Syria: Sojojin HKI Sun Kai Wa Yankin Tartus Hari
Published: 4th, March 2025 GMT
Kamfanin dillancin labarun “Sana” na kasar Syria ya ambaci cewa; jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a wani wuri dake gefen garin Tartus, sai dai babu rahoto akan asarar rayuka har yanzu.
Kamfanin dillancin labarun “ Sana” ya ci gaba da cewa; Ma’aikatan agaji suna kokarin gano hakikanin inda aka kai wa harin.
Su kuwa sojojin HKI sun sanar da kai hari ne akan wani rumbun makamai dake yankin “Kardaha’.
Wannan ba shi ne karon farko da sojojin na HKI su ka kai hari a garin Tartus ba, a ranar 16 ga watan Disamba ba sun kai wannan irin harin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA