Xi Jinping Ya Halarci Bitar Tawagar Lardin Jiangsu
Published: 5th, March 2025 GMT
Da yammacin yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci bitar rahoton aikin gwamnatin kasar, na tawagar lardin Jiangsu, a taro na uku na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14.
Xi ya jaddada cewa, a matsayinsa na lardi mai karfin tattalin arziki, dole ne lardin Jiangsu ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta ci gaban kasar Sin, musamman ma a fannin sa kaimi ga inganta kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha, da dunkulewar masana’antu, da sa kaimi ga inganta zurfafa yin gyare-gyare, da bude kofa ga kasashen waje, da shigewa gaba wajen aiwatar da manyan tsare-tsare na ci gaban kasar, da kuma ba da misali a fannin samar da wadata ga jama’a baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu
Gwamna Zulum ya nuna jin dadinsa ga kwamishinonin biyu, tare da yi musu fatan alheri a cikin ayyukansu na gaba.
Sai dai ya sanar da nadin Engr. Mohammed Habib da Ibrahim Hala Hassan domin maye gurbin kwamishinonin biyu da aka sauke.
A halin da ake ciki, Gwamna Zulum ya kuma amince da nadin Farfesa Yusuf Gana Balami a matsayin Shugaban Hukumar Ilimin Sakandare ta Jihar Borno.
Balami, Farfesa a fannin ilimi, ya fito ne daga Hawul da ke kudancin jihar.
Zulum ya taya Balami murna tare da bukatar sa da ya yi amfani da shekarunsa na gogewa a fannin ilimi, a matsayin shugaba a bangaren gudanarwa da karantarwa wajen sake fasalin ilimin sakandare a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp