Yeman : Sojojin Amurka sun kai wani gagarumin farmaki kan lardunan Sanaa da Hudaidah
Published: 20th, April 2025 GMT
Mutane da dama ne suka mutu sannan wasu sun jikkata sakamakon wasu sabbin hare-hare da jiragen yakin Amurka suka kai kan wasu yankuna na kasar Yemen.
A daren jiya wayewar yau Lahadi, sojojin Amurka sun kai hare-hare ta sama akalla 20 a Sanaa babban birnin kasar Yemen, da kuma yammacinta da gabashi da kuma kudancin kasar.
Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar Yemen suka sanar a ranar Asabar cewa kimanin mutane 80 ne suka mutu, yayin da wasu 150 suka samu raunuka sakamakon harin da Amurka ta kai a ranar Juma’a a tashar mai na Ras Issa da ke birnin Hudaidah.
Hare-haren na Amurka a Yemen sun kara gurgunta halin da kasar ta Yemen ke ciki.
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana matukar damuwarsa game da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, ciki har da hare-haren da aka kai a kusa da tashar ruwan Ras Issa.
Kakakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Stéphane Dujarric, ya bayyana a wata sanarwa jiya Asabar cewa, “Guterres ya damu matuka da hare-haren da Amurka ta kai a ranakun 17 da 18 ga watan Afrilu a ciki da wajen tashar jiragen ruwa na Ras Issa na kasar Yemen, wanda ya yi sanadin jikkatar fararen hula da dama, ciki har da ma’aikatan agaji biyar.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Yemen
এছাড়াও পড়ুন:
Boko Haram Sun Hallaka ‘Yan Zaman Makoki 7, Sun Jikkata Wasu A Borno
Sanata Ali Ndume, mai wakiltar yankin Borno ta Kudu, ya bayyana cewa hare-haren na ƙara ƙamari a yankin abun takaici ne.
Ya ce ya samu rahoto tsakanin Hawul da Garkida inda aka ce an kashe ’yan sa-kai sama da 10 a ranar Litinin.
A cewarsa, sama da mutane 100 aka kashe cikin wata guda a hare-hare da aka kai Sabon Gari, Izge, Kirawa, Pulka, Damboa, Chibok, Askira Uba da wasu garuruwa da dama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp