GORON JUMA’A 28-03-2025
Published: 28th, March 2025 GMT
Ina mika sakon gaisuwata ga iyayena da yayyena da kannena, ‘yan uwana maza da mata wadanda muka yi makaranta tare da su, al’ummar Musulmi baki daya, duk ina yi muku fatan alkhairi tare da fatan an yi Juma’a lafiya. Allah ya maimaita mana, ina gaida mijina tare da yi masa fatan alkhairi da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya.
Sako daga Yusuf Murtala
Assalaikum alaikum,
Al’ummar Musulmi, ina yi wa kowa fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyayena ina yi musu fatan alkhairi da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana yayyena da kannena da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya. Ina gaida yayye iyaye da kannensu tare da yi musu fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da Juma’a.
Sako daga Sadiya Musa
Assalamu alaikum! Ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki na gida da na nesa ‘yan uguwarmu da wadanda muka yi makaranta tun daga kan firamare, Sakandire, jami’a duk ina muku fatan alkhair da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.
Sako daga Zainab Abba Hussain
Ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga mijina, ina mika sakon gaisuwata zuwa ga iyayena da fatan alkhairi ina fatan Allah ya jikan mahaifiyata ina mika sakon gaisuwa zuwa ga ‘ya’yana da ‘yan uwa da abokan arziki na gida da na waje da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa zuwa ga daukakin Musulmi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana, amin ya Allah.
Sako daga Haruna Ahmad
Ina mika sakon goron Juma’a ga al’ummar Musulmi gaba ki daya, da jamia’an tsaro dake kasar nan baki daya. Ina mika gaisuwata ga mahaifiyata Hajiya Lamee Musa, da mahaifina Alhaji Aliyu Isah. Ina mika sakon gaisuwata ga yaya ta Ummi, da kanwata Aisha, da yayana Faisal, da kanina Abdulrahman, da yaya na Sadik da fatan sako na ya iso ku cikin koshi lafiya.
Sako daga Sajida Ahmad Ibrahim
Assalamu alaikum!
Ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga mijina, ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga iyayena da fatan alkhairi ina mika sakon gaisuwa zuwa ga ‘ya’yana da ‘yan uwa da abokan arziki na gida da na waje da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa zuwa ga daukacin Musulmi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana amin ya Allah.
Sako daga Bara’atu Sani
Assalamu alaikum Ina mika sakon gaisuwa ga ma’aikatan wannan gidan jarida na LEAdERSHIP Hausa, tare da mika godiyata da suka ba ni dama da na mika sakon gasuwata na gode.
Ina mika sakon gaisuwa ta ga mijina da iyaye na ina fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa ta ga ‘yan ‘uwana yayyena da kannena da fatan suna cikin koshin lafiya sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.
Sako daga Aisha Abubakar
Assalamu alaikum! Ina mika sakon gaisuwata ga mutanen gidan wannan jarida mai albarka tare da mika godiyata da suka ba ni dama da na mika sakon gaisuwata na gode. Ina gaida iyaye da ‘yan uwa da abokan arziki, abokan karatu da abokan aiki na da al’ummar Musulmi baki daya tare da barka da Juma’a da fatan an yi Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.
Sako daga Umar Idris
Assalamu alaikum.
Al’umar Musulmi ina muku Sallama irin ta Addinin Musulunci, Assalamu alaikum Warahmatullahi ta’ala Wabarakatuhu! ina yi wa kowa fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyayena ina yi musu fatan alkhairi da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana yayyena da kannena da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya. Ina gaida yayye iyaye da kannansu tare da yi musu fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da Juma’a.
Sako daga Muhammad Hashim
Assalamu alaikum warahmatullah!
Ina mika sakon gaisuwa ga iyaye, ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kun yi Sallar Juma’a lafiya tare da kai ziyara, Allah ya sa haka amin, ina gaida kowa da kowa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: da fatan an yi Sallar Juma a lafiya Allah ya maimaita mana tare da fatan an yi Sallar Juma a lafiya da fatan sun yi Sallar Juma a lafiya ina mika sakon gaisuwa zuwa ga ina mika sakon gaisuwa ta Ina mika sakon gaisuwa ta yan uwa da abokan arziki Ina mika sakon gaisuwata ina mika sakon gaisuwata na mika sakon gaisuwata ummar Musulmi gaisuwata ga
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya janye dokar ta-ɓaci da ya ayyana ta tsawon watanni shida a Jihar Ribas.
Tinubu, ya ayyana dokar tun a ranar 18 ga watan Maris, 2025, saboda rikicin siyasa da ya haifar da tsaiko a harkokin mulki tsakanin ɓangaren Zartarwa da Majalisar Dokokin jihar.
NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025 Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyiA jawabin da ya gabatar a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Laraba, Tinubu ya ce matakin dokar ta-ɓacin ya cimma manufarsa, kuma ba za a tsawaita ba ƙarewar wa’adin da aka gindaya.
“Ina farin ciki yau game da bayanan da ke hannuna, an samu yanayin fahimta a tsakanin dukkanin masu ruwa da tsaki a Jihar Ribas domin dawo da mulkin dimokuraɗiyya cikin gaggawa,” in ji Shugaban Ƙasa.
Gwamnan Jihar, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, tare da ‘yan majalisar dokokin jihar, za su koma kan kujerunsu daga ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba, 2025.
Tun da farko, dokar ta-ɓacin ta dakatar da manyan jami’an gwamnati da masu madafun iko na jihar sakamakon rikici da aka daɗe ana yi a jihar.
“Da ban ayyana wannan dokar ta-ɓacin ba, da hakan ya zama babbar gazawa a wajena a matsayina na Shugaban Ƙasa.
“Amma yanzu da zaman lafiya da doka suka wanzu, al’ummar Jihar Ribas za su sake cin moriyar dimokuraɗiyya,” in ji Tinubu.
Ya kuma yi kira ga gwamnoni da majalisun dokokin jihohi na faɗin Najeriya da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin ɓangaren zartarwa da na majalisa.
Har ila yau, ya jaddada cewa zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci su ne tubalin kawo ci gaban dimokuraɗiyya ga al’umma.