An Bude Babban Taron Kasa Na Nijar
Published: 15th, February 2025 GMT
A Nijar yau ne aka bude babban taron kasar, wanda zai tsara dokoki kan yadda za’a tafiyar da kasar a lokacin mulkin rikon kwarya na soji.
Shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani ne ya kaddamar da taron a Yamai babban birnin kasar inda ake sa ran shafe kwanaki hudu ana tattaunawa.
Taron zai kuma bayar da shawara kan tsawon wa’adin gwamnatin rikon kwarya.
Taron ya samu halartar tsofaffin shugabannin kasar ciki har da Mahamadou Issoufou da tsofaffin shugabannin majalisar dokokin kasar da tsofaffin firaministoci na kasar da wasu baki daga Burkina Faso da Mali da wasu kasashen.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Tace Samar Da Kasar Falasdinu Mai Cikekken Yenci Ba Abin Tattaunawa Bane
Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa samar da kasar Falasdinu mai cikekken yenci , kuma da dukkan birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar, hakkin Falasdinawa ne wannan babu tattaunawa a kansa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jakadan kasar Iran na din din din a MDD Amir Said Iravani yana fadar haka, a jiya laraba, a lokacinda yake gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaro na majalisar.
Jakadan ya bukaci kungiyoyin Falasdinawa su hada kansu don duk wani sabani a tsakaninsu nasarace ga HKI.
Iranvani ya ce HKI tana ci gaba da aikata laifukan yaki a yankin Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan, tare da tallafin Amurka da wasu kasashen yamma. Kuma tallafin da wadannan kasashen suka bawa HKI, kama daga makamai, kudade, tallafin siyasa da sauransu ne suka sa HKI ta ke samun karfin giuwan ci gaba da sabawa dokokin kasa da kasa.
Tun kusan watanni biyu da suka gabata ne HKI ta hana shigar kayakin abinci da wasu bukatun mutanen kasar Falasdun a gaza, wanda shi shi kaidai ya isa laifukan yaki da dama, wadanda suka sa dole na a hukunta HKI kan wadannan laifuffukan. Da kuma wadanda suka taimaka masu.