.

 

Su kuma mutanen Najadu, Annabi (SAW) ya sanya musu Karnul-manazil ya zama Mikatinsu. Wani dutse ne da ke gabashin Makka yana kallon Arfa. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 94.

 

Su kuwa mutanen Yemen, Annabi (SAW) ya sanya wa mutanensu Yalamlam ya zama Mikatinsu. Shi ma dutse ne da ke kudancin Makka. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 54.

 

Annabi (SAW) ya kafa wa mutanen Iraki Zatu’irkin a matsayin Mikatinsu. Wuri ne da yake arewa-maso-gabas din Makka. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 94, nisan shi da Makka daya ne da na Mikatin mutanen Najadu.

 

Wadannan wurare da Annabi (SAW) ya kafa, su ne wuraren da mutanen duniya za su yi haramar Hajji ko Umura.

 

Idan zuwa Hajji ko Umura ya kama mutum a wata kasar da ba tashi ba, zai yi amfani ne da Mikatin da mutanen wannan kasar suke yin harama, ba zai ce tunda shi ba dan kasar ne ba, sai ya koma ta Mikatin kasarsa, a’a, zai yi haramar ce a Mikatin ‘yan kasan, ma’ana kamar shi ma ya zama dan kasar ke nan.

 

Amma su kuma wadanda suke cikin Makka (baki da ‘yan garin), a nan cikin garin ne za su yi harama. Kamar misali wadanda suke Hajjin Tamattu’i, bayan sun kammala Umura, to idan ranar da za a yi haramar Hajji ta zo, tun daga gida za su yi harama ba sai sun je wani wuri ba.

 

Amma idan dan cikin Makka zai yi Umura bayan Hajji, sai ya fita zuwa Tan’im kafin ya yi harama kamar yadda Annabi (SAW) ya yi umurni a kai Ummul-Mu’umina Aisha (RA) ta yi haramar Umura.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita za su yi harama Hajji ko Umura

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Addu’ar Kwana 3 Don Samun Isasshen Abinci

Ma’aikatar Gona da tsaron abinci ta tarayya ta sanar da gudanar da addu’a da azumi na kwanaki uku domin neman taimakon Allah wajen kare ƙasar nan da kuma tabbatar da wadatar abinci. Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da aka fitar a ranar 11 ga Yuni, 2025, wadda Daraktar Gudanarwa, Mrs. Adedayo Modupe O., ta sanya wa hannu.

A cewar sanarwar, dukkanin daraktoci, da mataimakan daraktoci, da shugabannin sassan sarrafa kayayyakin amfanin gona da sauran ma’aikatan ma’aikatar za su halarta. An sanya wa wannan shiri suna “Neman Taimakon Ubangiji Don Kariya da Cigaban Kasa.”

Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne – HJRBDA Gwamnatin Gombe Ta Yi Albishir Ɗin Gina Babban Zangon Noma Da Kiwo Ɗauke Da Kasuwar Duniya A Jihar 

Modupe ta bayyana cewa manufar wannan addu’a ita ce neman jagorancin Allah da tallafinsa ga ƙoƙarin gwamnati wajen samar da ingantaccen tsarin abinci mai ɗorewar a fadin ƙasa. Za a gudanar da zaman addu’ar ne a shalƙwatar ma’aikatar da ke Abuja a ranakun Litinin: 16, 23 da 30 ga Yuni, 2025.

Sanarwar ta buƙaci dukkan ma’aikata su kasance cikin azumi domin samun tsarkakewa da shiri na musamman wajen roƙon Allah game da matsalolin da ke addabar fannin noma da tsaron abinci a Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kungiyar Abokan Yarjejeniyar M.D.D Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ke Kai Wa Kan Iran
  • Amfanin ‘Ya’yan Gwanda Da Yadda Ake Sarrafa Su
  • Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Addu’ar Kwana 3 Don Samun Isasshen Abinci
  • Wani Gidan Gona A Jihar Ogun Zai Fitar Da Tarwada Ta Kimanin Naira Biliyan Shida A 2025