To Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, a matsayin aike shi ne karshe, shi ya zo da aike na karshe, wanda daga shi aiken Allah (Tabaraka Wa Ta’ala) ya kare. Sai dai na Manzon Allah (SAW) din nan ne za a yi ta bincikawa a yi ta gani saboda na Manzon Allah din nan yanzu ya dace da kowanne zamani. Ubangiji Tabaraka wa Ta’ala shi ne mai cikakken ilimi, shi ya halicci ilimi ma.

Allah shi ne farko kanta, shi ne karshe kanta, shi ne a sarari kuma shi ne a boye, ma’ana ya san komai ciki da bai, don haka a wannan matsayi nasa ya zuba ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam wannan ilimai a cikin wannan littafi na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam.

Galibin Annabawa kowa Allah yana aiko shi da iyakar ilimi da ya yi daidai da zamaninsa, duk idan muka duba a Alkur’ani za mu ga kowanne Annabi da irin kiran da ya yi. Cewar “a bauta ma Allah shi kadai” wannan na dukkan Annabawa ne, amma kuma za ka ga wani ya yi kira zuwa ga girmama iyaye, wani ya yi kira zuwa a yi awo da adalci, wani ya yi kira zuwa a yi tsarki, da sauransu, har aka zo kan Annabi Musa (AS) shine Mai Shari’a “Al-Kitabu”.

Allah ya ba Annabi Musa “Constitution” na abubuwa mai hukunce-hukunce wajen dari shida da wajen goma sha uku. Duk abinda Annabi Musa yake kai, da duk abin da zamaninsa yake kai sai da Allah ya rubuce masa shi a cikin Attaura. Kuma ya yi masa dalla-dallansa, sannan ya fitar da wadansu kyawawan dabi’u ya sanya masu suna “wasiyyoyi guda goma” (The Ten Commandments), su ma a cikin littafin suke amma saboda muhimmancin su ya sa Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya ware su daban. Amma wannan sako na Attaura iya na wannan zamanin ne, iya na al’ummar Annabi Musa ne (Yahudu), ba zai zama har abada ba. Don haka da Annabi Isah (AS) ya zo sai ya gaya masu “to Ni kam Allah ya aiko Ni in saukaka wadannan hukunce-hukunce na Annabi Musa”. Kamar yanda shi ma Annabi Musa Allah ya saukaka masa ne daga hukunce-hukuncen Hamuraabi; wani sarki da aka yi a Babylon, kasar Iraki. Kila shi ma Annabi ne, kila Bawan Allah ne, amma dai Sarki ne kasaitacce wanda shi ya kafa dokoki masu yawa a cikin tsararensa na mulki (Constitution). Akwai kisa da yawa a cikin hukunce-hukuncensa, amma Allah sai ya sanya ma Annabi Musa kisa goma sha takwas kawai. Amma da Annabi Isah (AS) ya zo, shi kuma yanzu kiransa ba iyakar Bani Isra’ila (al’ummar Annabi Musa) kadai ba ne, Annabi Isah (AS) yana so ya fadada kiransa zuwa ga halitta baki daya, wanda kuwa yake son irin haka to dole hukunce-hukuncensa su zama masu sauki kuma masu kyau.

Ko su hukunce-hukuncen masu tsauri na Attaura da aka sanya ma Bani Isra’ila an sanya masu ne saboda zaluncinsu. Shi kuwa Annabi Isah (AS) da ya zo sai ya ce ma Bani Isra’ila ku yi imani da ni, ni kuwa zan dan saukaka maku wani abu daga cikin wadanda aka haramta maku. Akwai wani wa’azinsa da ya yi a majami’a (temple) da dare, ya ce masu: “a Attaura ta ce muku kaza ni kuwa na ce muku kaza, a Attaura ta ce kar ku ci kaza, ni kuwa na ce ku ci babu wani abu da zai shiga cikin Dan Adam da zai gurbata Dan Adam din nan, shi dan Adam maganarsa da take fitowa daga cikinsa da kuma mummunan kudirinsa su ne suke gurbata shi.

Don haka za ka ga mabiyan Annabi Isah ba su da wani abu na ci da yake haram, domin ya ce shi bai ga wani abu daga waje wanda zai shiga cikin Dan Adam ya gurbata shi ba, sai dai abin da yake cikin Dan Adam din ne kawai zai iya gurbata Dan Adam, ma’ana shi Dan Adam din ne najasar da kansa, domin daga cikinsa maganganun batancin suke fitowa. Sai Annabi Isah (AS) ya ce ma jama’arsa “amma kun ga Annabi Ahmadu (SAW) da zai zo, shi kuwa zai zubar muku da duk abubuwan da aka hana maku din nan gaba daya, zai zubar da duk wani kunci”. Amma idan mai tambaya ya tambaye ka to ya aka yi na ga Haram a cikin addinin Annabi Muhammad (SAW) masu tarin yawa? Amsar ita ce wannan duk aikin malamai da fakihai ne, su ne suka sanya mafi yawancin haramun din cikin addinin nan namu tun daga kan Sahabbai (Allah ya yarda da su) zuwa Tabi’ai zuwa abin da ya yi kasa, akwai su “Sadduz Zari’ati” akwai haramta duk wasu hanyoyi wadanda sai idan ka biyo ne sannan za su iya kai ka ga aikata laifin. To Alhamdu Lillahi, yanzu zamani ya kawo, ko ka zama Annabi Isah din; ka zubar da kadan, ko kuma ka zama al’ummar Annabi Muhammadu; ka zubar da gaba daya! Kur’aninka dai yana nan ya fada maka komai gaba daya.

Annabi Isah (AS) ya zo da abubuwa masu sauki, ya yada littafan da suka zo kafin sa, Allah ya sanya sauki a cikin lamarinsa, Allah ya sanya sauki a cikin mutanensa, don haka ‘Yan Adam suka karba, amma saboda sauki (domin duk abu in ya yi sauki to ya zama na ‘Yan Adam baki daya, haka kuma duk abu in ya yi tsauri to iya naku ne). Daga nan har Allah ya kawo Bulus, wanda almajirin Annabi Isah din ne, shi kuwa Bulus gaba daya ma sai ya watsar da dokokin Attaurar ma, sai ya dauki “wasayal ashri” din nan, kawai abin da ya dauka a cikin Attaura kenan. To mu ma ikon Allah, wannan “wasaya” guda goma Allah ya tafi da su a cikin Kur’aninmu, ita ce “Furkánu”.

To, amma idan muka zo wajen Annabi Muhammad (SAW) wanda shi ne karshen ma’aika, shi kuwa Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya tattaro karatun fasahar “Engineering” din gaba daya ya damka masa (SAW). Duk littafin tafsirin da ka duba za ka ga ana yin sa ne daidai da wayewar al’ummar lokacin amma Alkur’anin kansa na farko ne na karshe ne, wata fahimtar ma tasa ba ta zo ba sai nan gaba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Tabaraka Wa Ta ala

এছাড়াও পড়ুন:

Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Umara Zulum ya sanar da fara fitar da kayayyakin robobi zuwa ƙasashen duniya wanda hakan ke nuna wani gagarumin ci gaba a wani ɓangare na ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arzikin Jihar.

Gwamnan ya jaddada cewa, wannan matakin wani ɓangare ne na babbar ajanda na bunƙasa masana’antu da kuma kawar da dogaro da jihar kan yi na kason da gwamnatin tarayya ke bayarwa duk wata.

Ƙwallo ta kashe ɗan wasan Cricket Za a rataye wanda ya kashe ɗan uwansa a Ekiti

Zulum ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin rangadin duba masana’antar robobi ta Borno da ke cikin yankin masana’antu na Maiduguri.

“Ina farin cikin lura cewa mutanen Jihar Borno ba za su sake sayen kayan robobi daga wasu wurare ba, kun ga an sayar da kayayyakin ga ƙasashen maƙwabta da sauran jihohi a cikin Najeriya.”

“Za mu zuba jari sosai a masana’antunmu, don haka nan gaba kaɗan, gwamnatin Jihar Borno ba za ta sake dogara da asusun tarayya ba don ayyukanta na yau da kullum,” in ji Zulum.

Gwamnan ya bayyana cewa masana’antar ta fara fitar da kayayyakinta ga ƙasashen waje, tare da jigilar kayayyakin filastik da aka gama zuwa ƙasashe maƙwabta kamar Chadi da Jamhuriyar Kamaru.

Zulum ya lura cewa an fara gina cibiyar ne a lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Kashim Shettima, amma an farfaɗo da ita a matsayin wani ɓangare na shirin murmurewa da ci gaban gwamnatinsa.

Wasu daga cikin kayan robobin

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • ‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
  • Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida
  • Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
  • Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai
  • An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
  • Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 
  • Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum