Babu Wani Abin Burgewa A APC, Za Mu Kori Wannan Gwamnati A 2027 – Tambuwal
Published: 21st, February 2025 GMT
Tambuwal ya bukaci ‘yan adawa da su hada kai su tsara dabarun tunkarar zaben 2027, yana mai jaddada bukatar bai wa ‘yan Nijeriya mafita mai inganci.
“Babu wani abin burgewa a APC wanda ya wuce amfanin kashin kai. Mu da muke kokarin saka kishin kasar nan wajen yi wa kasa hidima na gaskiya mu hada kai don korar wannan gwamnatin a 2027, domin ta gaza share wa ‘yan Nijeriya hawayensu.
A halin da ake ciki kuma, jam’iyyar PDP a yankin arewa maso yamma ta sake jaddada aniyarta ta kwato mulki a shekarar 2027, inda ta jaddada muhimmancin hadin kai a tsakin ‘ya’yan jam’iyyar.
Sanarwar da aka fitar a karshen taron, wanda shugaban jam’iyyar PDP na yankin arewa maso yamma, Sanata Bello Hayatu Gwarzo ya karanta, ya kara jaddada aniyar jam’iyyar na dawo da shugabancin Nijeriya.
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati Za Ta Kafa Cibiyoyin Kiwo a Yankuna Shida — Ƙaramin Ministan Noma
A cewar ministan: “Aikin haɗin gwiwa da haɗin kai tsakanin Ma’aikatun Noma, Muhalli, Albarkatun Ruwa, Bunƙasa Kiwon Dabbobi da kuma Tattalin Arzikin Ruwa yana da matuƙar muhimmanci domin cika manufofin Ajandar Sabunta Fata.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp