Ma’aikatan Da Ba Malamai Ba A Jami’ar Jihar Taraba Sun Fada Yajin Aiki
Published: 2nd, May 2025 GMT
Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU), Comr. Muhammad Haruna Ibrahim ya bukaci gwamnatin jihar Taraba da ta gaggauta biyan ‘yan kungiyar SSANU, jami’ar Jalingo ta jihar Taraba alawus-alawus da suke bi bashi.
Comr. Haruna ya yi wannan bukata ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron majalisar zartarwa na shiyyar karo na 11 da ya gudana a Jalingo.
Shugaban SSANU ya dage cewa ya kamata a yi wa ’ya’yan kungiyar adalci, domin wadanda ba aikin koyarwa ba na daga cikin bangarori hudu da suka kafa jami’a.
Sai dai ya yi gargadin cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani memba da ya sabawa ka’idojin jami’a ba.
Tun da farko, Comr. Bitrus Joseph Ajibauka, shugaban kungiyar TSU reshen, ya yabawa gwamna Agbu Kefas bisa yadda ya amince da biyan wani bangare na bashin albashi da alawus-alawus na kungiyar da kuma aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000.
JAMILA ABBA
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Taraba
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai
A jawabinsa yayin taron, Gwamna Sani ya gabatar da kasida mai taken: “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa”, inda ya bayyana yadda Jihar Kaduna ke ci gaba da samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma, da tsarin tallafiwa jama’a.
Gwamnan Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki da kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su samu nasara a rayuwarsu.
Gwamna Uba Sani, ya kuma halarci shirin baje koli na birnin Dubai mai taken : “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira, da Tasirin Zamantakewa”, inda nan ma ya jaddada cewa jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha a mulki suna da matuƙar muhimmanci wajen buɗe damarmaki ga mutane da birane.
A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da wata ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta Janar na birnin Dubai inda suka tattauna batutuwan haɗin gwiwa a fannin kirkirar makamashin sharar gida da kula da sharar gida ta zamani, da kuma tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.
A ganawar, duk Bangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin jihar Kaduna zuwa tattalin arzikin mai ɗorewa.
Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Jihar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun ƙasashen duniya wajen yin haɗin kai, ƙirƙira, da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa da ci gaban kowa da kowa a fadin Nijeriya da ma duniya baki ɗaya
ShareTweetSendShare MASU ALAKA