2025-09-17@22:17:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7236

«a watan Agusta»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Wata kotu a Ƙasar Amurka, ta yanke wa Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede, daga Jihar Osun, hukuncin ɗaurin shekara huɗu da rabi a gidan yari saboda samun sa da laifin zamba a tallafin COVID-19. Alƙalin kotun, Christopher Boyko ne, ya yanke wa Sarkin mai shekara 62 a duniya hukunci a ranar 26 ga watan Agusta, 2025. ’Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun sace ɗan kasuwa a Kaduna ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe Sarkin ɗan ƙasar Amurka ne, da ke zaune a Ohio. Bayan ya fito daga gidan yari, zai yi shekara uku ƙarƙashin kulawa, sannan dole ne ya biya sama da dala miliyan 4.4. Kotun ta kuma ƙwace gidansa da ke Ohio da...
    ’Yan bindiga sun kai hari garin Hunƙuyi da ke Ƙaramar Hukumar Kudan, a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wani ɗan kasuwa. Mutanen yankin sun ce maharan sun kai hari  ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare. ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe Babu ɗaya daga cikin buƙatunmu da gwamnati ta aiwatar — Shugaban ASUU Maharan sun shiga yankin ne ta ɓangaren Katsina ɗauke da bindigogi, inda suka dinga harbi a sama. Sun harbe wani mutum mai suna Aminu Shehu har lahira, sannan suka yi awon gaba da wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Shehu Dakin. Majiyoyi, sun bayyana cewa maharan sun yi amfani da wayar Alhaji Shehu wajen kiran iyalansa,...
    ’Yan bindiga sun kai hari garin Hunƙuyi da ke Ƙaramar Hukumar Kudan, a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wani ɗan kasuwa. Mutanen yankin sun ce maharan sun kai hari  ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare. ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe Babu ɗaya daga cikin buƙatunmu da gwamnati ta aiwatar — Shugaban ASUU Maharan sun shiga yankin ne ta ɓangaren Katsina ɗauke da bindigogi, inda suka dinga harbi a sama. Sun harbe wani mutum mai suna Aminu Shehu har lahira, sannan suka yi awon gaba da wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Shehu Dakin. Majiyoyi, sun bayyana cewa maharan sun yi amfani da wayar Alhaji Shehu wajen kiran iyalansa,...
    Shirin Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL) ya raba wa ƙungiyoyin manoma 47 a Jihar Gombe, buhunan iri na zamani 6,220 don bunƙasa harkar noma. An gudanar da rabon ne yayin taron kwanaki biyar na masu ruwa da tsaki kan kula da manyan koguna na Gongola, Gali-Lamurde da Hawal-Kilunga, wanda yake ɗaya daga cikin muhimman ayyukan ACReSAL a Najeriya. Babu ɗaya daga cikin buƙatunmu da gwamnati ta aiwatar — Shugaban ASUU ’Yan bindiga sun sace ma’aurata da ’yarsu mai shekara ɗaya a Katsina Shugaban shirin a Jihar Gombe, Dokta Sani Adamu Jauro, ya ce Gwamna Inuwa Yahaya ya nuna jajircewa wajen tallafa wa manoma ta hanyar shirin. Ya ƙara da cewa an samu nasarori kamar shuka bishiyoyi a dukkanin ƙananan...
    Ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya bayyana jin dadinsa ga hadin kai da goyon bayan Iran ga kasarsa A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Iran, ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya yabawa irin hadin kai da goyon bayan Iran ga ‘yancin kai, yana mai jaddada aniyar Iran na kare ta daga barazanar Amurka. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna da takwaransa na kasar Venezuela Ivan Gil Pinto ta wayar tarho game da alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaban da ake samu a yankin Caribbean. A cikin wannan kiran, Ministan Harkokin Wajen Venezuela ya ba da rahoto kan abubuwan da ke faruwa a yankin Caribbean bayan karuwar barazanar Amurka da...
    Rasha ta ba da shawarar tsawaita kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran Mataimakin wakilin dindindin na kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Dmitry Polyansky ya sanar da cewa, Rasha ta gabatar da shawarwarin a Majalisar Dinkin Duniya na tsawaita sahihancin kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran. Tashar talabijin ta Russian Today ta ruwaito cewa: Polyansky ya shaida wa manema labarai cewa: “Wannan ba batun sassauta takunkumi ba ne na tsawon watanni shida, amma a maimakon haka, a tsawaita kuduri mai lamba 2231. A gaskiya ma, Rasha da Chana, a matsayin masu kula da shirin hadin gwiwa na shirin (JCPOA), suna son ba da karin sarari ga diflomasiyya da...
    Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), Farfesa Chris Piwuna, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta aiwatar da ɗaya daga cikin yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙungiyar ba. Ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin hira da gidan talabijin na Trust TV. ’Yan bindiga sun sace ma’aurata da ’yarsu mai shekara ɗaya a Katsina DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Farfesa Piwuna, ya ce ASUU a koyaushe na zaɓar tattaunawa da jami’an gwamnati a matsayin mafita. Amma duk da cewa sun cimma matsaya kan batutuwa masu muhimmanci kamar kuɗaɗen gudanarwa, albashi, ’yancin malamai, ‘yancin jami’o’i, da sake duba wasu dokoki, ba a ɗauki mataki kan kowanne ba. “Babu saɓani a tsakaninmu da tawagar...
    Uzodimma ya ce ƙarin albashi zai inganta rayuwar ma’aikata, sannan ya bunƙasa tattalin arziƙin jihar. Ya kuma bayyana cewa kuɗaɗen shiga na cikin gida sun ƙaru daga Naira miliyan zuwa sama da Naira biliyan uku a kowane wata, yayin da bashin jihar ya ragu daga sama da Naira biliyan 280 a shekarar 2020 zuwa Naira biliyan 100. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa cire tallafin mai, yana cewa duk da ya jawo tsadar rayuwa, amma ya ƙara yawan kuɗin da ake raba wa jihohi kuma ya bai wa gwamnati damar yin sauye-sauye. Gwamnan ya ƙara da cewa daga ranar 27 ga watan Agusta, gwamnati za ta fara biyan kashin ƙarshe na kuɗaɗen fansho da ake bai wa tsoffin ma’aikata,...
    Gwamna Uba Sani ya umarci jami’an tsaro da su kamo waɗanda suka aikata laifin tare da wanzar da zaman lafiya. Jami’ai sun ce jihar ta samu zaman lafiya sosai cikin shekaru biyu da suka gabata sakamakon Kaduna Peace Model, wanda ya rage rikice-rikice tare da sake ba da damar zuwa gonaki da kasuwanni a wuraren da aka daɗe ana fama da rikici. Sai dai sun yi gargaɗin cewa rashin tsaro daga jihohin maƙwabta na yawan zuwa cikin Kaduna, don haka ana buƙatar gwamnatoci na jihohi su haɗa kai domin kawo ƙarshen irin waɗannan hare-hare a nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”. A al’adance, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan. NAJERIYA A YAU: Ci Gaban Da Harshe Da Al’adun Hausa Suka Samu A Shekaru 10 DAGA LARABA: Yadda wasu tsare-tsaren ba da tazarar haihuwa ke yin illa ga mata Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waɗannan mazan da ba sa son haihuwa da kuma dalilan su. Domin sauke shirin, latsa nan
    Haka kuma, a wani samame daban da rundunar ta kai a ranar 15 ga watan Agusta, 2025, ‘yansanda a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu sun yi artabu da ‘yan bindiga a kusa da garin Dankade. Sun ceto mutum biyu da aka sace; Tukur Bello da Isyaka Abubakar, waɗanda aka sace a dajin Gairi na Jihar Zamfara a ranar 9 ga watan Agusta yayin da suke kiwon shanu. ‘Yansanda sun ce sun ƙwato makamai da harsasai daga hannun ‘yan bindigar, tare da alƙawarin ci gaba da yaƙi da masu garkuwa da mutane a faɗin ƙasar nan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    Shugaba Donald Trump, ya yi barazanar sauke Lisa Cook, Gwamnar Babban Bankin Amurka (Federal Reserve), yana mai sukar yadda ake tafiyar da harkokin bankin, musamman batun bayar da bashi da tsare-tsaren lamuni. A wata sanarwa da fadar White House ta fitar, Trump ya zargi Cook da gabatar da “bayanan ƙarya” kan sharuɗan bayar da lamunin gidaje (mortgage), yana mai cewa hakan ya jefa dubban Amurkawa cikin wahala sakamakon hauhawar kuɗin ruwa da kuma tsadar bashi. Sai dai Lisa Cook ta mayar da martani da cewa shugaban ba shi da ikon sauke ta daga muƙamin da take riƙe da shi, saboda dokar da ta kafa Babban Bankin Amurka ta tanadar da cikakken ’yanci ga ’yan kwamitin gudanarwarsa. Ta sha alwashin cewa...
    Cutar kwalara ta ɓarke a ƙananan hukumomin Gumi da Bukkuyum a Jihar Zamfara, inda ta kashe aƙalla mutum bakwai tare da kwantar da kusan mutum 200 a asibiti. Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Hon. Sulaiman Abubakar Gumi, ya ce cutar ta fara tun 10 ga watan Agusta, kuma tana ƙara yaɗuwa. Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya Hukumar NRC Ta Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Kasa Na Abuja zuwa Kaduna Ya bayyana cewa rashin tsaftar muhalli da ruwan sama sun taimaka wajen yaɗuwar cutar, musamman a inda ‘yan gudun hijira suke zaune. Ya yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, cutar na iya zama annoba. Daga...
    Idris ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesan sa da jajircewar sa wajen zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai a Nijeriya.   A cewar sa: “Yayin da muke ɗaukar wannan babban mataki na ƙaddamar kwangilar gyara tiransimitar ‘shortwave’ ta Muryar Nijeriya mai ƙarfin kilowat 250, ya dace mu nuna ɗimbin godiyar mu ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa hangen nesa da jajircewar sa wajen farfaɗo da kuma zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai na Muryar Nijeriya.”   Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa wannan aikin zai sauya yanayin yadda ake yaɗa labarai a ƙasar nan.   Ya ce: “Da zarar an kammala wannan aiki, na’urorin tiransimita na VON da aka...
    Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya kaddamar da shirin dashen bishiyoyi na shekarar 2025 a Damaturu babban birnin jihar. Gwamna Buni ya kuma yi gargadi game da sare itatuwa ba gaira ba dalili, yana mai jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta amince da ayyukan da za su sanadin kwararowar hamada da lalata muhalli ba. Da yake jawabi a wurin bikin mai taken: “Shirin Buni na dakile kwararowar hamada” Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na yaki da kwararowar hamada, da raya gurbatacciyar kasa, da dakile illolin sauyin yanayi. Ya yi nuni da cewa, tun daga shekarar 2020, gwamnatin jihar Yobe ta dasa miliyoyin itatuwa iri-iri a fadin jihar domin dakile kwararowar hamada daga kudancin Jihar. Daga kanmu,...
      Opeifa ya kara da cewa, tuni tawagar kwararru daga Hukumar, jami’an Hukumar Binciken Tsaro ta Nijeriya (NSIB) da sauran hukumomin da abin ya shafa suka isa wurin domin gano musabbabin wannan matsala da kuma tabbatar da daukar matakan kariya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta dakatar da sufurin jirgin ƙasan da ke jigila a tsakanin Abuja zuwa Kaduna. NRC ta sanar da ɗaukar wannan matakin ne har sai an kammala bincike kan hatsarin jirgin da ya auku a wannan Talatar. An yi kiciɓus da gawar ’yar shekara 14 a cikin gida a Kano Hisbah ta haramta al’adun gargajiya yayin bukukuwan aure a Bauchi Shugaban hukumar, Kayode Opeifa, ne ya sanar da haka jim kaɗan bayan faruwar lamarin. Ya bayyana cewa tuni tawagar masu bincike da suka haɗa da ma’aikatan NRC, hukumar binciken sufuri ta ƙasa (NSIB) da sauran hukumomin tsaro, sun isa wurin domin gudanar da bincike. Opeifa ya yi watsi da maganganun da ake...
      A nasa bangaren Volodin ya ce, a karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, dangantakar Rasha da Sin ta ci gaba da zurfafa cikin nasara. Majalisar dokokin Rasha ta himmatu wajen aiwatar da muhimman yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin dokokin kasashen biyu, da kuma himmatuwa wajen samun karin sakamako mai kyau a dangantakar kasashen biyu. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Fasinjoji na jirgin kasa wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka kan layin dogo da misalign karfe 11:00 nan safe kusa da garin jere. Da dama daga cikin fasinjojin suna cikin tashin hankali saboda matsalolin tsaro da ake fama da shi a kan hanyar. Amma Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa an kawo jami’an tsaro a yankin don tsaron fasinjojin. Kamfanin jiragen kasa na kasa wato ‘The Nigerian Railway Corporation (NRC) bai bada wani bayani kan al-amarin ba har zuwa lokacin bada wannan labarin. Saukan jirgin daga layin dogon dai bai jiwa wani rauni ba, kuma babu wanda ya rasa ransa. A cikin watan mayun shekara ta 2024 da ya gabata ma, an sami...
    Ribadu ya yaba da jajircewar sojoji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro da suka gudanar da aikin, yana mai cewa, wannan wata nasara ce da za a yi alfahari da ita a tarihin yaki da ta’addanci.   A Guji Siyasantar da Tsaro Sai dai Ribadu ya gargadi shugabannin siyasa da masu rike da madafun iko da su guji siyasantar da al’amuran tsaro, yana mai cewa: “Wannan ƙalubale na gama gari ne, ba wai na shugabanni kaɗai ba. Domin haka nake kira ga al’umma da shugabanni su daina siyasantar da tsaro.”   Ribadu ya ƙara da cewa, gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, za ta ci gaba da yin duk abin da ya kamata domin magance barazanar tsaro tare da kawo...
    An yi kiciɓus da gawar wata budurwa mai shekaru 14 a cikin gidansu da ke unguwar Dandinshe a Ƙaramar Hukumar Dala da ke Jihar Kano. Lamarin dai ya ɗugunzuma mazauna unguwar yayin da Aminiya ta riski iyaye, ’yan uwa da kuma maƙwabta cikin alhini a yayin ziyarar da ta kai har gida. Hisbah ta haramta al’adun gargajiya yayin bukukuwan aure a Bauchi Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka Bayanai sun ce an yi arba da gawar Fatima Sulaiman rataye a jikin wata taga a cikin gidansu, lamarin da ya jefa shakku da ayoyin tambaya kan musabbabin mutuwarta. Aminiya ta zanta da mahaifiyar marigayiyar, Malama Madina Inuwa Makwalla, wadda ta bayyana ganawa ta ƙarshe da ta yi da...
    Hukumar ta SEMA ta dauki nauyin kwashe fasinjojin da suka makale, da bayar da agajin gaggawa, da kuma tabbatar da cewa duk wadanda abin ya shafa sun samu kulawar gaggawa a inda ya dace.   “Gwamnan ya ba da umarnin a baiwa fasinjoji duk wani tallafi da ya dace don rage tasirin wannan mummunan lamari, duk wanda ya samu rauni za a kula da shi cikin gaggawa, yayin da ake ba da tallafin gaggawa na psycho-socio da tallafin likita ga wadanda abin ya shafa,” in ji Maiyaki.   Sanarwar ta ci gaba da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin jirgin, inda ta kara da cewa gwamnatin jihar na sanya ido sosai kan lamarin tare...
    Hukumar Hisbah ta haramta karuwanci da duk wasu munanan ɗabi’u da ake gudanarwa a otal-otal, wuraren casu da duk wasu cibiyoyin nishaɗi a Jihar Bauchi. Babban Kwamishinan Hisbah, Barista Aminu Balarabe Isah, ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da masu otal-otal da wuraren shaƙatawa a Bauchi. Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka Jirgin kasa dauke da fasinjoji ya yi hastari a hanyar Kaduna-Abuja Ya ce an haramta gudanar da al’adun gargajiya irin su Shadi, Sharo, Garaya da kuma shagulgulan wannan zamani kamar Kauyawa Day, Gala, DJ, Aloba da sauransu a bukukuwan aure. Isah ya ce an ɗauki waɗannan matakan ne bayan samun korafe-korafe daga jama’a kan yadda abubuwa na rashin tarbiyya da tayar da...
    Wasu daga cikin ’yan kasuwar sun yi kira ga gwamnati da ta sake duba matsayar ta, inda suka ce kasuwar ce tushen rayuwarsu da iyalansu, kuma rushe ta zai kara jefa su cikin talauci da rashin aikin yi. Haka kuma, sun yi barazanar kai ƙarar gwamnati kotu idan aka ƙi biyan su diyya, domin a cewarsu, an tauye musu haƙƙin kasuwanci da kuma dukiyar da suka shafe shekaru suna tarawa. Sai dai gwamnatin Legas ta ce irin waɗannan ayyuka na rusau na daga cikin shirinta na zamanantar da manyan kasuwanni, don su dace da tsarin birane na zamani da kuma kare muhalli. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Wasu daga cikin ’yan kasuwar sun yi kira ga gwamnati da ta sake duba matsayar ta, inda suka ce kasuwar ce tushen rayuwarsu da iyalansu, kuma rushe ta zai kara jefa su cikin talauci da rashin aikin yi. Haka kuma, sun yi barazanar kai ƙarar gwamnati kotu idan aka ƙi biyan su diyya, domin a cewarsu, an tauye musu haƙƙin kasuwanci da kuma dukiyar da suka shafe shekaru suna tarawa. Sai dai gwamnatin Legas ta ce irin waɗannan ayyuka na rusau na daga cikin shirinta na zamanantar da manyan kasuwanni, don su dace da tsarin birane na zamani da kuma kare muhalli. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarihi ba zai yafe jinkirin yin Allah wadai da bala’in Gaza ba Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: “Al’umma ta tuna cewa bala’in Gaza bai shafi musulmi kadai ba, wannan lamari ne na gwaji na lamiri na dukkanin bil’adama, don haka suna kira ga dukkanin al’umma ba tare da la’akari da addini ko yanayin kasa ba, da su tsaya a bangaren bil’adama, adalci da mutunci, wato a bangaren dama na tarihi.” Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a wajen taron baje kolin na majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, inda ya yi jawabi ga...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tun bayan barkewar yakin da Iran, babu wata hulda da ta hada ta da Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya jaddada cewa: “Turawa za su iya taka muhimmiyar rawa a shawarwari,” yana mai bayanin cewa: “Tun bayan barkewar yaki da Iran, kasar Iran ta daina yin mu’amala da Amurkawa, amma tana ci gaba da hulda da Turawa ko da a lokacin da ake tsaka da yakin.” A wata hira da jaridar Süddeutsche Zeitung ta Jamus dangane da shawarar da Turai ta gabatar na tsawaita wa’adin aiki da hanyar da za a bi wajen ganin an dawo da takunkumin majalisar dinkin duniya kan Iran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen...
    Shugaban kasar Faransa ya bayyana cewa: Kakaba yunwa ga dukkan al’umma laifi ne da ya wajaba a dakatar da ita nan take Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ce yunwar da al’ummar zirin Gaza suke ciki wani laifi ne da ya zama dole a dakatar da ita nan take. A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, Macron ya kara da cewa a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jiya litinin ya tattauna da sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani game da mummunan halin da ake ciki a Gaza. Ya ci gaba da cewa, “Suna aiki kafada da kafada da Qatar don tabbatar da nasarar kokarin masu shiga tsakani da kuma shirya taron kan abin da ya...
    Ya ƙara da cewa jama’a na shiga ADC saboda suna ganin ita ce mafita. “Gazawar gwamnatin APC ta tilasta mutane su nemi mafita, kuma ADC za ta bayar da wannan damar,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yau 26 ga watan Agusta take ranar murnar zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya. A halin yanzu shirye-shirye sun yi nisa domin fara gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya a birnin Daura, Jihar Katsina. An shirya gudanar da gagarumin bikin na bana a birnin Daura ne, kasancewarsa inda ake gani a matsayin asalin Hausawa, shekaru arau-aru. Mahaya dawaki da sauran mahalarta bikin daga sassa daban-daban na Najeriya da kasashen waje da mazauna garin Daura sun fara tururuwa zuwa filin bikin, wanda zai samu. An kuma shirya gudanar da gagarumin hawan daba a Fadar Sarkin Daura, albarkacin zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na 10. A wannan ranar ake cika shekara 10 da fara wannan gagarumin biki,...
    Mataimakin Ministan harkokin wajen Iran da takwarorinsa na Faransa, Jamus, da Birtaniyya za su gudanar da wani sabon zagaye na tattaunawa a birnin Geneva na kasar Switzerland, a daidai lokacin da kasashen uku ke barazanar aiwatar da abin da ake kira tsarin dawo da takunkumin  Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a kan Iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya fada a ranar Litinin cewa, za a koma  yin shawarwari tsakanin wakilan Iran da E3 a ranar Talata. Ya ce za a gudanar da taron ne a matakin mataimakan ministocin harkokin waje da daraktocin siyasa. Hakan na zuwa ne bayan wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da babban wakilin kungiyar EU mai...
    A duk ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara ake bukukuwan zagayowar Ranar Hausa ta Duniya. An fara wannan biki ne tun a shekarar 2015, inda wani tsohon ma’aikacin sashen Hausa na BBC kuma ma’aikacin TRT Hausa a yanzu, Abdulbaƙi Jari Aliyu ya ƙirƙiro tare da wasu masu amfani da shafukan sada zumunta. An ɓullo da ranar ce domin haɗa kan masu magana da harshen Hausa a faɗin duniya da nufin magance matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya. Da farko dai, an fara bikin wannan rana ce kamar wasa a shafukan sada zumunta, inda aka yi ta amfani da kalmar #RanarHausa. Zuwa shekara ta 2018 kuma aka fara yin bikin a zahiri tare da gudanar da tarurruka...
    Matashin, wanda yake yin atisaye a makarantar Mount Kelly ta Birtaniya, ya nuna cewa Nijeriya na da ƙwarewa a harkar ninkaya, duk da cewa har yanzu babu ɗan wasan ninkayar Nijeriya da ya taɓa kai wa gasar Olympics. Nijeriya dai ta taɓa lashe lambobin yabo 27 a wasannin Olympics amma ba ta taɓa yin nasara a fannin ninkaya ba. Hukumar wasanni ta kasa ta taya shi murna, tare da hukumar kula da wasannin ruwa ta Najeriya. Darakta Janar, Bukola Olopade, a cikin sanarwarsa a ranar Lahadi, ya ce wannan babbar nasara ce ga wasannin Najeriya baki ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Batun cikin gidan kasar Labanon ya jaddada cewa, kungiyar ba za ta taba mika makamanta ba matukar dai Isra’ila na mamaye da wani yanki na Lebanon, ko kuma akwai barazana a kan kasar. A yayin jawabin nasa, Sheikh Naim ya nanata katsalandan din wuce gona da iri da Amurka ke yi a cikin harkokin kasar Labanon, yana mai tabbatar da cewa hukumar kasar ce ke da alhakin kare kasar ta Lebanon, da tsaronta, da kuma ‘yancin kai. Dangane da batun kwance damarar kungiyar kuwa, Sheikh Qassem ya ce matakin gwamnatin Labanon ba shi da tushe balle makama, kuma idan har ta ci gaba da bin wannan tafarki, to kuwa ta mika ‘yancin kan...
    Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty ya tattauna da takwaransa na Tunisiya Mohamed Ali Nafti kan batutuwa da dama da suka shafi yankin gabas ta tsakiya a gefen taron majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a birnin Jeddah na kasar Saudiyya. Dangane da ci gaban da halin da ake ciki a Gaza, Abdel Aty ya gabatar da kokarin Masar tare da hadin gwiwar bangarorin shiyya da na kasa da kasa, na cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta ba da tabbacin sako mutanen da aka yi garkuwa da su da fursunoni da kuma bude hanyar shigar da kayan agaji. Ya lura da matsaloli na  jin kai da suka biyo bayan manufofin Isra’ila na haifar...
    “Mun yi tattaunawar gaskiya, amma gwamnati tana yi mana wasa,” in ji shi. Ya ce an yi watsi da rahotanni masu muhimmanci, an kafa manufofin da ke cutar da ilimi, sannan an jefa malaman da suka yi ritaya mummunan hali. “Wannan gwamnati ta raina ilimi da malamai. Mun gaji,” in ji shi. Shugaban ASUU ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta ƙi ɗaukar mataki, za ta ɗauki alhakin duk wata matsala da za ta biyo baya. Ya kuma kira mambobin ASUU da su fito ƙwansu da kwarkwata wajen tarukan da za a gudanar a manyan jami’o’i a ranar Talata, 26 ga Agusta, 2025, yana mai cewa wannan shi ne mataki na farko da ƙungiyar za ta ɗauka don nuna rashin...
    Gwamnatin Kano ta musanta rahotannin da ke zarginta da karkatar da Naira biliyan 6.5 daga baitul-malin jihar, tana mai cewa labarin “ƙarya ne da ‘yan adawa suka kitsa domin ɓata mata suna.” Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin. PDP ta miƙa wa kudancin Najeriya takarar shugaban ƙasa a 2027 PDP ta tabbatar da Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa Sanarwar ta ce labarin da aka wallafa a wani shafin yanar gizo a ranar 22 ga watan Agusta, wani yunƙuri ne na ɓata sunan gwamnatin da kuma lalata martabar jami’anta kafin Zaɓen 2027. Sanarwar ta ce taƙaddamar wadda a yanzu haka tana gaban kotu ta...
    Amma, a cikin wata sanarwa mai kakkausar murya da ya fitar a ranar Litinin, Daraktan Yada Labarai na Gidan Gwamnati, Sanusi Bature DawakinTofa, ya karya rahoton da cewa “aiki ne na tatsuniyoyi, wadanda abokan hamayyar siyasa suka shirya su, domin bata wa gwamnati suna don su samu madafun iko gabanin zaben 2027.   “Kowane tsabar kudi da ke fita a cikin Ma’aikatun gwamnati a tsare suke yadda ya kamata a cikin kundin kasafin kudi na jihar. Don haka, babu wani mutum a cikin gwamnati da ke kula da kudaden jama’a ba tare da wata manufa ta musamman ba,” in ji sanarwar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
    Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar adawa ta PDP ya tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa. Wannan dai na zuwa ne a yayin zaman NEC na 102 da ke gudana a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja. A jawabinsa na karɓar shugabanci, Damagum ya gode wa sauran mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) bisa taimako da haɗin kai da suka ba shi wajen gudanar da aikinsa. Ya kuma gode wa mambobin NEC bisa yabawa da amincewa da ƙoƙarinsa wajen farfaɗo da jam’iyyar, abin da ya ce hakan ya taimaka wajen tabbatar da shi a matsayin shugaban jam’iyyar.
    Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta keɓe wa kudancin Nijeriya tikitin takarar kujerar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027. Jam’iyyar ta tabbatar da haka ne a babban taron Kwamitin Zartarwa karo na 102 da ta gudanar ranar Litinin a Abuja. PDP ta tabbatar da Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa Wata mata ta mayar da N4.8m da aka yi kuskuren tura wa asusunta a Maiduguri A baya-bayan nan dai wasu masu ruwa da tsaki kan sha’anin siyasa sun zafafa kiraye-kiraye ga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi wa jam’iyyar takara a Zaɓen 2027. A yayin taron na yau ne kuma PDP ta tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa a hukumance. Damagum wanda ya shafe fiye da...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya godewa kasar Rasha saboda goyon bayanta ga kasar kan hakkinta na tace makamashin uranium, musamman a taron kwamitin tsaron MDD wanda za’a gudanar nan gaba dangane da kudurin kwamatin mai lamba 2231 dangane shirin nukiyar kasar Iran ta JCPOA, Inda kasashen turai 3 wato triko wadanda suke bukatar sake dawoda takunkuman MDD kan kasar ta Iran. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakato Pezeshkiyan yana fadar haka a lokacinda yake magana ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimir Putun a yau litinin. A nashi bangaren shugaba Putin ya bayyana cewa Rasha za ta tabbatar da cewa sakamakon taron kwamitin tsaro dangane da shirin “snapback” zai fito mai kyau ga kasar Iran....
    Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar adawa ta PDP ya tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa. Wannan dai na zuwa ne a yayin zaman NEC na 102 da ke gudana a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja. A jawabinsa na karɓar shugabanci, Damagum ya gode wa sauran mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) bisa taimako da haɗin kai da suka ba shi wajen gudanar da aikinsa. Ya kuma gode wa mambobin NEC bisa yabawa da amincewa da ƙoƙarinsa wajen farfaɗo da jam’iyyar, abin da ya ce hakan ya taimaka wajen tabbatar da shi a matsayin shugaban jam’iyyar.
      Ya kuma yi gargadin cewa, “Wannan ba lokaci ba ne da Arewa za ta naɗe hannunta tana kallo yayin da al’amura ke ci gaba da taɓarɓarewa, lamarin tsaro yana kara ta’azzara yayin da ake ci gaba da kwashe albarkatun yankin, ambaliyar ruwa na ci gaba da barazana, dole ne mu tashi tsaye mu hada kai domin kare yankin.”   Osuman ya koka da kashe-kashen da ake yi a Arewacin Nijeriya a kullum, yana mai jaddada cewa, babu yadda za a yi, a zura ido ana kallo.   “Mun yi asarar yara, matasa maza da mata, da tsoffi saboda ambaliyar ruwa, bala’o’i, ‘yan bindiga da masu kwacen wayoyi, halin da ake ciki, akwai matukar damuwa, don haka nake kira da...
    Wata mata mai aikin shara da goge-goge, Fa’iza Abdulkadir, ta mayar da kuɗi har N4.8m da aka yi kuskuren tura wa asusun bankinta a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Da take zantawa da News Central a Maiduguri, Fa’iza wadda take ɗaukan albashin Naira dubu 30 duk wata ta ce ta yanke shawarar mayar da kuɗin ne saboda tsoron Allah. An yaudari ’yan Nijeriya da suka hana Jonathan lashe Zaɓen 2015 — Ƙungiya Za a yi amfani da Hausa wajen samar da zaman lafiya — Abdulbaqi Jari “Wannan kuɗi ba haƙƙi na ba ne, ba ni na mallaki kuɗin ba, shi ya sa na mayar. Na fi son na zauna cikin kwanciyar hankali da kuma gudun azabar Allah a ranar lahira,”...
    Wata ƙungiyar siyasa da ke goyon bayan masu fafutikar nan ta “Bring Back Our Goodluck” ta buƙaci tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, da ya tsaya takara a Zaɓen 2027. Ƙungiyar ta ce a Zaɓen 2015 an yaudari ‘yan Najeriya da suka dage wajen ganin bai yi nasara ba a ƙoƙarinsa na neman wa’adi na biyu, lamarin da yanzu kowa yake nadama saboda an jefa ƙasar cikin tsanani da tsadar rayuwa da rashin tsaro. Za a yi amfani da Hausa wajen samar da zaman lafiya — Abdulbaqi Jari Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 35 a iyakar Najeriya da Kamaru A yayin wani taro na Arewa maso Yamma da aka gudanar ranar Lahadi a Kano, madugun ƙungiyar na ƙasa, Dokra...
    Za a yi amfani da harshen Hausa a matsayin hanyar samar da zaman lafiya a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na goma (10), wanda za a gudanar a Daura da ke Jihar Katsina, a ranar Talata, 26 ga watan Agusta, 2025. Jagoran taron, Abdulbaqi Aliyu Jari, wanda shi ne ya ƙirƙiri wannan rana, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Katsina. Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 35 a iyakar Najeriya da Kamaru Jami’an tsaro sun tsare jagoran Falasdinawa mazauna Najeriya Ya ce dukkan shirye-shirye sun kammala, kuma manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya tuni sun fara isowa domin halartar bikin. Jari ya ce an tsara taron ne domin baje kolin al’adun Hausawa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’adda kimanin 35 da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP ne a kusa da iyakar Najeriya da Kamaru. ’Yan ta’addan sun taru a yankin Kumshe, wani gari da ke kan iyaka a Jihar Borno, da safiyar Asabar domin kai hari kan sansanin sojoji da ke yankin. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa bayan samun bayanan sirri, sojojin kasa sun nemi taimakon rundunar sojin sama, inda jiragen yaki suka kai hare-hare a wuraren da aka gano ’yan ta’addan sun taru. “Ranar Asabar, 23 ga Agusta, sojojin runduna ta 21 sun dakile wani hari da ’yan ta’adda suka kai da daddare, inda jiragen yaki suka ragargaza ’yan ta’addan,” in ji wata majiya. Binciken bayan harin ya nuna cewa an...
    ’Yan Arewa a Kasuwar Alaba Rago, shahararriyar kasuwar ’yan Arewa a Jihar Legas sun roki gwamnatin jihar ta biya su diyya kan asarar da suka yi sakamakon rushe kasuwar da gwamnati nta yi. Sun bayyana cewa asarar da suka tafka ta haura Naira biliyan 20 bayan Gwamnatin Legas ta rusa masallatai sama da 40 da shaguna kimanin 3,000 a Kasuwar wadda suka kafa shekara 45 da suka gabata a jihar. A karo na biyu a ’yan kwanakin nan mahukunta a Jihar Legas suka rushe sassa da dama na kasuwar, wadda ta yi fice da kasuwancin kayan abinci da dabbobi da karafa da sauran kayan masarufi, wacce Hausawa suka kafa a shekarar 1979. A cikin watan Mayun 2024, jami’an hukumar ’yan...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Hadin kan al’umma, jami’ai, da sojojin da ke dauke da makamai, jan layi ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Bayan da makiya suka kasa murkushe al’ummar Iran ta hanyar yaki, a halin yanzu suna neman cimma manufarsu ta hanyar haifar da sabani da rarrabuwar kawuna. Ya ce: “Dukkan jama’a, jami’ai, marubuta, da jaridu, dole ne su kare tare da karfafa garkuwar karfe na hadin kan kasa mai tsarki da dukkan karfinsu.” Jagoran ya jaddada bukatar tallafa wa masu yi wa kasa hidima, musamman ma shugaban kasar wanda ya bayyana a matsayin mai jajircewa da kuzari, yana mai jaddada cewa hadin kan al’umma, gwamnati,...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Gudanar da hidima wa mutane aikin kowa ne Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa yi wa al’umma hidima aiki ne na kowa da kowa, yana mai bayanin cewa hadin kai da fahimtar juna kan kasa suna samun nasarar gudanar da mulki da tsayin daka wajen tunkarar makiya. A yayin jawabin da ya gabatar a wajen bikin sabunta mubaya’ar Imam Khumaini (r.a) a hubbarensa mai tsarki da ke birnin Tehran, shugaban kasar Masar Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: “Aikin hadin kan jama’ar kasa ne yi wa al’umma hidima da nuna musu kauna, idan har za a iya tabbatar da adalci a cikin halayen al’umma, za a yi nasara wajen hidimtawa al’umma, kuma dukkan...
    Kwamandan sojojin Iran ya yi barazanar mayar da martani mai muni da zai haifar da nadama ga makiya Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya jaddada cewa: Sojojin kasar Iran da jarumtarsu suna tsayawa da dukkan karfinsu wajen fuskantar barazanar makiya. A yayin ziyarar da ya kai Jami’ar Kimiyyar Sojin Ruwa ta Imam Khumaini (RA) da ke tashar jiragen ruwa ta Noshahr ta arewacin kasar Iran a jiya Lahadi, Manjo Janar Hatami ya bayyana cewa: “A yau Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da matsayi na musamman a tsakanin kasashen yankin, ya kamata makiya su sani cewa al’ummar kasar na kwarai a cikin sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye suke, kamar yadda suka saba a baya, da...
    Kafofin yada labarai na yahudawan sahayoniyya sun yarda da gazawar dakile Yemen daga ci gaba da ayyukan soji kan Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, wadanda tashar 12 da tashar ta 13 ke wakilta, sun amince da cewa: Hare-haren da makiya ke kaiwa kasar Yemen, ya gaza hana sojojin Yemen harba makamai masu linzami zuwa yankunan Isra’ila da aka mamaye. Waɗannan tashoshi na yahudawan sahayoniyya sun yi imani cewa; Da’awar iya dakile hare-haren sojojin Yemen kan yankunan Isra’ila, rudu ne kawai na jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila ganin tsawon lokacin da   za a iya dauka domin hana kai waɗannan ayyuka saboda “haɗarinsu.” Tashar talabijin ta yahudawa ta 13 ta yarda cewa harin na baya-bayan nan da aka kai kan kasar Yemen ba...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya shekara arbain zuwa sama ya san irin tarbiyyan da ya samo daga wurin iyayen sa a da baya can, irin mu’amalan dake tsakanin sa da iyaye har ma da shakuwan dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye.   A yanzu kuwa abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincabe sukayi wa iyaye yawa. Daya daga cikin manyan sauyin da aka samu sun hada da aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda hakan a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawan da ‘ya’ya suke samu. NAJERIYA A YAU: Ayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su a nan gaba...
    A nasa ɓangaren, Farfesa Usman Yusuf Bugaje ya gargadi gwamnati cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, matsalar za ta iya bazuwa zuwa manyan birane a jihar. A ƙoƙarin gwamnati, rundunar sojin Nijeriya ta sanar da shirin kafa sabuwar bataliya a ƙaramar hukumar Malumfashi domin ƙarfafa yaƙi da tashe-tashen hankulan ƴan bindiga a jihar Katsina. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Isra’ila ta kaddamar da wani farmaki ta sama a kan babban birnin kasar Yemen Sanaa a jiya Lahadi, inda ta kai hare-hare a yankin kudu maso gabashin birnin San’a. Wakilin tashar Almayadeen ya bayyana cewa, Isra’ila ta kai harin ne kan wani gidan mai  a kudu maso gabashin birnin San’a mallakin kamfanin mai na kasar Yemen da ke kan titin Al-Sitteen, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane  tare da jikkata wasu da dama a lokacin da suke shan mai a motocinsu da sauran ababen hawa a wurin. Kamfanin mai na kasar Yemen ya kuma tabbatar da cewa al’amura sun daidaita an kuma shawo kan gobarar da ta tashi a wurin, tare da kwantar da hankalin ‘yan kasar, kamar yadda wakilin...
    Gwamnatin Jihar Kano ta yi shiru yayin da wasu ƙungiyoyin farar hula suka buƙaci ta dakatar da manyan jami’abta da ake zargi da almundahana ta biliyoyin naira tare da gurfanar da su a gaban kotu. Wani rahoto na kafar yaɗa labarai ta Daily Nigerian ya bayyana cewa hukumomin ICPC da EFCC masu ya ki da almundahana sun gano badaƙalar Naira biliyan 6.5 da ake zargin Abdullahi Ibrahim Rogo, Darakta Janar na Al’amuran Kula da Baƙi a Fadar Gwamnatin Kano. Takardun da kafar ta ambato cewa ta samu suna zargin almundahanar ta faru ne tsakanin watan Nuwambar 2023 da Fabrairun 2025 ta hanyar kwangilolin bogi da sunan kamfanonin H&M Construction Nigeria Ltd, A.Y. Maikifi Petroleum da Ammas Oil & Gas Ltd....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau ne babbar jam’iyyar adawa ta PDP za ta gudanar da zama na 102 na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC), inda ake sa ran ta yanke hukunci kan wasu jiga-jiganta da ake zargi da cin dunduniyarta, ciki har da Ministan Abuja Nyesom Wike da tsohon Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom. Majiyoyi a jam’iyyar sun ce a yayin taron, za a gabatar da rahoton kwamitin ladabtarwa ƙarƙashin jagorancin Tom Ikimi, wanda ya ba da shawarar ɗaukar mataki a kan waɗanda ake zargi da yi wa jam’iyyar zangon ƙasa. Har ila yau, taron zai tattauna shirin gudanar da babban taron jam’iyya na ƙasa a Ibadan a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba, inda za a zaɓi sababbin shugabanni. Kazalika rahoton...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar 27 ga watan nan na Agusta, za a bude cibiyar tattarawa da watsa labarai game da bukukuwan cika shekaru 80 da samun nasara a yakin turje wa harin Japan da karshen yakin duniya na II.   Cibiyar wadda take hotel na Beijing Media Center, za ta bayar da shaidar watsa labarai da shirya damarmakin hirararki ga ‘yan jarida na kasar Sin da na ketare. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Matasa da dama a garin Kafanchan, da ke Ƙaramar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, sun yi aikin gayya domin gyara hanyar garin. Sun yi amfani da gatari, fatanya, diga da sauran kayan aiki wajen yi wa hanyar gyara. Ɗaliba ta haɗu da ajalinta a hatsarin mota a Yobe Japan za ta bai wa Najeriya rancen $190m don inganta wutar lantarki Aikin ya haɗa da haƙa da faɗaɗa magudanan ruwa don kaucewa ambaliya da kuma hana hanyar ƙara lalacewa. Shugaban ƙungiyar Kafanchan Youth Forum, Injiniya Sa’adu Bako, ya ce sun yi aikin ne domin rage wahalar da jama’a ke sha, musamman wajen zuwa jana’iza, musamman a lokacin damina. Ya kuma yi kira ga gwamnati ta gyara hanyar, kasancewar ba maƙabarta kaɗai...
    Ɗariƙar Tijjaniyya a Jihar Gombe, ta yi babban rashi bayan rasuwar ɗaya daga cikin fitattun malamanta, Sheikh Umar Bojude. Sheikh Bojude shi ne babban limamin Masallacin Juma’a na Alhaji Gidado Dalibi Yahaya (AG Dalibi). Japan za ta bai wa Najeriya rancen $190m don inganta wutar lantarki Rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC a Gombe Malamin ya rasu a ranar Lahadi, kuma an yi jana’izarsa a unguwar Jan Kai da misalin ƙarfe 5 na yamma. Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ta bakin Daraktan Yaɗa Labaransa, Isma’ila Uba Misilli. Ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga ɗariƙar Tijjaniyya, iyalansa da kuma al’ummar jihar. “Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalan marigayi, ɗariƙar Tijjaniyya, Fityanul Islam...
    Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa Najeriya za ta karɓi rancen dala miliyan 190 daga Ƙasar Japan domin inganta wutar lantarki. Wannan na cikin wata sanarwa da ma’aikatar lantarki, yayin da ake gudanar fa taron ƙasashen Afirka da ke gudana a birnin Yokohama na Ƙasar Japan. Mutum 6 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Sakkwato An harbe masu garkuwa da mutane 3 a Kebbi Tawagar Najeriya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu ta halarci taron. Rancen zai fito ne daga hukumar Japan International Cooperation Agency (JICA), kuma ana sa ran zai taimaka wajen samar da wutar lantarki mai ɗorewa a yankunan da ba su da isasshiyar wuta. Ma’aikatar ta kuma ce wannan lamuni ya zo ne a matsayin ƙari...
    Jam’iyyar ADC a Jihar Gombe, ta sanar da korar tsohon ɗan takarar gwamnanta na shekarar 2015, Nafiu Bala, bisa zargin yi mata zagon ƙasa. Shugaban ADC na jihar, Auwal Abba Barde, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudana a Gombe. An harbe masu garkuwa da mutane 3 a Kebbi Mutum 6 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Sakkwato A cewarsa, kwamitin ladabtarwa na unguwar Nasarawo ya binciki Bala, inda ya same shi da laifukan cin amanar jam’iyyar wanda hakan ya saɓa wa dokokinta. Ya ce an gayyaci Bala domin ya kare kansa a gaban kwamitin amma ya ƙi bayyana. Barde ya ƙara da cewa kwamitin zartarwa na jihar, ya tabbatar da wannan hukunci,...
    ’Yan sanda sun samu nasarar kashe wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da ƙwato bindigar AK-47 bayan musayar wuta da su a yankin Shanga na Jihar Kebbi. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya fitar. Mutum 6 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Sakkwato An tsinci gawar saurayi a gefen kudiddifi a Kalaba Sanarwar ta bayyana cewa lokacin da lamarin ya faru, DPO na Shanga ya gaggauta haɗa jami’an ‘yan sanda da ‘yan sa-kai waɗanda suka fafata da ‘yan bindigar, inda aka kashe uku daga cikinsu, sauran kuma suka tsere cikin daji. Kakakin ’yan sandan ya ce wannan nasara na da nasaba da...
    Aƙalla mutane shida sun rasa rayukansu, yayin da har yanzu an nemi wasu uku an rasa, sakamakon kifewar kwale-kwale a Garin Faji na Ƙaramar Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne lokacin da mazauna yankin ke tsere wa wani harin ‘yan bindiga da misalin ƙarfe 5:30 na safiyar Alhamis, 21 ga watan Agusta. An tsinci gawar saurayi a gefen kudiddifi a Kalaba Sarkin Musulmi ya ayyana Litinin 1 ga watan Rabi’ul Awwal Wannan shi ne karo na biyu cikin kasa da mako guda da irin wannan ibtila’i ya faru, domin a kwanaki shida da suka gabata, mutane huɗu sun mutu a hatsarin kwale-kwale makamancin wannan a Ƙaramar Hukumar Goronyo ta jihar. Aminiya ta ruwaito cewa, waɗanda...
    An tsinci gawar wani saurayi mai suna Daniel Ekanen, mai kimanin shekaru 18, a gefen wani kudiddifi da ke unguwar Ikot Effanga a Ƙaramar Hukumar Kalaba, Jihar Kuros Riba. Lamarin ya jefa firgici a zukata da kuma zaman dar-dar a cikin mazauna yankin, inda aka ruwaito cewa an kawo marigayin ne wurin dangin mahaifinsa daga ƙauyen Ikot Offiong da ke ƙaramar hukumar Odukpani a jihar. Sarkin Musulmi ya ayyana Litinin 1 ga watan Rabi’ul Awwal Dangote ya ci gaba da zama attajiri mafi arziƙi a Afirka — Forbes Rahotanni sun nuna cewa ana zargin masu tsafi da sassan jikin ɗan adam ne suka yi kisan, domin kuwa an yanke kansa kafin a jefar da gawarsa a gefen kudiddifin. Wani daga...
    Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya tabbatar da cewa gobe Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025, ita ce za ta zama 1 ga watan Rabi’ul Awwal, 1447 bayan hijira. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin shugaban kwamitin kula da harkokin addini a majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda ya bayyana cewa ba a samu labarin ganin sabon wata na Rabi’ul Awwal a ranar Asabar, 29 ga Safar ba. Dangote ya ci gaba da zama attajiri mafi arziƙi a Afirka — Forbes An haramta bukukuwan aure a Taraba Farfesa Sambo wanda kuma shi ne Wazirin Sakkwato, ya ce saboda haka, Lahadi, 24 ga watan Agustan 2025, za ta zama 30 ga watan Safar, sannan kuma bisa...
    Fitaccen attajirin nan, Aliko Dangote ya ci gaba da riƙe kambinsa na mutum mafi arziƙi a nahiyar Afirka, inda dukiyarsa ta kai dala biliyan $24.4, a cewar sabuwar ƙididdigar da mujallar Forbes ta fitar a bana. Wannan ya sanya shi zama mutum na 88 a jerin masu kuɗin duniya, inda ya rike wannan matsayi da tazara mai nisa a kan sauran attajiran Najeriya. An kama matashi kan zargin kashe matar ɗan uwansa mai juna biyu An haramta bukukuwan aure a Taraba Abdulsamad Rabiu wanda ya mallaki rukunin kamfanin BUA, shi ne ya biyo bayansa da dukiyar da ta kai dala biliyan $7.2, wanda ya sa shi zama attajiri na 516 a duniya. Sai kuma Mike Adenuga da dukiya mai darajar...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara, ta kama wani matashi mai shekara 29, Sylvester Enemo, bisa zargin kashe matar ɗan uwansa, Misis Esther Enemo, wacce ke ɗauke da juna biyu a Ilorin. An samu gawar Esther mai shekara 39 a yankin Temidire Zone 4, a bayan gidanta cikin daji, an yayyanka jikinta. An haramta bukukuwan aure a Taraba NDLEA ta kama matashi da wiwi ta miliyan 10 a Kano An gano wasu sassan jikinta a cikin wani buhu da aka jefar a ƙarƙashin gada, sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a ga kanta ba. Shaidu sun ce an ga Sylvester da safiyar ranar Alhamis ya fita daga gidan da leda baƙa kuma da jini a jikinta. Maƙwabta, sun...
    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Kano ta bayyana cewa akwai katin zaɓe na dindindin (PVC) sama da dubu 367,000 da jama’a ba su karɓa ba har yanzu a jihar. Kwamishinan INEC na Kano, Ambasada Abdu Zango, ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi tawagar kwamitin gwamnatin jihar kan rajistar katin zaɓe ƙarƙashin jagorancin kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya. Ya yabawa matakin kafa kwamitin tare da kira ga mambobinsa da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a domin su tafi su karɓi katin zaɓensu. Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas 2027: ‘Yan Siyasa Sun Yi Watsi Da Gargadin INEC, Sun Ci Gaba...
    Yakasai ya kawo misalin tattaunawa da aka yi da kamfanoni a kasar China lokacin gwamnatin Abdullahi Ganduje, inda aka kawo tawaga Kano don duba yiyuwar saka hannun jari amma rashin wutar lantarki ya kawo cikas, ganin cewa dokar gwamnatin tarayya a wancan lokaci ta hana jihohi samar da wutar lantarki ta kansu. Ya bayyana roƙo ga gwamnatin Kano ta yanzu da ta mayar da hankali wajen tabbatar da isasshiyar wutar lantarki, musamman ta hanyar wutar solar ko haɗin gwuiwa da manyan kamfanoni kamar Dangote da BlackRhino, don farfado da masana’antun jihar. A cewar Yakasai, damuwa mafi girma ita ce yadda albarkatun Arewa ake dauka zuwa wasu jihohin kudu don a sarrafa, daga bisani kuma a dawo da su a sayar...
    Sanarwar ta kara da cewa, “Da isar rundunar, ta fara artabu da ‘yan bindigar, inda ta samu nasarar kashe Uku, tare da kwato bindiga kirar AK-47,” in ji sanarwar.   Kwamishinan ‘yansandan jihar Kebbi, CP Bello M. Sani ya yabawa babban jami’in da jami’ansa bisa wannan namijin kokarin da suka yi. Ya bayyana nasarar a matsayin shaida na kudurin rundunar na kawar da masu aikata munanan laifuka a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Taron na Gusau, ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya kuma tattauna kan halin da ƙasar ke ciki, matsalolin tsaro, raguwar darajar Dimokraɗiyya, da shirye-shiryen babban taron PDP mai zuwa.   Gwamnonin sun buƙaci mambobin ƙungiyar da su kaurace wa yunƙurin kawo cikas ga taron, inda suka bayyana jam’iyyar PDP a matsayin hanya ɗaya tilo wajen saita Dimokraɗiyya, kuma za ta iya maido da Nijeriya kan turbar shugabanci na-gari da ci gaba.   “Zauren ya sake tabbatar da cikakken ƙudurin da aka yi na taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 101 na Yuli 2025 dangane da babban taron ƙasa na ranar 15 ga Nuwamba.   “Muna kira ga mambobin ƙungiyar da su bijire wa duk wani yunƙuri...
    Wasu majiyoyi na kusa da Putin dai sun bayyana cewar, ya na fatan ganawar da za su yi ta gaba da Zelensky da Trump zai jagoranta ta kasance a Mo scow.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Fluminense Fabio a ranar Talata ya zama mutum na farko a tarihin wasan kwallon kafa na maza da ya buga yawan wasanni a tarihi, lokacin da dan Brazil din ya buga wasa karo na 1,391. Dan wasan mai shekaru 44 a ranar Asabar ya yi daidai da tarihin da tsohon dan wasan Ingila Peter Shilton ya rike na wannan adadin ya samu wannan nasarar a wasan da suka doke America de Cali da ci 2-0 a filin Maracana dake Rio de Janeiro. Kafofin yada labaran Fluminense da na Brazil sun ce a yanzu Fabio ya kasance shi kadai a tarihin kwallon kafa, duk da cewa FIFA ko hukumar CONMEBOL ba ta bayyana hakan...
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Sayyid Aliyul Khaminae, yace mafarkin da gwamnatin Amurka take yi na JMI ta yi biyayya a gareta, abu ne wanda ba zai taba faruwa ba. Ya kuma yi gargadi ga mutanen kasar su yi hattara da kokarin raba kansu. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Imam Khaminae yana fadar haka a safiyar yau Lahadi a jawabin da ya gabatar a wani taro a cikin Hussainiyyar Imam Khomani (q) dake nan Tehran. Labarin ya kara da cewa Jagoran ya gabatar da jawabin ne, a ranar shahadar Limami na 8 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), wato Imam Aliyu dan Musa Arridah (a). Labarin ya kara...
    Dakarun kare juyin juya halain Musulunci a nan Iran sun nuna goyon bayansu ga gwamnatin JMI, sun kuma yaba da ayyukan da gwamnatinn take yi na kawo ci gaban kasar. Tashar talabijian ta Prestv a nan Tehran ta nakalto dakarun na IRGC na bayyana haka a wani rahoton da suka fitar wanda yayi dai dai da Makon gwamnati a nan Iran. Sun kuma kara da cewa jami’an tsaron kasar suna goyon bayan hadin kan da ke tsakanin bangarorin gwamnati daban daban, da jami’an tsaron kasar. Rahoton yace duk tare da matsalolin da kasar take fama da makiya a waje da cikin kasar amma kasar tana ci gaba, mutane da gwamnati da kuma jami’an tsaron kasar suna aiki tare don ganin...
    A yayin zaman majalisar dokokin jihar Katsina, Babban Mai Tsawatarwa na majalisar, Hon. Ibrahim Umar Dikko, ya fashe da kuka a gaban takwarorinsa, yana bayyana yadda ’yan bindiga suka mamaye mafi yawan yankunan da ke cikin Ƙaramar Hukumar Matazu da yake wakilta. Hon. Dikko ya bayyana cewa daga cikin gundumomi 10 da ke cikin Matazu, guda 8 sun faɗa hannun ’yan bindiga, inda ya ce manoma ba sa iya zuwa gonakinsu saboda tsoron harin da ake kai musu. “A jiya da safe, a bakin garin kusa da makarantar sakandare, sun kashe wani matashi sannan suka sace shanu hudu da ake amfani da su wajen noma,” in ji shi cikin hawaye. Ya kara da cewa a cikin kwanaki biyu da suka...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Armenia ta yi alkawalin cewa babu wani sojojin Amurka da zai shiga yankin kaukas ta kudu kusa da kanika da kasar Iran. Musamman ta san cewa Iran bata son haka hakama kasar Rasha. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Arachi yana fadar haka, bayan tattaunawa da jami’an gwamnatin Armenia a lokacin da shugaban Iran masoud Pezeshkiyan ya kai ziyarar kasar ta Armenia. Kafin haka dai a makon da ya gabata ne shuga Trump a fadar “White House” ya gana da shuwagabannin kasashen Armenia da Azerbaijan inda suka rattaba hannu a kan yarjeniyar sulhu a tsakanin kasashen biyu, tare da amincewar Armenia ta bawa Azerbaijan damar...
    Jakadann Amurka na musamman a kasar Lebanon Tom Barrack ya bayyana cewa ya yarda da matakan da gwamnatin kasar Lebanon take dauka don kwance damarar kungiyar Hizbulla ta kasar, Shafin yanar gizo na Alarabia na kasar Saudiya ya bayyana cewa Barrack ya shaidawa gwamnatin kasar Lebanon kan cewa yana kirin kungiyar Hizbullah da kuma kasar Iran wadanda dukkaninsu mabiya mazhabar shia ne da sun a cewa su yi aiki da gwamnatin kasar don sasantawa. Kafin haka dai a ranar 7 ga watan Augusta da muke ciki ne gwamnatin kasar Lebanon ta yanke shawarar kwance damarar kungiyar Hizbullah, sannan ta bawa sojojin kasar umurnin wannan aikin. Kuma ta bawa sojojin kan cewa su kammala wannan aikin zuwa watan satumma mai zuwa....
    Gwamnatocin kasashen Iran da Pakisatan sun amince su ninninka yawan kayakin noma na kasuwanci a tsakaninsu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto minitan noma na kasar Iran Jihad Gholam reza Nouri yaqna fadar haka a jiya litinin ya kuma kara da cewa kasashen biyu zasu karfafa harkokin siyasa da kuma tattalin arziki tsakaninsu, inda suke son ya kai dalar Amurka billiyon $3 daga biliyon $1.4 da yake a halin yanzu. Ya ce suna saran zsu kai wannan adadin a cikin shekaru biyu masu zuwa. Nouri ya bayyana haka ne bayan ya gana da Rana Tanveer Hussain  Na ma’aikatar cibiyar binciken na ayyukan noma na kasar Pakisatan a nan birnin Tehran. Ya ce idan wannan shirin ya kankankama...
    A yau ake gurfanar da wani majinyaci mai shekaru 40, zai gurfana a kotu, bisa zargin cin zarafin wata likita mai suna Fatima Umar Gamsa a asibitin Ƙwararru na tunawa da marigayi Janar Sani Abatch da ke Damaturu Jihar Yobe. Shugaban Ƙungiyar Likitocin Najeriya reshen Jihar Yobe, Dakta Umar Aji, ya ce kungiyar ta kai ƙara gaban ’yan sanda kuma tana jiran hukuncin da kotu za ta yanke. “A yanzu shari’ar tana gaban kotu, kuma ƙungiyar ba za ta ce komai ba har sai ta ji sakamakon hukuncin kotun,” Aji ya jaddada. Wanda ake zargin, Ahmed Usman mazaunin rukunin gidajen Abba Ibrahim da ke Damaturu an tsare shi  a gidan yari na Potiskum har zuwa lokacin da za a saurari...
    Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata haɗala a Cibiyar Fasahar Sufuri ta Kasa (NITT) da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Kano. Mataimakin Kwamandan Hukumar, Mujahid Aminudeen, ya ce mutane — maza 27 da mata 35, “A ranar Lahadi, jami’anmu tare da haɗin gwiwar NDLEA suka su su 62 a cibiyar horarwa ta NITT da ke Dawakin Kudu, bayan samun bayanan sirri daga wasu masu kishin ƙasa.” Ya ce mutanen sun yi amfani da saukar ruwan sama da ake samu lokaci-lokaci a yankin don aikata  baɗala. “Muna amfani da wannan dama don gargaɗi ga matasa masu aikata abubuwan batsa da su daina, ko su fuskanci hukuncin doka. Hisbah ba za ta zauna ba tare da daukar...
    Yara 2 sun mutu wasu 6 sun jikkata bayan tashin bom a yankin Ƙofa Biyu da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno. Shaidu a garin sun shaida wa wakilinmu cewa bom ɗin ya tashi ne bayan yaran sun kawo shi gida bisa rashin sani. Sun shaida wa wakilinmu cewa yaran sun kawo bam ɗin cikin gari ba tare da sanin hatsarinsa ba, suna ɗauka ƙarfe ne da za a sayar. Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 5 na yamma a ranar Lahadi. ’Yan bindiga sun yi hatsari bayan karbar kudin fansa An rage kuɗin wankin koda da kashi 76% a asibitocin tarayya NAJERIYA A...
    Aƙalla gidaje 70 ne suka ruguje wasu da dama suka lalace sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya haddasa ambaliya a Ƙaramar Hukumar Malam Madori ta Jihar Jigawa. Yankunan da ibtila’in ya shafa sun haɗa da Tonikutara, Gandun Sarki, Gandun Bundugoma da rukunin gidajen Shagari Quarters, bayan ruwan sama da aka kwashe sa’o’i da dama a ranar ya mamaye kwalbatoci da magudanan ruwa a yankin. Dan-Ummah Abba, wani magidanci da lamarin ya shafa a Gandun Sarki ya bayyana cewa gidansa da yake zaune a ciki sama da shekara 30 ya rushe a sakamakon lamarin. Daga nan ya roƙi Gwamnatin Jihar Jigawa da ta kawo musu ɗaukin gaggawa. NAJERIYA A YAU: Halin Da Muke Ciki Bayan Rasa ‘Yan Uwanmu A...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ‘Yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwa da ya faru a garin Kojiyo dake karamar hukumar Goronyo a jihar sakkwato sun samu kansu cikin damuwa.   Yayin da kalilan daga cikin wadanda abun ya rutsa dasu suka tsira da ransu, wasu da dama sun mutu, a gefe guda kuma an kasa gano inda sauran da abun ya rutsa dasu suke. Wannan lamari ya tayar da hankulan jama’a, musamman ‘yan uwan waɗanda abin ya shafa, waɗanda yanzu ke cikin damuwa, jimami da rashin sanin makoma. NAJERIYA A YAU: Dalilan Karyewar Farashin Hatsi A Kasuwanni DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya Shirin Najeriya  A Yau na wannan...
    Gwamnatin Tarayya ta rage farashin jinyar ciwon ƙoda daga kimanin N50,000 zuwa N12,000 a Asibitocin Tarayya — ragin da ya kai kashi 76 cikin 100. Wannan saukin farashi ya samu ne bayan amincewar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda mai ba shi shawara kan harkokin sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. Bwala ya ce hakan zai kawo saukin rayuwa ga dubban ’yan Najeriya da ke fama da cutar, wadda ke bukatar yin jinya sau da dama a kowane mako. “Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da tallafin tarihi domin rage farashin jinyar ciwon koda ga ’yan Najeriya. An rage farashin kowace wankin ƙoda daga N50,000 zuwa N12,000 kacal,...
    Allah Ya yi wa Alhaji Ahmed Momohsani Ododo, mahaifin Gwamna Ahmed Usman Ododo na Jihar Kogi, rasuwa yana da shekara 83 a duniya. Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya sanar da rasuwar a yammacin ranar Litinin, 18 ga Agusta, 2025. Gwamnatin jihar ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyalan Gwamna da kuma al’ummar jihar baki ɗaya. Sanarwar ta kara da cewa kafin rasuwarsa, Marigayi Alhaji Ododo ya kasance mutum mai daraja wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen gina halaye da dabi’un ɗansa, Gwamna Ahmed Usman Ododo. Ta kuma miƙa ta’aziyya ga Gwamna Ododo, iyalansa da dangin Ododo gaba ɗaya, tare da addu’ar Allah ya ba su ƙarfin juriya da haƙuri.
    Mutum 333 sun shiga hannu kan zargin aikata laifuka a yayin zaben cike gurbi da aka kammala a Jihar Kano. A ranar Asabar aka gudnar da zaben na cike gurbi a mazabun Majalisar Tarayya da akamaimaita a ranar Asabar a mazabar Ghari/Tsanyawa da kuma zaben cike gurbi na Bagwai/Shanono. Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya sanar da karuwar adadin mutanen daga 288 a ranar Litinin a hedikwatar rundunar da ke Kano. A cewarsa, zaben ya fuskanci barazana sakamakon “shigo da ’yan daba da dama daga cikin da wajen jihar” da suka yi yunkurin dagula tsarin zaben, amma an samu nasarar shawo kan lamarin ta hanyar haɗin gwiwar hukumomin tsaro.   ...
    Kawo yanzu an ceto mutum 26 ana ci gaba da neman wasu 25 bayan hatsarin kwalekwale a yankin Goron yo da ke Jihar Sakkwato.  Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta sanar da cewa irgin ruwan ya dauko mutane 51 tare da kayansu da babura kafin ya tuntsure. Babban Jami’in Kula da Ayyukkan na Hukumar, Aliyu Shehu ya bayyana cewa “Kokarin ceto mutanen na tafiya kuma mun sanar da garuruwa makwabta su taimaka a wajen bincikar mana mutanen a wurin da suke.” A lokacin da manema labarai suka tafi wurin dangin wadanda suka nutse, sun yi jungum don rashin tabbas ga ’yan uwansu. Ya soka wa budurwarsa wuka har lahira ’Yan bindiga sun yi hatsari bayan karbar kudin fansa Albashin...
    Wani mutum ya soka wa budurwarsa mai suna “Ima” wuka har lahira a unguwar Okereke Street da ke garin Fatalkwal na Jihar Ribas. Mutumin, wanda ake wa lakabi da “Doctor” ya daba wa budurwar tasa mai suna “Ima” wuka ne bisa zargin tana cin amanarsa. Lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi, wanda shaidu a unguwar suka ce ya samo asali ne daga zargin da Doctor ke yi wa Ima, wanda ya rikide zuwa tashin hankali. Mai kula da gidan da lamarin ya faru ya kai rahoto ofishin’yan sanda na Azikiwe Division, Mile 2 Diobu, wanda hakan ya kai ga cafke wanda ake zargi. ’Yan bindiga sun yi hatsari bayan karbar kudin fansa Mutane 62 da aka sace sun tsere...
    Wasu masu garkuwa da mutane sun yi hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa rabon kudin fansar mutanen da suka sace a Jihar Nasarawa. Jami’an tsaro sun kwato bindigogi uku da tsabar kudi Naira miliyan 6.9 daga motar ’yan bingidar bayan hatsarin motar a yankin Garaku, daura da wani shingen bincike na Jami’an Kula da Lafiyar Ababen Hawa (VIO) Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta ce ta kwato makamai masu haɗari da kuɗi sama da naira miliyan shida, bayan wani haɗari da ya faru a kusa da Angwan Mayo. ’Yan sanda daga yankin Garaku sun ce da misalin ƙarfe 9:08 na safe, suka samu kiran gaggawa dangane da haɗarin motar kirar Opel Vectra wadda shaidu suka ce mutane biyu da ke...
    Mutum 62 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su sama da wata guda sun tsere bayan rundunar soji ta kai farmakin sama da ƙasa a maboyar ’yan ta’adda a Karamar Hukumar ƊanMusa, Jihar Katsina. Farmakin da aka kai a ranar Asabar da misalin ƙarfe 5:10 na yamma ya gudana ne bisa sahihan bayanan leƙen asiri, inda dakarun sojin sama da na ƙasa suka haɗa kai wajen kai hari a kauyen Jigawa Sawai, wanda ke iyaka da Jihar Zamfara. A cewar sanarwar da Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Katsina ta fitar, farmakin ya tilasta ’yan bindigar guduwa, lamarin da ya ba wa mutanen da aka yi garkuwa da su damar tserewa cikin ruɗani. Wasu daga cikin waɗanda suka...
    Kungiyar M23 da ke dauke da makamai a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, ta yi watsi da tattaunawar zaman lafiya da gwamnatin kasar, tana mai cewa ba za ta koma tattaunawa ba, sai dai idan hukumomi sun cika sharuddan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a baya. Rikicin da aka gwabza tsakanin dakarun gwamnati da mayakan na M23 a watan Janairu ya kara kamari, yayin da kungiyar mai  dauke da makamai ta kwace iko da yankuna masu yawa a yankin gabashin kasar mai arzikin ma’adinai, kafin dukkan bangarorin biyu su cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a tattaunawar da aka yi a Qatar a watan da ya gabata, wanda ke da nufin share fagen samar da zaman lafiya mai dorewa. Kungiyar ta...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya barazana ce ga wanzuwar tsaron yankin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya suna wakiltar wata barazana ga wanzuwa tsaro da zaman lafiyar yankin da kuma kasashensu. Idan ba a dakile wannan barazanar ba, to babu shakka yankin zai fuskanci yake-yake marasa iyaka. A yayin taron manema labarai na mako-mako a ranar Litinin, Baqa’i ya yi ishara da zagayowar ranar 28 ga watan Mordad (19 ga Agusta, shekara ta 1953, yana mai cewa: Ba za a iya mantawa da wannan lamari mai zafi ba, juyin mulkin da ya hambarar da zababbiyar gwamnatin al’ummar Iran tare da hadin gwiwar Amurka da Birtaniya. Dangane da ci...