A Kalla Mutane 48 Ne Su Ka Mutu A Wajen Hako Zinariya A Kasar Mali
Published: 16th, February 2025 GMT
A jiya Asabar ne aka sami hatsari a wani wurin hako zinariya dake yammacin kasar Mali da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 48.
‘Yan sanda a yankin da lamarin ya faru ne su ka sanar da faruwar hatsarin a wurin da ake hako zinariya ba tare da izinin hukuma ba,wanda kuma ya rutsa da wata mace da karamin yaronta.
Wani jami’in yankin da lamarin ya faru ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne a wani wurin hako zinariya da aka kauracewa,da a halin yanzu mata ne su ka fi hako zinariya a cikinsa.
A nashi gefen shugaban hukumar masu hako zinariya a kasar ta Mali Abubakar Keita ya bayyana cewa; A kalla mutane 48 ne su ka kwanta dama sanadiyyar afkuwar wannan hatsarin.
Daga lokaci zuwa lokaci ana samun afkuwar irin wannan hatsarin a cikin kasashen yammacin Afirka da ake hako zinariya ba bisa izinin mahukunta ba, kuma ba bisa tsari ba.
Mali tana cikin kasashen da suke da wuraren hako ma’adanai mafi girma a cikin yammacin Afirka wanda yake taka rawa a kasafin kudin kasar da kawo ¼.
A watan Disamba na shekarar da ta gabata, ministan kudi na kasar ta Mali Alosini Sano ya ce, kasarsa ta gudanar da wani bincike da sake yin bitar wata yarjejeniya akan cinikin zinariyar da ya ba ta damar dawo da kudaden da sun kai kudin Farank biliyan 700, wato fiye da Euro biliyan daya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: hako zinariya
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴansanda Sun Kama Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025
Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025 Labarai Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda October 31, 2025