2025-06-15@21:30:04 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4785
«Gwamnatin Obasanjo»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Abdulazeez pleaded not guilty to the two-count charge. Abdulazeez ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da su biyu. Bayan rokon da ta yi, lauyan ICPC, Hamza Sani, ya bukaci kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Yuni, 2025, domin masu gabatar da kara su gabatar da shaidu. Sai dai daga baya kotun ta ba da ranar sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Yunin 2025 domin sauraron karar. Lauyan wanda ake tuhuma ya nemi a ba shi belin, wanda ICPC ba ta yi adawa da shi ba. Mai shari’a Iheabunke ya bayar da belinta a kan kudi naira miliyan 10, tare da mutane biyu da za su tsaya mata. Ya ce dole ne...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cikakken shirin Iran na tunkarar duk wani mataki na wuce gona da iri a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar barazanar daukar matakin soji kan kasar. Manjo Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne yau Alhamis, yayin da rahotanni ke nuni da cewa, Amurka ta sanya ofisoshin jakadancinta da sansanonin sojinta da ke yammacin Asiya cikin shirin ko-ta-kwana saboda fargabar yiwuwar kai wa Iran hari. “A wasu lokuta makiya suna yi mana barazana da daukar matakin soji, mun sha bayyanawa, kuma muna maimaitawa a yau, cewa mun shirya tsaf don fuskantar duk wani yanayi,” in ji shi. “Muna da kwarewa, mun karfafa karfinmu tare da samar...
Sadeeƙ Umar da ake yi wa laƙabi da Mane, matashin ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne da yake tashen taka leda a rukunin ’yan dagaji a Jihar Kano. Matashin, wanda tauraronsa ke haskawa a fagen tamola ya yi fice ne bayan da ya kafa wani sabon tarihi na zura ƙwallaye 10 a raga a wasanni 10 da ya buga tare da ba da taimako sau 6 wajen wasu ƙwallayen a rukuni gasar wasannin ’yan dagaji aji 1 da aka fi sani da Amateur 1 a Jihar Kano. An ciro gawarwaki sama da 200 daga jirgin Indiya da ya yi hatsari Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamna Zulum ya yi wa fursunoni 66 afuwa A cikin tattaunawarsa da Aminiya, Sadeeƙ Mane ya bayyana cewa, ƙwazo...
An sanar da tashin shi daga City kafin karshen kakar wasa ta bana, kuma De Bruyne ya yi bankwana da magoya baya a filin wasa na Etihad bayan wasansa na karshe a gida da suka buga da Bournemouth a watan Mayu, City ta yi kokarin cike gibin da De Bruyne ya bari, yayinda ta dauki yan wasan tsakiya Tijjani Reijnders daga AC Milan da Rayan Cherki daga Lyon. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Iran ta yi Allah-wadai da wani kuduri da ta danganta da na siyasa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta dauka, tana mai cewa ba shi da tushe na fasaha ko doka. Hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran (AEOI) da ma’aikatar harkokin wajen kasar sun fitar da sanarwar hadin gwiwa yau Alhamis bayan da majalisar gwamnonin hukumar ta IAEA suka amince da wani kuduri da ke zargin Iran da rashin cika alkawuran da ta dauka na nukiliya. Kuri’u 19 ne suka amince da kudurin wanda Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus suka tsara. Kasashen Rasha, China da Burkina Faso sun kada kuri’ar kin amincewa da shi, Yayin da kasashen Afirka ta Kudu, Indiya, Pakistan, Masar,...
A ranar dimokuraɗiyyar Najeriya ta 2025, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis, ya yi afuwa ga fursunoni 66 a babbar Cibiyar gyaran hali da ke Maiduguri. Ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a gidan yari a ranar 12 ga watan Yuni, 2025, ya yi amfani da ikon da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba wa gwamnonin jihohi, wanda ya ba da damar yin afuwa bayan ya tattauna da wata majalisar ba da shawara kan jinƙai. 12 ga Yuni: Najeriya na bikin ranar dimokuraɗiyya An hana hawa babur da daddare a fadin jihar Gombe “Dangane da ikon da aka bani a ƙarƙashin sashe na 212 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (wanda aka gyara)...
A yau Alhamis ne aka bude bikin baje kolin hada-hadar tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na hudu a birnin Changsha fadar mulkin lardin Hunan, taron dake kara jaddada himmar kasar Sin ta fuskar karfafa alaka da nahiyar Afirka, nahiyar dake da mafiya yawan kasashe masu tasowa a duniya baki daya. Kusan kamfanonin Sin da na kasashen Afirka 4,700, da sama da mahalarta 30,000 ne za su halarci bikin na kwanaki hudu, wanda aka yiwa taken “Sin da Afirka: Tunkarar zamanantarwa tare.” Rahotanni daga mashirya bikin na cewa, kwarya-kwaryar darajar ayyukan hadin gwiwa da aka amincewa sun haura dalar Amurka biliyan 11. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci bikin bude baje kolin, inda kuma...
A ranar dimokuraɗiyyar Najeriya ta 2025, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis, ya yi afuwa ga fursunoni 66 a babbar Cibiyar gyaran hali da ke Maiduguri. Ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a gidan yari a ranar 12 ga watan Yuni, 2025, ya yi amfani da ikon da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba wa gwamnonin jihohi, wanda ya ba da damar yin afuwa bayan ya tattauna da wata majalisar ba da shawara kan jinƙai. 12 ga Yuni: Najeriya na bikin ranar dimokuraɗiyya An hana hawa babur da daddare a fadin jihar Gombe “Dangane da ikon da aka bani a ƙarƙashin sashe na 212 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (wanda aka gyara)...
A yau ne Najeriya ke bikin ranar Dimokuraɗiyya, wanda masana siyasa a ciki da wajen ƙasar ke jinjina kan yadda aka kwashe shekara 26 kan tafarkin mulkin farar hula. Najeriya, ta kasance ƙasa mafi yawan al’umma a Nahiyar Afirka inda ake bikin murnar ranar dimokuraɗiyyar domin tunawa da zaɓen 12 ga watan Yuni wanda ake ganin shi ne zaɓe mafi inganci da aka taɓa gudanarwa a Najeriya. NAJERIYA A YAU: 12 Ga Yuni: Me Ranar Dimokuraɗiyya Ke Nufi Ga Talakan Najeriya? An kashe jaririn wata 9 da wasu 3 a Filato Hakan dai na zuwa ne duk kuwa da cewa an soke zaɓen, lamarin da ya haifar da taƙaddama da ruɗani game da zaɓen. Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da kutsawa cikin masallacin al-Aqsa da ministan Isra’ila Itamar Ben-Gvir ya yi a baya bayan nan, tana mai cewa tana da nufin tayar da “yakin addini” a wannan wuri mai tsarki. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce “Kutsen da Itamar Ben-Gvir, ya yi a cikin masallacin Al-Aqsa mai alfarma, da kuma ziyarar tsokanar da ya kai a harabar masallacin… rashin mutunta ra’ayin musulmi da kuma keta alfarma da matsayin masallacin Al-Aqsa a duniyar Musulunci.” Kungiyar ta jaddada cewa wannan wulakanci da aka yi yana nuna ” girman kai na wannan gwamnati mai tsattsauran ra’ayi da kuma dagewarta na rura wutar yakin addini.” Hamas ta kuma bukaci dukkanin...
Ministan yakin Isra’ila, Israel Katz, ya umarci sojojin kasar da su hana ayarin motocin agaji na arewacin Afirka shiga yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya. A cikin wata sanarwa ofishin Katz ya umarci sojojin Isra’ila da su hana “masu fafatuka daga Masar shiga yankin Zirin Gaza. Katz bukaci “Hukumomin Masar dasu hana zuwan masu fafatukar a kan iyakar Masar da Isra’ila.” Ministan ya ya bayyana hakan a matsayin hadari ga jami’an tsaron Isra’ila na IDF.” Wannan dai na zuwa ne bayan ayarin motoci 100 da ya kunshi dubban masu fafatuka daga kasashen Morocco, Aljeriya, Tunisia, Libya da Masar, suka yunkuri anniyar wayar da kan al’ummar duniya kan matsalar jin kai a Gaza, da neman kawo karshen yakin kisan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumomi a India sun ce da yiwa a samu wanda ya tsira daga hatsarin jirgin samanAir India da ya faru a yau Alhamis. Jirgin samfarin Boeing 787 Dreamliner wanda ya tashi Ahmedabad zuwa birnin Landan ya yi hatsari jim kadan bayan tashinsa dauke da fasinjoji 242 da ma’aikatan jirgin inji kamfanin air India. Bayanan farko da kamfanin na Indiya ya fitar sun ce akwai, Indiyawa 169, ‘yan Burtaniya 53 da, ‘yan Portugal 7 sai dan Canada guda a cikin jirgin. Kuma babu wanda ya tsira, a cewar shugaban ‘yan sandan Ahmedabad. Hukumomin India da na Ingila da Portigal duk sun jajanta game da mummunan hatsarin. Jami’an kashe gobara a arewa maso yammacin Indiya tun da farko sun shaidawa kamfanin dillancin...
A yayin da ake tsaka da bikin Ranar Dimokradiyya a Najeriya, al’ummar jihar Gombe sun wayi gari da sabuwar dokar takaita zirga-zirgar babura daga ƙarfe 7:00 na yamma zuwa ƙarfe 6:00 na safe a duk faɗin jihar. Sanarwar da ta fito ne daga hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta jihar, DSP Buhari Abdullahi, ranar Alhamis, a madadin kwamishinan ’yan sandan jihar Bello Yahaya. Sanarwar ta ce an kafa dokar ne don rage ayyukan ta’addanci a fadin jihar. Guguwa ta hallaka mutum 6, ta jikkata 30 a Taraba An kashe mutum 41 cikin mako ɗaya a Filato Kafa dokar na zuwa ne kwana uku bayan wasu matasa da ba a tantance su wane ne ba suka kashe...
A wani bayani na hadin gwiwa da hukumar makamashin Nukiliya ta Iran da kuma ma’aikatar harkokin wajen Iran su ka fitar, sun bayar da umarnin a bude wani wuri na daban na sirri domin ci gaba da tace sanadarin Urani’um, sannan kuma a maye gurbin bututu tace sanadarin mai mataki na daya, da mai mataki na shida a cibiyar “Pardo.” Bayanin dai ya zo ne a matsayin mayar da martani ga sanarwar da ta fito daga kwamitin alkalai na hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa akan Iran. Bugu da kari, bayanin na Iran ya kuma ce; A kodayaushe jamhuriyar musulunci ta Iran tana aiki da nauyin da ya rataya a wuyanta, kuma har ya zuwa yanzu babu wani rahoto...
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Manjo Janar Hussain Salami ya fada a yau Alhamis cewa; Abokan gaba suna yi mana barazana da yaki, sannan ya tabbatar da cewa a shirye suke su fuskanci duk abinda zai faru. Manjo janar Salami wanda ya gabatar da jawabi ga taron dakarun sa-kai na “Basiji a nan Tehran ya kuma kara da cewa; Babu wani wuri komai zurfi da nisansa a HKI da ba mu tsinkayowa, idan kuwa aka ba mu umarni to za su yi nasara, mu Sanya abokin gaba ya yi nadama. A gefe daya ministan tsaron Iran ya bayyana cewa; Duk wani hari da ake tunanin kawo wa Iran, to kuwa zai fuskanci mayar da martani mai...
Wata mummunar guguwa ta yi sanadin mutuwar mutum shida sannan ta jikkata wasu 30 a garin Garba-Chede da ke karamar hukumar Bali a jihar Taraba. A cewar wani mazaunin yankin wanda guguwar ta lalata wa gida mai suna Abubakar Dodo, an shafe shekaru masu yawa ba su ga irin ta ba a yankin saboda munin barnar da ta yi. Rashin wutar lantarki ya durƙusar da kasuwanci a Arewa Maso Gabas An kashe jaririn wata 9 da wasu 3 a Filato A cewarsa, ban da gidaje, guguwar ta kuma lalata makarantu da masallatai da coci-coci, sannan kayan abinci na miliyoyin Naira sun salwanta. Dagacin garin na Garba-Chede, Kaigama Maigandi, ya yi kira ga Gwamnan Jihar, Agbu Kefas, da ya taimaka wa...
Hukumar dake kula da ‘yan hijira dake karkashin MDD ta sanar da cewa, mutanen yake-yake da rikice-su ka tilastawa yin hijira a duniya ya kai miliyan 122. A yau Alhamis ne dai hukumar dake kula da ‘yan hijirar ta bayyana haka, tana kai kara da cewa; gajiyawar da aka yi na warware fadace-fadace da rikicen da suke faruwa a duniya ne su ka kara yawan ‘yan hijirar, daga ciki har da kasashen Sudan da kuma Ukiraniya. Haka nan kuma ta ce; Tun daga 2015 ne ake samun koma baya na kudaden da ya kamata a rika bayarwa domin taimakawa ‘yan hijira. Shugaban hukumar ‘yan hijirar ta MDD Filippo Grandi wanda ya gabatar da rahoto akan halin da ake ciki, ya...
Jami’in tafiyar da sha’anin Mulki a yankin Cape ya fada a jiya Laraba cewa; An sami karuwar wadanda su ka rasa rayukansu ya karu zuwa 49. Shugaban tafiyar da sha’anin Mulki a yankin na garin Cape, Oscar Mobyan ya bayyana haka ne a wani taron manema labaru,kamar yadda kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto. Wasu yankuna na kasar ta Afirka Ta Kudu sun fuskanci saukar ruwa kamar da bakin kwarya, haka nan kuma saukar kankara, da hakan ya sa aka shiga cikin yanayin sanyi mai tsanani da kuma yankewar wutar lantarki a wasu yankunan. Ambaliyar ruwan da aka samu a kusa da wata makaranta ya ja motar da take dauke da dalibai 13, da hakan ya yi sanadiyyar rasuwarsu. Tuni...
Haka kuma, ya zargi Matawalle da karɓar Naira miliyan 300 daga tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, don a sako ɗaliban, amma ya bai wa ‘yan bindiga miliyan 30 kacal. APC ta ƙaryata wannan zargi. Ta kuma bayyana cewa zargin Kaura yana shafar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar kamar tsohon Gwamna Abdulaziz Yari, wanda yanzu ke wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa. Jam’iyyar APC ta ƙalubalanci Kaura da ya kawo hujjoji kan wannan zargi da kuma wasu mutane da aka sace a jihar, kamar satar ɗalibai mata 270 daga makarantar Government Girls Secondary School da ke Jangebe a ranar 26 ga watan Fabrairun 2021, da kuma satar ɗaliban Kwalejin Noma da Kiwo da ke Bakura. APC ta jaddada cewa gwamnatin...
Aƙalla mutum huɗu ciki har da jaririn wata tara aka kashe a wani hari da aka kai ƙauyen Nkiendowro da ke Ƙaramar Hukumar Bassa a Jihar Filato. Mutanen da suka rasu sun haɗa da mata biyu da namiji ɗaya, wanda aka ce suna aikin jigilar kwashe tumatir daga ƙauyen zuwa kasuwar Farin-Gada da ke Jos lokacin da aka kai musu hari. Rashin wutar lantarki ya durƙusar da kasuwanci a Arewa Maso Gabas An kashe mutum 41 cikin mako ɗaya a Filato Wasu mutum biyu kuma sun jikkata a harin, wanda yanzu haka suna karɓar magani a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba. Shugaban tsaron al’ummar Miango, Josiah Zongo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an...
Haka kuma, ya taɓa zama mataimakin kocin Super Eagles lokacin da Jose Peseiro ke jan ragamar ‘yan wasan Nijeriya. A kakar bara ta NPFL, ya jagoranci Kano Pillars ta ƙare a matsayi na 9. Ko da yake Usman bai bayyana cikakken dalilin saukarsa ba, masu sharhi a wasan ƙwallon ƙafa na ganin matsin lamba daga magoya baya da rashin nasara sun taka rawa. Har yanzu, ƙungiyar ba ta fitar da sabuwar sanarwa kan wanda zai maye gurbinsa ba. Masu sha’awar wasan ƙwallon ƙafa a Kano na fatan za a kawo sabon kocin da zai dawo da martabar Pillars a wasannin gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Rashin wutar lantarki a Arewa maso Gabashin Najeriya ya tilasta wa jama’a da ’yan kasuwa zaman ɗari-ɗari da asarar dukiya, sakamakon aikin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN), ke yi na aikin sabbin turakun wutar lantarki. Rashin wutar, wanda ya fara daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Yuni, ya shafi layin wutar lantarki na Jos–Bauchi–Gombe mai ƙarfin 132kV. An kashe mutum 41 cikin mako ɗaya a Filato Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa Alhazai A Jihar Adamawa, musamman a birnin Yola, jama’a na cikin matsanancin hali. Hajiya Aisha Babangida daga Jimeta, ta ce rashin wutar ya tilasta masa soye dukkanin naman ragon sallarta domin babu wutar da za ta ajiye shi a firinji....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba An ware ranar 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Dimokuraɗiyya a Najeriya domin tunawa da ranar da aka gudanar da zaɓen da ake ɗauka a matsayin mafi sahihanci da adalci a tarihin ƙasar. Sai dai, bayan sama da shekaru 30 da gudanar da wannan zaɓe da kuma gwagwarmayar da ta biyo baya, wasu masana na ganin har yanzu ba a kai ga amfanin da ake murad daga dimokuraɗiyyar ba. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa Ko mene ne hujjar kowane ɓangare? Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau zai yi duba a wannan lokaci. Domin sauke...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba An ayyana 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin Ranar Dimokuradiyya a Najeriya don tunawa da ranar da aka gudanar da zaben da aka yi amanna cewa shi ne mafi sahihanci da inganci a tarihi. Sai dai bayan fiye da shekara 30 da wannan zabe da fafutukar da ta biyo baya, wasu masana suna ganin har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Matsalar Kwacen Waya DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Ko mece ce hujjarsu? Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
JMI ta bayyana cewa zata yi amafani da hakkinta wanda doka ya bata na ficewa daga yarjeniyar NPT don sake farfado da takunkuman tattalin arziki na MDD a kan kasar. Jakadan kasar Iran a MDD, Amir Saeid Iravani ne ya bayyana haka a jiya Laraba. Kamfanin dillanbcin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Iravani yana fadar haka a wata wasika da ya rubutawa kwamitin tsaro na MDD a jiya. Ya kuma kara da cewa Iran zata yi amfani da dokokin da suka bada damar yin hakan. Kasashen Turai guda Uku jamusa Farana da Burtania suna son su yi amfani da damar da ake kira snap back don sake farfado da takunkuman MDD a kan kasar na yarjeniyar JCPOA. Ya...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas aragchi da tokwransa na kasar Masar Badr Abdullati da kuma tokwaransu na kasar Omman Badr ben Hamad Al-Busaidi sun tattauna a tsakaninsu a birnin Oslo inda suka halattar taron tattaunawa ta 22th da ake gudanarwa a birnin na Oslo babban birnin kasar Norway. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa bangarorin biyu sun yi maganar rikice-rikicen da ke faruwa a yankin da kuma hanyar warwaresu. Taron oslo na shekara shekara dai a wannan karon ya maida hankali ne kan abubuwan da suke faruwa a yankin Asiya da kuma hanyoyin da yakamata abi don rage halin da ake ciki a yankin. Musamman matsalar yaki da kima kissan kiyashin da ke faruwa a...

Ministan Tsaro Na Kasar Iran ya bada Labarin Gwajin Wani Sabom Makami Mai Limzami Mai Daukar abubuwan Fashewa Har Ton Biyu
Ministan tsaro na kasar Iran ya bayyana cewa sojojin kasar sun yi gwajin wani makami mai linzami wanda yake iya daukar abubuwan fashewa hart un biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Burgediya Janar Amir Nasirzade yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa . wannan gwajin sako ne ga gwamnatin Amurka da kawayenta. Idan wani ya dora mana yaki sai sun fi mu shan wahali. Don tare da wadannan shirye shiryen da kuke na kare kammu sai mun kori amurka daga yankin nan. Yace iran tana cikin fushi kan abinda yake faruwa a Gaza don haka duk wata dama da ta samu zata maida martanin da ya dace. Ministan ya bayyana haka ne a jiya Laraba...
Ministan man fetur na kasar Iran Mohsen Paknejad ya bayyana cewa kasarsa zata ci gaba da saida danyen man fetur ga masu sayensa a kasashen waje duk tare da kokarin gwamnatin kasar Amurka na kara kuntatawa kasar a bangaren saida makamashin kasar ga kasashen waje. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya laraba bayan taron majalisar ministocin kasar a nan Tehran. Ministan ta kara da cewa shirin Amurka na hana Iran saida danyen manta ga kasashen waje zai rugurguje kamar yadda ya rugurguje a baya. Y ace don mun rika mun gano kan zaren lalata duk wani shiri na hana mu saida danyin man ga masu sayan man kasar. Ministan ya bayyana...
Ya ce ya fahimci haka ne bayan kallon wani shiri a talabijin inda ya ga wasu mutane na nuna rashin jin daɗi. Wike ya ce wannan baƙin ciki na su shi ne ke ba shi ƙwarin gwiwa. “Na ji wani irin abu a zuciyata, sai na kunna talabijin. A nan ne na gano cewa wasu na cikin baƙin ciki saboda abubuwan alheri da ake yi,” in ji shi. Ya ƙara da cewa: “Yanzu da na gane suna cikin baƙin ciki, zan ci gaba da sanya musu ƙarin ciwon zuciya. Farin cikinmu na ƙaruwa ne da jin haushinsu. Wannan shi ne sabon aikina na ci gaba da sa musu hawan jini.” Wike ya yi raha da cewa yayin da suke cikin...
Aƙalla jihohi 11 na Najeriya sun kashe sama da Naira biliyan 6.2 wajen tallafa wa Alhazansu domin sauƙaƙa musu wajen zama a ƙasar Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin 2025. Wannan tallafi ya haɗa da kuɗi, jakunkunan tafiya, da kuma sayen raguna na hadaya domin sallar Layya. Tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka cikin shekaru uku masu zuwa — Bankin Duniya Dalilin da babu abin da gwamnatin NNPP ta taɓuka a Kano — APC Gwamnatin Jihar Sakkwato ce ta fi kowa bayar da tallafi mafi yawa, inda Gwamna Ahmed Aliyu, ya bai wa kowane daga cikin alhazai 3,200 na jihar Riyal 1,000 (kimanin Naira 450,000). A Kano kuwa, kowane alhaji daga cikin alhazai 3,345 sun samu kyautar Riyal 50. Gwamnatin Jihar...
A Shenzhen dake kudancin Sin ma, ana amfani da jiragen marasa matuka wajen jigilar kayayyakin kiwon lafiya ta yadda hakan ke magance tsaikon da ake samu saboda cunkoson motoci a tituna da kuma taimakawa wajen ceto rayukan marasa lafiya da ke bukatar daukin gaggawa. Bugu da kari, an samar da tsarin sufurin jirage masu tafiya kusa da doron kasa a lardunan Jiangxi, Sichuan da Guangxi inda ake fuskantar dimbin kalubalen fadada hanyoyi saboda yanayin tsaunukansu. Tabbas, duka wadannan sun zo da wani irin sabon salo a duniya da kasashe za su yi koyi da kasar Sin wajen zamanantar da sha’anin jigilarsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
A yau ne aka gudanar da taron ministoci masu daidaita ayyukan da aka amince, a gun taron tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, a birnin Changsha dake lardin Hunan na kasar Sin, inda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci bikin kaddamar da taron, tare da karanta wasikar murnar bude bikin ta shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana ministan harkokin wajen kasar Kongo Brazaville Jean-Claude Gakosso, ya karanta wasikar murnar bude bikin ta shugaban kasarsa Denis Sassou Nguesso. Taron ya samu halartar ministocin kasashe membobin kungiyar FOCAC, da wakilan kwamitin AU, da jakadun kasashen Afirka dake kasar Sin, wadanda adadinsu ya zarce 100. Wang Yi ya jaddada cewa, ya kamata Sin da Afirka su nuna goyon...
Majalisar Dattawan Nijeriya ta bayyana shirin kafa dokar da za ta mayar da rantsar da shugaban kasar a kwaryar majalisar, maimakon yadda ake yi a dandalin taro na Eagle da ke tsakiyar birnin Abuja. DW ta ruwaito cewa ita dai Majalisar Dokokin Nijeriya ta 10 ta yi fice wajen dauko batutuwan da ke haifar da cece-kuce, kama daga yunkurin mayar da yin zabe ya zama dole da kuma hukunta duk wanda ya ci mutuncin taken Nijeriya sai kuma wannan batu na amfani da doka domin sauya tarihin da aka daura dambarsa tun a shekara ta 1999 da aka sake kafa dimokuradiyya a kasar. Tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka cikin shekaru uku masu zuwa — Bankin Duniya Dalilin da babu abin...
Bankin Duniya ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka ba tare da taɓarɓarewa nan da shekaru uku masu zuwa. Bankin ya yi hasashen haɓakar ma’aunin tattalin arzikin cikin gida, GDP da kashi 3.6 cikin 100 a shekarar 2025, sai kashi 3.7 a shekarar 2026 da kuma kashi 3.8 a shekarar 2027. Dalilin da babu abin da gwamnatin NNPP ta taɓuka a Kano — APC Amurka da China sun cimma sabuwar yarjejeniyar kasuwanci A cewar sabon rahoton tattalin arzikin duniya da Bankin ya fitar, ana sa ran za a tallafa wa matsakaicin lokaci na Nijeriya ta hanyar samar da ingantattun albarkatun mai, da gyare-gyaren da ake ci gaba da yi, da kuma farfado da ƙwarin gwiwar masu zuba jari....
Ƙungiya mai rajin kishin APC a Kano mai suna APC Patriotic Volunteers, ta ce shekaru biyun da jam’iyyar NNPP ta shafe tana mulkin jihar nakasu ne da ke nuna tsantsar rashin ƙwarewarta a gwamnatance. A taron da ta gudanar da manema labarai a Kano, ƙungiyar bisa jagorancin shugabanta Alhaji Usman Alhaji (Wazirin Gaya) ta ce nazarin da ta yi wa salon mulkin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar mata da gazawarsa wajen haɓaka ɓangarori masu muhimmanci duk da makudan kudaden shiga da gwamnatin tarayya ke bata, da kuma kudaden shiga na cikin gida da take samu. Mokwa: Zulum ya kai ziyarar jaje Neja, ya bayar da tallafin N300m Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Amurka da China sun cimma sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da ke kawo karshen zaman tankiyar da aka soma tsakanin kasashen biyu tun bayan hawan Donald Trump karagar mulki. Kasashen biyu sun cimma matsaya a kan kan cinikin wani rukini na ma’adinai da Chinar ke fitarwa, wadanda ake kira da sunan Terres Rares, wadanda ake yi amfani da shi wajen samar da lantarki da kuma makamashin da ake sabbintawa. An kashe mutum 15 a sabbin hare-hare a Filato Mokwa: Zulum ya kai ziyarar jaje Neja, ya bayar da tallafin N300m A baya a taron kasar Switzerland, Washington ta amince da rage haraji kan kayayyakin kasar China daga kashi 145 zuwa kashi 30 cikin 100, don musanya makamancin wannan mataki da Beijing ta...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ta sha bamban da majalisun da ke goyon bayan masu goyon baya masu laifi misalin masu kisan gilla a Gaza Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada a yau Laraba cewa: Matsayin majalisar shawarar Musulunci ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bambanta da kasashen duniya, kuma ya sha bamban da majalisar da ke goyon bayan zalunci, nuna wariya, banbance-banbancen ra’ayi da masu aikata laifuka irin su kisan gilla a Gaza. Yayin ganawarsa da mambobin majalisar shawarar Musulunci a ranar Laraba, Jagora ya yi la’akari da cewa: Majalisun dokokin duniya suna da kamanceceniya ta fuskar nauyi doka. Duk da haka, ya jaddada cewa ma’auni...
Wani ganau mai suna Kespan Iliya wanda shi ma mazaunin unguwar ne ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan unguwar na cikin barci lokacin da ‘yan bindigar suka iso cikin shigar kwamandoji, inda suka rika harbe-harbe kan mazauna unguwar. LEADERSHIP ta fahimci cewa, sama da gidaje 96 ne kuma aka kone a Gyenbwas, al’ummar gundumar Langai ta karamar hukumar Mangu a yayin harin. Kokarin jin ta bakin jami’im yada labarai na rundunar ‘Operation Save Haven (OPSH)’, Manjo Samson Zhakom ya ci tura domin wayarsa a kashe take a lokacin rubuta wannan rahoto. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Inganta sinadarin Uranium da ɗage takunkumai na iya sa tattaunawar ta yi amfani Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta cewa: A bayyane yake cewa cimma yarjejeniyar da za ta tabbatar da zaman lafiya na dindindin na shirin makamashin nukiliyar Iran abu ne mai yiyuwa, kuma ana iya cimma shi cikin sauri. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta a shafinsa na Twitter game da sabon zagayen tattaunawa tsakanin Iran da Amurka da kuma matsayin Iran a kansu yana mai cewa: Shugaba Trump ya bayyana a lokacin da ya shiga fadar White House cewa ba lallai ne Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, wannan matsayi ya yi daidai da akidar Iran...
Rayukan aƙalla mutum 15 sun salwanta a wasu sabbin hare-haren da aka kai wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Mangu a Jihar Filato. Shugaban ƙaramar hukumar, Emmanuel Bala, ya shaida wa manema labarai cewa, a daren ranar Talata ce aka kashe mutum bakwai a kauyen Bwai sai kuma mutane takwas a kauyen Chinchim duk a ƙaramar hukumar ta Mangu. Mokwa: Zulum ya kai ziyarar jaje Neja, ya bayar da tallafin N300m Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya Wannan lamari na daga cikin sabbin hare-hare da tashin hankali da ke ci gaba da faruwa a yankin a wannan makon tsakanin yan kabilar Mwaghavul da Fulani. Hare-hare daban-daban guda uku da suka faru a yankin ƙaramar hukumar...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Sake Tunzura Iran Shirin Makamashin Nukiliyarta Zai Fuskanci Martani
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Sake kunna ‘hanyar tayar da hankali’ zai gamu da martani mai ƙarfi na Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Fitar da kudiri kan Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta yi ba zai shafi kudurin al’ummar Iran ba ko kuma ci gaban shirinta na makamashin nukiliya na zaman lafiya. A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Iran a yammacin ranar Talata, Baqa’i ya yi la’akari da dukkanin rahotanni da kudurorin da suka shafi siyasa. Ya kuma kara da cewa Iran ba ta keta hurumin da ya rataya a wuyanta ba, kuma kasashen yammacin turai suna dora barazanarsu ne kan...

He Lifeng Ya Bukaci Amurka Da Ta Warware Takaddamar Cinikayya Da Sin Ta Hanyar Tattaunawa Da Hadin Gwiwa
Mataimakin firaministan Sin He Lifeng, ya bukaci Amurka da ta warware takaddamar cinikayya da Sin ta hanyar tattaunawa, da hadin gwiwa da zai iya haifar da moriyar bai daya. He, ya ce Sin na jaddada burin ganin Amurka ta yi aiki da bangaren Sin, ta yadda za a martaba alkawura da matakai da aka amince, da nuna sahihanci wajen yin aiki tukuru, da aiwatar da gaskiya da kwazo wajen aiwatar da matsayar da aka cimma, ta yadda za a kai ga kare nasarorin da aka cimma ta hanyar shawarwari. He, ya yi tsokacin ne yayin taron farko na shawarwari game da harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, wanda ya gudana a ranakun Litinin da Talata a birnin...
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da takwarorinsa na kasashen Afrika da suka zo kasar Sin domin halartar taron ministoci masu jagorantar aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin a taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika. Wang Yi wanda kuma mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya tattauna jiya Talata a Changsha, babban birnin lardin Hunan, da ministocin da suka hada da Musalia Mudavadi na Kenya da Yassine Fall ta Senegal da Mahmoud Thabit Kombo na Tanzania da Selma Ashipala-Musavyi ta Namibia da Phenyo Butale na Botswana da kuma Tete Antonio na Angola. Da yake ganawa da Musalia Mudavadi na Kenya, Wang Yi ya ce a shirye Sin take ta hada hannu da...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kai ziyara Jihar Neja domin jajanta wa mutanen Mokwa da iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa. Zulum ya kuma bayar da tallafin Naira miliyan 300 domin taimaka wa waɗanda iftila’in ya shafa. Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3 Zulum, ya ce Gwamnatin Borno ta kawo wannan taimako ne don tallafabwa gwamnatin Neja wajen rage raɗaɗin ambaliyar da ta kashe mutane da lalata dukiyoyi. Ya kuma buƙaci sauran gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi su haɗa kai don kare al’umma daga iftila’i da sauyin yanayi ke haddasawa. Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya nuna godiya bisa wannan...
Tinubu ya bayyana cewa, aikin titin, wanda aka yi watsi da shi tuni duk da muhimmancin titin a cikin taswirar Abuja, amma yanzu ya kammalu a karkashin jagorancin Ministan babban birnin tarayya. Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya bai wa babban birnin tarayya zaman lafiya, da ci gaban Nijeriya, da kuma bai wa sojojin Nijeriya aminci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Shugabannin Sin Da Kongo (Brazaville) Sun Aike Da Wasikun Taya Murna Ga Taron Ministocin Kula Da Aiwatar Da Sakamakon Taron FOCAC
Yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Kongo Brazaville Denis Sassou Nguesso, sun aike da wasiku na taya murna ga taron ministocin kula da harkokin da suka shafi aiwatar da sakamakon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wato FOCAC, inda suka taya murnar bude taron. Cikin sakonsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, a halin yanzu, yanayin kasa da kasa ya cika da sauye-sauye da hargitsi. Kuma kasar Sin ta dage wajen samar da sabbin damammaki ga duniya tare da sabbin nasarorin da aka samu na zamanantarwa iri ta kasar Sin, da samar da sabon kuzari ga kawayen kasashe masu tasowa na duniya kamar kasashen Afirka ta hanyar shiga a dama da su a...
Ana zargin wata mata mai suna Khadija kan zargin kashe ’yarta mai shekaru 11, Fadila, saboda Naira 100 da ta samu a yawon Sallah a unguwar Tukur Tukur da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna. Lamarin ya faru ne a ranar Asabar kafin sallar Magariba, inda lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a unguwar har maƙwabta suka ƙi yi wa gawar yarinyar sallah saboda tsoron abin da zai biyo baya. Ranar Dimokuraɗiyya: Tinubu zai yi wa ’yan Najeriya jawabi Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3 Wasu maƙwabta sun bayyana cewa Khadija ta doke Fadila da taɓarya ne saboda ta zargi yarinyar da satar Naira 100. Sun ce irin wannan ɗabi’a na duka da tsangwama...
Cherki ya buga wasansa na farko a Lyon yana da shekara 16 a watan Oktoban 2019 kuma ya bar kungiyar inda ya ci kwallaye 29 sannan ya taimaka aka jefa 45 a wasanni 185 da ya bugawa kungiyar ta Faransa. Cherki ya wakilci kasar Faransa kuma ya lashe lambar azurfa a gasar Olympics da aka gudanar a birnin Paris na kasar Faransa a bara. Daraktan kwallon kafa na Manchester City, Hugo Viana ya ce, “Babu shakka a yanzu Cherki yazo inda ya dace kuma zai cigaba a karkashin jagorancin Guardiola, kuma na yi imani zai iya zama babban dan wasa a duniya tare da goyon bayan abokan wasa da masu horarwa”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Don haka, a cikin sanarwar da aka fitar a wannan karo, kasashen Afirka sun nuna yabo kan jajircewar kasar Sin, da kuma kudurin da kasar ta dauka na kare adalci, da kuma ingancin tsare-tsaren tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa. Har ila yau, kasar Sin ita ma ta nuna godiya ga kasashen Afirka, kan yadda suke bin ka’idojin kare ‘yancin kai, da adalci, tare da tsayawa kan matsaya guda wajen fuskantar matsin lamba da aka sanya musu. Hakika idan mun tantance kwarin gwiwar Sin da Afirka, za mu ga da farko ya zo daga dangantakarsu mai dorewa ta hadin gwiwa da juna. Za mu iya daukar misalin bangaren ciniki: daga shekarar 2000, lokacin da aka kafa dandalin tattaunawar...
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar Alhamis, domin bikin ranar dimokuraɗiyya na 2025. A cewar wata sanarwa daga kwamitin shirya bikin, shugaban ƙasa zai kuma je zaman haɗin gwiwa da ’yan majalisar dokoki da rana. Na shirya yin haɗaka don ƙalubalantar Tinubu a 2027 – Amaechi Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3 Sanarwar ta kuma bayyana cewa ba za a yi faretin bikin a bana ba. A maimakon haka, za a yi muhawara da jama’a a fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 4 na yamma. Bikin bana na zuwa ne yayin da Najeriya ke cika shekara 26 a gwadaben mulkin dimokuraɗiyya...
Tsohon Ministan Sufuri kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa ya shirya yin haɗaka da wasu ’yan siyasa domin ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027. A wata hira da ya yi da BBC, Amaechi ya ce matsin tattalin arziƙi da tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar ne babban dalilin da ya sa ake buƙatar sabuwar haɗaka a siyasa. Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3 Rikicin Filato: An sake kone gidaje 96 a Mangu Ko da yake bai tabbatar da cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa ba, sai dai ya ce komai zai bayyana nan da wani lokaci. “Lokaci ne kawai zai nuna,” in ji shi....
Majalisar Dokokin Jihar Kuros Riba, ta dakatar da shugabar Ƙaramar Hukumar Bekwara, Hon. Theresa Ushie, na tsawon wata uku, domin a gudanar da bincike kan wasu zarge-zarge da ake mata. An ce kimanin wakilan ƙaramar hukumar 10 daga cikin 11 ne suka yi ƙarar shugabar, inda tara daga cikinsu suka rattaba hannu suna goyon bayan a dakatar da ita. Gwamnatin Kano za ta binciki musabbabin gobarar kasuwar Farm Center Za a dauke wa jihohin Arewa maso Gabas wutar lantarki na tsawon kwana 4 Ɗaya daga cikin wakilan ne kawai bai yarda ba. Ana zargin Hon. Ushie da amfani da kuɗin Ƙaramar Hukumar ba tare da shawarar majalisar jihar ba, tare da yin wasu muhimman ayyuka ba tare da tuntuɓar ’yan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin da zai binciki musabbabin gobarar da ta tashi a kwanan nan a kasuwar wayoyin hannu ta Farm Center da ke jihar. A ranar Juma’ar da ta gabata ce dai gobara ta tashi a kasuwar wacce aka yi kiyasin ta kone shaguna sama da 300 tare da janyo wa ’yan kasuwa asarar miliyoyin Naira. Za a dauke wa jihohin Arewa maso Gabas wutar lantarki na tsawon kwana 4 Kotu ta yi fatali da bukatar Akpabio, ta umarce shi ya biya Natasha N100,000 Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Ibrahim ne ya rantsar da kwamitin a madadin Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf. Kwamitin dai kasance karkashin jagorancin Kwamishinan Ayyuka na Musammanna jihar, Alhaji Umar Ibrahim kuma...
Kamfanin Dakon Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa za a dauke wutar lantarki a ilahirin jihohin yankin Arewa maso Gabas guda shida na tsawon kwana hudu. A cikin wata wasika da ya aike wa kamfanonin rarraba wutar lantarki da ke kula da jihohin shida, TCN ya ce yayin da a wasu jihohin wutar za ta dauke gaba daya, wasu yankunan kuwa karancin wutar za a samu a tsakanin kwanakin. Jihohin da lamarin zai shafa sun hada da Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe. Kotu ta yi fatali da bukatar Akpabio, ta umarce shi ya biya Natasha N100,000 DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Wasikar wacce ke dauke da sa hannun...

Iran Ta Sami Nasara Akan Korea Ta Arewa Akarkashin Share Fagen Shiga Gasar Cin Kofin Duniya Na Kwallon
Kungiyar kwallon kafa ta Iran ta sami nasarar akan abokiyar karawarta ta kasar Korea Ta Arewa da kwallaye uku masu kyau a wasan da aka yi a filin wasa na “Azadi” na Tehran. Kasashen biyu dai suna a karkashin; bangare na uku a Asiya saboda share fagen kai wa ga shiga gasar cin kofin kwallon duniya na 2026. Dan wasa mai suna Muhammad Muhibbi ne ya ci kwallon farko, a mintuna 74 da fara wasan, sai kuma Mahdi Darimi a mintuna 77, sa Amir Husain Husain zadeh, a minti 3 da aka kara, bayan cikar mituna 90. A bangaren kungiyar kwallon kafa ta Korea Ta Arewa kuwa, ta kammala wasannin nata da ‘yan wasa 10 bayan da aka kori daya...
Sojojin HKI sun kai hari akan Falasdinawan da su ka yi cincirindo domin karbar abinci da hakan ya yi sanadiyyar shahadar da dama daga cikinsu. Tun da safiyar yau Laraba ne dai sojojin HKI su ka rika kai hare-hare akan cibiyoyin cibiyoyin raba agaji wadanda dama suna a karkashin kulawar su kansu ‘yan sahayoniyar da kuma Amurka. Har ila yau hare-haren sun shafi gidajen fararen hula a cikin wasu unguwanni na zirin Gaza. Majiyar Asibitin “Audah” ta sanar da cewa an kai shahida 4 da kuma wadanda su ka jikkata sanadiyyar hare-haren na sojojin mamaya a wurin raba kayan agaji dake kan titin “Salahuddin” a tsakiyar zirin Gaza. A arewacin yankin Gaza kuwa wasu samarin Falasdinawa 4 sun yi shahada...
Ya ƙara da cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe zaɓe shi kaɗai. “Ku bai wa Kudu tikitin, ku ga sakamako. Amma idan PDP ta ci gaba da tafiya a kan wannan kuskure, to, za ta fuskanci babbar matsala a 2027,” Yusuf ya bayyana. Ya kuma bayyana cewa Atiku Abubakar ba ɗa jam’iyyar PDP ba ne a yanzu, yana tare da wata sabuwar tafiyar haɗin gwiwa ta siyasa. Yusuf ya ɗora alhakin faɗuwar jam’iyyar a zaɓen 2023 kan rashin kyakkyawan shugabanci da kuma rabon tikiti ba bisa ƙa’ida ba. Ya ce rikicin cikin gida da kuma gazawar PDP wajen kulawa da ‘yan Kudu ne suka sa jam’iyyar ta faɗi. Ya kuma nuna takaicinsa game da sauya sheƙar Gwamnan...
Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta yi fatali da bukatun Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, sannan ta ci shi tarar Naira 100,000. Kotun, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Hamman Barka dai ta yi watsi da bukatun ne kan karar da aka shigar ranar 21 ga watan Mayun 2025, bayan neman bukatar janye karar da aka daukaka. Bukatun dai na kunshe ne a cikin wasu kararraki masu lamba CV/395/M1/2025 da kuma CV/395/M2/2025, wadanda aka shigar a ranakun uku da kuma 25 ga watan Mayun 2025, wanda a cikinsu aka ambaci sunan Akpabio a matsayin mai daukaka kara. DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Rikicin Filato:...
Sai dai wasu daga cikin dillalan man fetur a Nijeriya na ganin ya kamata matatar ta riƙa sayar da lita ɗaya ƙasa da Naira 800, la’akari da cewa ana sayar mata da ɗanyen mai a kuɗin Naira maimakon Dala. Dangote dai ya nuna ƙwarin guiwar cewa kamfaninsa zai taka rawar gani wajen samar da isasshen mai ga ‘yan Nijeriya tare da sauƙaƙa matsin da mutane ke ciki sakamakon hauhawar farashin fetur a ƙasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Amma har zuwa yanzu, babu cikakken bayani daga Gwamnatin Tarayya. A watan Mayun 2025 ne Tinubu ya miƙa buƙatar samun amincewar majalisa domin karɓar rancen Dala biliyan 21 daga ƙasashen waje, ciki har da Dala biliyan biyar daga Aramco. Rahoton Reuters bai bayyana sunayen bankunan da za su taimaka ba, amma majiyoyi sun ce ɗaya daga cikin bankunan na nahiyar Afrika ne, sauran kuma daga Gabas ta Tsakiya. Idan aka cimma yarjejeniyar, wannan zai zama mafi girma daga cikin bashin da Nijeriya ta taɓa karɓa a irin wannan hanya daga Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
A cewarsa, shuwagabancin Tinubu ya gina tubalin ci gaba mai ɗorewa ta hanyar yanke hukunci masu wahala amma masu amfani. Dangane da sauyin jam’iyyun siyasa da ke faruwa, Namadi ya ce yawaitar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC alama ce da ke nuna yadda jama’a ke ƙara amincewa da shugabancin Tinubu da kuma burin da yake shi ga ƙasar nan. Ya ce masu barin jam’iyyunsu suna haka ne domin suna ganin makoma mai kyau a ƙarƙashin jagorancinsa. Har ila yau, Namadi ya bayyana cewa ziyarar aikin da ya kai Indiya kwanan nan ta samar da muhimman yarjejeniyoyi da masu saka jari da ƙwararru don bunƙasa harkar noma a Jihar Jigawa. Ya ce an cimma matsaya a fannoni irin su kiwon shanu,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Asibiti ko dakin shan magani ko wani bigire mai kama da wadannan wuri ne da marasa lafiya kan je ko ake kai su don neman waraka a duk lokacin da bukatar haka ta taso. Wuri ne da akan ware domin ceto rayukan wadanda suka jikkata suke kuma bukatar agajin gaggawa. A bisa al’ada kuma, ana sa ran samun tausayi da jinkai da sadaukarwa wajen yin dukkan mai yiwuwa kuma a ko wane lokaci don ceton rayuka daga jami’an lafiya. Sai dai ’yan Najeriya da dama sun dade suna kokawa da yadda a cewarsu wasu jami’an kiwon lafiya kan nuna halin ko-in-kula, a wasu lokutan ma da sakaci, wanda kan kai rasa rayuka. NAJERIYA...
Iran ta bada sanarwan cewa ta sharia matakan da zata dauka kan hukuma IAEA mau kula da makamashin nukliya ta duniya idan ta samar da kudurin yin allawadai ko kuma rashin bada ahadin kai ga hukumar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ik Baghae yana fadara haka a jiya Talata . Ya kuma kara da cewa martani da zata mayar tare da hadin kai da hukumar makamashin nukliya ta kasar wato ko Atomic Energy Organization of Iran (AEOI). Baghae yayi allawadai da rahoton da Daraktan hukumar IAEA Rafael Grossi ya bayar dangane da shirin Nukliyar kasar kafin taron gwamnonin hukumar. Yace wannan a fili ya nuna cewa hukumar AIEA tana aiki...
Gwamnatin kasar Burtaniya ta bada sanarwan kakabawa ministocin HKI guda biyu takunkuman tattalin arziki saboda ra’yinsu na wuce gona da Iri wanda zai bata duk wani shirin da kasashen duniya suke da shin a tabbatar da zaman lafiya a yanking abas ta tsakiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kira-kirayen ministocin na kara mamaya da kuma korar falasdina daga yankin yamma da kogin Jordan ne yasa burtaniya ta nuki wannan batakin. Bezalel Smotrich dai , wanda shi ne ministan kudi na HKI ya ce HKI zama kara mamayar yankin yamma da kogin Jordan, kafin zaben shekara ta 2026, sannan ya rantse kan cewa za’a share falasdinawa a gaza, kuma zasu wargaza kungiyar Hamas a cikin...
Tawagar fursinonin yaki na kasar Rasha daga kasar Ukrain sun koma gida, saboda yarjeniyar da kasashen biyu suka cimma a birnin Istambul na kasar Turkiyya. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya bayyana cewa a taro na biyu tsakanin jami’an gwamnatocin kasashen biyu a birnin Istambul na kasar Turkiya wato ranar 2 ga watan yunin da muke ciki ce suka cimma yarjeniyar musayar fursinonin a karo na biyu. Labarin ya nakalto ministan tsaron kasar Rasha yana cewa fursinonin Rasha da suke hannun Ukraine sun isa kasar Rasha a jiya talata. Haka ma bangaren Rasha ta mikawa gwamnatin Ukraine wasu daga cikin fursinonin da suke hannunta. Ministan ya kara da cewa a halin yanzu firsinonin suna kasar Belerus inda aka...
Kasashen Sin da Kenya sun zurfafa hadin gwiwarsu a bangaren kiwon lafiya, inda kasar Sin ta bayar da guraben tallafin karatu 500 da kaddamar da shirye-shiryen musaya 20 a kwacce shekara. Wata sanarwa da aka fitar bayan taron da aka yi tsakanin jakadar Sin dake Kenya Guo Haiyan da babban sakataren ma’aikatar lafiya ta kasar Aden Duale, ta ce hadin gwiwar kasashen biyu na da muhimmanci wajen kyautata makomar kasar ta zama jagora a bangaren kiwon lafiya. A cewar Adel Duale, bangarorin biyu sun kuma tattauna game da kafa cibiyoyin samar da riga kafi da harhada magunguna ta hanyar amfani da fasahar kasar Sin. Ya kara da cewa, shirin hadin gwiwa na dala miliyan 500 a tsakaninsu zai mayar da...
Gwamnatin Jihar Borno ta yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta hanzarta ɗaukar mataki kan ɗan kwangilar da ta baiwa aikin yashe dam ɗin Alau da ya haifar da ambaliya a bara. Ta ce duk da cewar sun yashe wani sashe na dam ɗin amma, har yanzu akwai babbar barazana da za a iya fuskantar mummunar ambaliya. Dalilin da Nijeriya ke fuskantar tsaiko wajen karɓar rancen $5bn daga Saudiyya Saudiyya za ta fara bayar da bizar Umara Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin tsaro na Jihar Borno, Farfesa Umar Tar da harkokin tsaro ya shaida wa BBC cewa an bayar da kwantaragin kuma minista ya je ya ƙaddamar da aikin. “Har yanzu ba mu ga ’yan kwangila sun zo domin...
Gwamnatin Jihar Borno ta yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta hanzarta ɗaukar mataki kan ɗan kwangilar da ta baiwa aikin yashe dam ɗin Alou da ya haifar da ambaliya a bara. Ta ce duk da cewar sun yashe wani sashe na dam din amma, har yanzu akwai babbar barazana da za a iya fuskantar mummunar ambaliya. Dalilin da Nijeriya ke fuskantar tsaiko wajen karɓar rancen $5bn daga Saudiyya Saudiyya za ta fara bayar da bizar Umara Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin tsaro na Jihar Borno, Farfesa Umar Tar da harkokin tsaro ya shaida wa BBC cewa an bayar da kwantaragin kuma minista ya je ya ƙaddamar da aikin. “Har yanzu ba mu ga ’yan kwangila sun zo domin...
LEADERSHIP ta tuna cewa, gwamnatin jihar da jami’an tsaro sun fuskanci matsin lamba daga mazauna yankunan da lamarin ya shafa domin shawo kan lamarin. Fanwo, ya ba da tabbacin cewa, gwamnati ta yi shiru, amma tana samun nasara a yakin da take da masu aikata laifuka ta karkashin kasa, musamman masu garkuwa da mutane a jihar. Ya ce, nasarar da gwamnati ta samu ya biyo bayan ingantattun tsare-tsare da zurfafa hadin gwiwar hukumomin tsaro da nufin tabbatar da tsaro da walwalar kowane dan jihar Kogi. Yayin da take jajantawa iyalan wadanda hare-haren na baya-bayan nan ya shafa, gwamnatin jihar ta jaddada cewa, bai kamata a yi amfani da irin wadannan kalubalen wajen yada labaran karya ko firgita...
Nijeriya tana fuskantar tsaiko a tattaunawar da ake yi da kamfanin man fetur mafi girma a duniya mallakin Saudiya wato Aramco, dangane da shirin karɓar rancen Dala biliyan biyar. Wani rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ne ya bayyana hakan da cewar Nijeriyar na neman rancen kuɗin ne wanda take shirin ƙulla yarjejeniyar biya da ɗanyen manta. Gwamnan Kebbi ya bai wa ’yan kasuwar katako tallafin ibtila’in gobara A saurari sauyin da za mu yi wa ɓangaren man fetur a Nijeriya — Dangote Wasu majiyoyi huɗu sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa faɗuwar baya bayan nan da farashin ɗanyen mai ya yi a kasuwannin duniya shi ne ya janyo tsaikon, bayan da bankunan da ake sa ran...
Gwamnan ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Neja kan mummunar barnar da ambaliyar ruwan ta yi, na salwantar da rayuka da barnata dukiya da dama. Gwamna Umar Bago na jihar Neja, ya yabawa takwaransa na Borno bisa wannan ziyarar da kuma bayar da gudunmawar, inda ya ce lokaci ya yi da za a nuna soyayya ga juna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Kebbi, Dakta Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) ya jajanta wa al’ummar kasuwar katako ta bayan kara da ke Birnin Kebbi bisa ibtila’in gobara da ta auka musu. Mataimakin Gwamnan, Sanata Umar Abubakar Tafida ne ya wakilci gwamnan a yayin ziyarar jaje da ya kai wa ’yan kasuwar da abin ya shafa. A saurari sauyin da za mu yi wa ɓangaren man fetur a Nijeriya — Dangote NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Matsalar Kwacen Waya A lokacin da ya zagaya domin duba irin ɓarnar da wutar ta yi a kasuwar, Mataimakin Gwamna ya yi kira da su mayar da lamarin ga Allah da kuma ɗaukar wannan ibtila’in a matsayin jarabawa daga gare Shi. Haka kuma, ya miƙa wa ’yan kasuwar gudumawar...
Gidauniyar Hind Rajab (HRF), mai rajin kare hakkin Falasdinawa, ta shigar da kara kan laifukan yaki bayan farmakin da sojojin ruwan Isra’ila suka kai kan jirgin ruwan agaji na Birtaniya Madleen a ruwan kasa da kasa a yammacin Lahadi. Koken dai ya shafi rundunar sojin ruwa ta Isra’ila Shaytet 13 da kwamandan ta, Vice Admiral David Saar Salama. Gidauniyar ta HRF ta yi kira da a gaggauta sakin masu fafutuka 12 da ake tsare da su, ciki har da mai fafutukar kare muhalli Greta Thunberg, dan wasan kwaikwayo Liam Cunningham, da Rima Hassan ta faransa, wadanda ke hannun Isra’ila. Jirgin ruwan na Madleen, na kungiyar Freedom Flotilla Coalition, na dauke da kayayyakin jinya, da abinci, da madarar jarirai, da sauran...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa, a halin yanzu Jamhuriyar Musulunci za ta iya kai wa Isra’ila hari “daidai” inda ta ke so bayan samun bayanan sirri kan cibiyoyin nukiliyar gwamnatin Isra’ila. Manjo Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne a wata wasika mai zuwa ga ministan leken asirin kasar, Esmail Khatib, inda ya taya shi murnar wani samame da aka kai a kwanan baya wanda ya bayar da damar samun bayyana sirrin Isra’ila da dama kan shirinta na nukiliya. Wannan nasarar, ta baiwa hukumomin leken asirin Iran damar samun wasu tarin takardun Isra’ila da suka shafi makaman nukiliya, soji, tsaro da wasu wurare na kayayyakin more rayuwa. Wuraren sun hada da wuraren...
Shugaban hukumar lafiya ta duniya, Dr. Tedros Ghebreyesus, ya bayyana cewa har yanzu cutar kyandar biri wato Mpox na kasancewa mai matukar hadari a faɗin duniya. Wannan sanarwa ta biyo bayan taro na hudu da kwamitin gaggawa na kiyaye dokokin harkar lafiya na duniya IHR ya gudanar a ranar 5 ga Yunin 2025, domin nazarin halin da ake ciki game da yaduwar cutar ta Mpox. Hukumar ta kuma ce duk da cewa an samu ci gaba a wasu kasashe wajen fuskantar cutar, kwamitin ya gargadi shugaban hukumar da cewa lamarin har yanzu babbar barazana ce ga lafiyar jama’a a duniya. Kwamitin ya danganta wannan da ci gaba da karuwar yawan masu kamuwa da cutar, ciki har da karin wadanda suka...
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce nan ba da jimawa ba al’ummar Nijeriya za su ga gagarumin sauyi a ɓangaren man fetur ɗin ƙasar. Dangote ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai, a lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci matatar mansa da ke yankin Lekki a Jihar Lagos. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Matsalar Kwacen Waya Mijina bai saci kuɗin Nijeriya ba — Maryam Abacha Ya ce sauyin da al’umma za su gani a yanzu, ba wai na rage farashin man ba ne kaɗai, wanda zai sauya baki ɗaya yadda ake gudanar da harkokin mai ne a ƙasar. “A yanzu da shugaban ƙasa ya ziyarcemu, kuma ya ba mu ƙarin makamashi, ina mai...
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce nan ba da jimawa ba al’ummar Nijeriya za su ga gagarumin sauyi a ɓangaren man fetur ɗin ƙasar. Dangote ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai, a lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci matatar mansa da ke yankin Lekki a Jihar Lagos. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Matsalar Kwacen Waya Mijina bai saci kuɗin Nijeriya ba — Maryam Abacha Ya ce sauyin da al’umma za su gani a yanzu, ba wai na rage farashin man ba ne kaɗai, wanda zai sauya baki ɗaya yadda ake gudanar da harkokin mai ne a ƙasar. “A yanzu da shugaban ƙasa ya ziyarcemu, kuma ya ba mu ƙarin makamashi, ina mai...
Iran ta bayyana cewa: Tace sinadarin Uranium wani bangare ne na bunkasa masana’antar nukiliya kuma ba zata amince kan tattaunawa ko yin sulhu kansa ba Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Sarrafa sinadarin Uranium wani bangare ne na masana’antar nukiliya, kuma batu ne da ba za a tattaunawa kansa ko yin sulhu kansa ba, kasancewarsa masana’antar cikin gida ne kuma an shefe tsawon shekaru da dama ana sarrafa shi a cikin kasa, sakamakon kokarin da masana kimiyya suka yi. babu wata kasa da ke da ikon bayyana ra’ayi kan wannan hakkin. A cikin taron manema labarai na mako-mako, Baqa’i ya yi ishara da abubuwan da ke faruwa a duniya a halin yanzu, yana mai jaddada...

Jami’in Makamashin Nukiyar Iran Ya Ce; Zarge-Zargen Da Ake Yi Kan Shirin Makmashin Nukiliyar Iran Siyasa Ce Kawai
Jami’in makamashin nukiliyar Iran ya jaddada cewa: Zarge-zargen da ake yi wa Iran kan shirinta na makamashin nukiliya, siyasa ne tsantsa Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran Behrouz Kamalvandi, ya ce: Zargin da ake yi wa Iran game da batun Shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya, tsagwaron siyasa ne, ba bisa ka’ida ko na fasaha ba. Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya kara da cewa: Kudurorin da suka biyo baya da kuma kara matsin lamba a kan Iran suna share fagen fuskantar al’amura a nan gaba. Yayin da yake ishara da cikas iri-iri da ke kawo sarkakiya ga ci gaban shirin makamashin nukiliyar Iran, Behrouz Kamalvandi ya bayyana cewa: Wadannan kalubalen da suka kara ta’azzara a cikin ‘yan shekarun...

Iran Ta Yi Kakkausar Suka Kan Babban Darektan Hukumar IAEA Saboda Yadda Yake Mika Wuya Ga Bakar Siyasa
Babban darektan hukumar IAEA ya zama tamkar wata yar tsana ce a hannun kasashen Yamma don dakile shirin nukiliyar Iran An fara taron kwata-kwata na hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa a birnin Vienna, wanda ya samu halartar wakilan kasashe 35 mambobi hukumar Bisa la’akari da rahoton da babban daraktan ya fitar game da sa ido da tabbatar da shirin nukiliyar Iran karkashin yarjejeniyar kare kai da kuma tsarin aiwatar da ayyukan hadin gwiwa ta (JCPOA) na daya daga cikin batutuwan da za a tattauna. Babban darektan hukumar ta IAEA Rafa’el Grossi ya sanar a wani rahoto da ya fitar a makon da ya gabata cewa; Yawan sinadarin uranium da Iran ke da shi ya ninka har...

Al’ummomi Daga Sassan Duniya Suna Yin Tofin Allah Tsine Kan Sace Masu Fafatuka A Kan Hanyarsu Ta Zuwa Gaza
Al’ummu daga dukkan sassan duniya suna mayar da martaninsu cikin fushi bayan sace jirgin ruwa Madeleine mai dauke kayayyakin jin kai zuwa Gaza Kwamandojin sojojin mamayar Isra’ila sun yi garkuwa da jirgin ruwan farare hula Madeleine, wanda ke yunkurin karya killace yankin Zirin Gaza da aka yi a kokarinsu na shigar da kayan agaji ga al’ummar yankin da suka rage. Sojojin mamaya sun garkuwa da masu fafutuka tare da kai su tashar ruwan Ashdod. Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin yankin sun yi tir da laifin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata. Kungiyar Hamas ta bayyana shi a matsayin ta’addancin kasa da kasa. A wani sabon laifin da ya saba wa dukkanin ka’idojin kasa da kasa da na jin kai, sojojin...
Gwamnatin Sudan ta zargi ‘yan tawayen kasar na dakarun kai daukin gaggawa da kai hari kan ayarin motocin agaji kai a yankin Darfur Gwamnatin Sudan ta sanar da cewa: “Dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan ayarin motocin agajin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Darfur ta Arewa ta hanyar jiragen sama marasa matuka ciki.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Sudan ta bayyana matukar bacin ranta tare da tofin Allah tsine da Allah wadai kan wannan mummunan lamari, tana mai jaddada cewa: “Yunkuri ne na ganganci na nufin toshe kungiyoyin agaji da dakile ayyukansu na kai kayan agaji ga fararen hula da suka makale a birnin El Fasher da sansanonin gudun hijira.” Sanarwar ta...
A wani samame da aka kai a Mallamfatori, cikin Karamar Hukumar Abadam, sojojin sun gano ƙarin gawarwakin ‘yan ta’adda da kuma tarin makamai. Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47, babura, harsasai masu yawa, ma’ajin harsasai, bututun roka, bom na hannu, rediyon hannu da wasu kayayyakin soji. Rundunar sojin ta ce waɗannan hare-hare na baya-bayan nan na nuna ƙwazon da ake yi wajen murƙushe Boko Haram da ISWAP tare da dawo da zaman lafiya a yankin Arewa Maso Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
Ma’aikatar tsaron ta Amurka ta sanar da cewa za ta baza zaratan sojojin kasar na “Marines” akan titunan birnin Los Angeles domin fuskantar tashe-tashen hankulan da ake yi domin hana korar ‘yan ci-rani ba bisa ka’ida ba. Sanarwar ma’aikata tsaron kasar ta ce; Tuni na shirya sojojin na “Marines” 700 domin su yi aikli da rundunar “National Guards” wacce tuni tana kan titunan birnin bisa umarnin shugaba Donald Trump domin kama ‘yan hijira ba bisa ka’ida ba. Ministan tsaron kasar ta Amurka ya ce ; za a kai sojojin ne a cikin birnin saboda bayar da kariya ga muhimman gine-ginen gwamnatin tarayya da kuma dawo da doka da oda. Shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya fada a jiya cewa,...
Da safiyar yau Talata ne dai sojojin HKI su ka kai wani hari a garin “Aytas-sha’ab’ dake kudancin Lebanon da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutane biyu. Kafafen watsa labarun Lebanon sun ambaci cewa, mutanen biyu da su ka yi shahada sun hada da wani makiyayi da dansa da suke kiwon dabbobinsu a burtalin dake kan iyaka da Falasdinu dake karkashin mamaya. A jiya Litinin ma dai wani jirgin sama maras matuki na ‘yan sahayoniyar, ya kai hari a garin Nabadhiyyah. Har ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan ko harin na jiya ya yi sanadiyyar shahadar wasu ko jikkata. Sai dai kuma gobara ta tashi a cikin motar da ‘yan sahayoniyar su ka kai wa harin na jiya. Daga...
A wa’adinsa na farko a 2017, Trump ya kafa irin wannan haramci da ya shafi ƙasashe bakwai ns Musulmai, wanda ya jawo gagarumar suka daga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam. Masana harkokin tsaro da na diflomasiyya na ganin cewa wannan sabon mataki na iya ƙara tsamin dangantaka tsakanin Amurka da ƙasashen da abin ya shafa, musamman a lokacin da ake buƙatar haɗin kai tsakanin ƙasashen duniya wajen fuskantar manyan ƙalubale na tsaro da tattalin arziƙi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Mun bi tsarin mulki kuma mun ƙi rashin adalci. Da PDP ta yi haka, ba za ta fuskanci wannan matsala ba.” Taron ya haɗa da tsoffin gwamnonin jihohi Samuel Ortom (Benue) da Okezie Ikpeazu (Abia), da sauran shugabannin jam’iyyar. Wike ya soki shugabannin PDP saboda sanya son rai fiye da haɗin kan jam’iyyar. Ya ce jam’iyyar sai ta koma tubalinta na asali don samun ci gaba. “Wasu shugabanni suna karkatar da dokoki don amfanin kansu,” in ji Wike, yana ambaton yadda gwamnan Taraba ya tsaya takarar gwamna ba tare da ya yi murabus a matsayinsa na shugaban jam’iyyar ba. “Dole ne a daina wannan.” Tsohon Gwamna Ortom ya yarda da maganar Wike, ya amince cewa PDP ta yi manyan kurakurai....
A bara ne dai dam ɗin Alo ta cika da ruwa har wani ɓangare ya buɗe, lamarin da ya haddasa mummunar ambaliya a Maiduguri, inda aka rasa rayuka da dukiyoyi da dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta bayyana cewa jerin wuraren da zata kaiwa hare hare a HKI a duk wani yakin da zata taso tsakanin kasshen biyu, suna hannu. Daga ciki har da ciboyoyin Nukliyar kasar wadanda ta boye su. Tashar talabjin ta Presstv a nann Tehran ta nakalto majalisar ta na fadar haka a jiya Litinin, ta kuma kara da cewa ta kara samun bayanai masu muhimmanci a wannan fagen, bayan bayanan leken asirin da ta samu a cikin yan kwanakin da sukka gabata. Labarin ya kara da cewa a halin yanzu sojojin JMI suna cikin shiri fiye da na ko wani lokaci, don maida martani ga makiya. Tace a halin yanzu jerin wuraren da sojojin Iran zasu...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya zanta ta wayar tarho da firay ministan HKI Benyamin Natanyahu kan kasar Iran da kuma yakin Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa majiyar ofishin Natanyahu ta bayyana cewa tattaunawar tana zuwa ne a dai-dai lokacinda rikici da yaki yake ci gaba a gaza, da kuma tattaunawa kan shirin Nuclear kasar Iran ke ci gaba. Labarin ya kara da cewa shugaban kasar Amurka na jirin jawabin da kasar Iran zata mayar masa dangane da shawarar da ya gabatar na warware matsalar tashe makamancin Yuranium a Iran. Har’ila yau ya na jiran jawabin da kungiyar Hamas za ta bayar kan yarjeniyar dakatar da yaki a Gaza. Shugaban dai yana cikin matsin...
Wani kamfanin kera kayakin aikin likita mai zaman kansa a nan Tehran ya gabatar da wata na’ura mai aikin tiyata wanda kuma aka dora masa kayan aiki na zamani. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gabatara da wannan na’urar a kasuwar baje kolin kayakin aikin likita karo na 26TH wanda ke gudana a nan birnin Tehran. Labarin ya kara da cewa samar da kayalin aikin likita wadanda suke tafiya da zamani, ya zama dole ne bayanda aka haka sayarwa kasar Iran irinsu daga waje. Wannan hanin ya sa a dole daga cikin gida kwararru suka fara samar da kayakin aikin likita na zamani, don wadatar da asbitocin kasar daga sayan na waje, har ma tana...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya suna ci gaba da nuna damuwa da yadda rahotannin kwace-kwacen waya suke karuwa a sassan daban-daban na kasa. Daya daga cikin rahotanni na baya-bayan nan shi ne inda a birnin Kaduna aka bayar da rahoton cewa wani matashi ya daba wa wani babban soja wuka saboda jami’in ya ki ya mika wayarsa. Ko me mahukunta suke yi don hana aikata wannan laifi? NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin Sallah Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
A baya, irin wannan mummunan abu ya faru a yankin, inda sojoji da dama suka rasa rayukansu sakamakon fashewar bama-bamai. Hakan na ƙara nuna irin barazanar da matsalar tsaro ke ci gaba da haifarwa a Jihar Sakkwato, inda mazauna ke roƙon gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen hare-haren ‘yan ta’adda, musamman masu tayar da bama-bamai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mataimakin firaministan Sin He Lifeng, ya gana da babbar ministar kudin Birtaniya Rachel Reeves jiya Lahadi a birnin Landan, inda suka zurfafa musaya game da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da hadin gwiwa a fannin hada-hadar kudade, da sauran batutuwan dake janyo hankulan kasashensu. He, wanda kuma shi ne ya jagoranci tawagar kasar Sin a tattaunawar tattalin arziki da harkokin cinikayya tsakanin Sin da Birtaniya, ya ce kamata ya yi kasashen biyu su yi aiki tare, wajen aiwatar da muhimman kudurori da shugabannin kasashen suka cimma, su kuma ingiza nasarar dandalin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Birtaniya, da zurfafa musaya da hadin gwiwa a dukkanin sassan tattalin arziki da cinikayyarsu, da ingiza cimma moriya tare, da wanzar...

An Kaddamar Da Taron Farko Na Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Amurka A London
A yau Litinin 9 ga wata ne memban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, da jami’an bangaren Amurka, suka halarci taron farko na tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya na Sin da Amurka, wanda aka kaddamar a birnin London dake kasar Birtaniya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tun daga yau Litinin 9 ga watan Yuni, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar bai wa ’yan wasu kasashe iznin shiga cikin kasar ba tare da takardar biza ba, ciki har da Saudiyya, da Oman, da Kuwait, da Bahrain. Kawo yanzu, adadin kasashen da kasar Sin ta bai wa jama’arsu izinin shiga cikin kasar ba tare da takardar biza ba, ya habaka zuwa 47. Tun daga ranar 9 ga watan Yunin shekara ta 2025, zuwa ranar 8 ga watan Yunin shekara ta 2026, mutanen dake da takardar fasfo daga kasashen Saudiyya, da Oman, da Kuwait, da kuma Bahrain, idan suna so su shigo kasar Sin don yin kasuwanci, ko yawon bude ido, ko ziyartar iyalai da abokansu, ko kuma...