NUJ Ta Dukufa Wajen Kula Da Jin Dadin ‘Yan Jarida
Published: 14th, February 2025 GMT
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) karkashin jagorancin shugaban kasa Alhassan Yahaya, ta jaddada aniyar ta na inganta aikin jarida da kuma jin dadin ‘yan jarida a fadin Najeriya.
Kungiyar tana aiki tukuru don ganin an zartar da kudurin dokar inganta kafafen yada labarai a majalisar dokokin kasar don karfafa masana’antar.
A cikin sanarwar da ta fitar a karshen taron kaddamar da kwamitin koli (CWC), wanda aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, kungiyar na hada kai da Majalisar Dokoki ta kasa, kungiyoyin farar hula, da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an samar da dokar inganta harkokin yada labarai.
Sanarwar ta bayyana cewa, CWC ta yanke shawarar gano harkokin kasuwanci don samun kudaden shiga don tabbatar da tafiyar da harkokin kungiyar cikin sauki.
Har ila yau, ta ce, mambobin CWC sun yaba wa shugaban NUJ bisa hangen nesansa kuma sun bukace shi da ya ci gaba da ci gaba da ciyar da manufofin kungiyar gaba.
Sanarwar ta yi bayanin cewa, kungiyar za ta shirya taron karawa juna sani na horar da ‘yan jarida guda biyu a cikin rubu’in farko na shekara don bunkasa sana’o’i a bangarori daban-daban na harkar yada labarai.
Domin tabbatar da gaskiya wajen fitar da kudaden rajista, kungiyar na tattaunawa da ofishin biyan albashi na zamani na tarayya (IPPIS) domin tabbatar da cewa duk kudaden da aka cire daga mambobin kungiyar NUJ ana tura su kai tsaye zuwa asusun NUJ.
CWC ta yabawa gwamnatin jihar Kebbi kan ci gaban ababen more rayuwa da suka hada da titunan gari, filin ajiye motoci na zamani, zuba jarin noma, da tsare-tsare na jin dadin jama’a, ya kuma bukaci gwamnan da ya ci gaba da gudanar da wannan kokari na ganin ya cika aikin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na dan kungiya.
Kungiyar ta NUJ ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da fadin kasar nan na noma domin bunkasa samar da abinci sannan kuma ta yi kira ga hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen magance kalubalen tsaron da ke addabar al’ummar kasar, haka ma gwamnati ta ba da fifikon jin dadin ‘yan kasa wajen tsara manufofi.
PR/Abdullahi Tukur/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
A nata bangare kuwa, Amurka ta bayyana aniyarta ta aiki tare da bangaren Sin, wajen ci gaba da warware sabani a fannonin tattalin arziki da cinikayya ta hanyar tsarin gudanar da shawarwari, da ingiza damar samar da karin nasarori daga tattaunawar, da kara samar da daidaito a alakar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da Sin.
Wakilin cinikayya na kasa da kasa na Sin karkashin ma’aikatar cinikayya, kuma mataimakin ministan cinikayyar kasar Li Chenggang, ya bayyana a yayin da yake yiwa manema labarai karin haske game da zaman tattaunawar sassan biyu. Ya ce sassan biyu suna sane da muhimmancin wanzar da daidaito, da kyautata alakar tattalin arziki mai nagarta tsakanin Sin da Amurka, sun kuma yi kyakkyawar musaya game da muhimman batutuwan cinikayya da na raya tattalin arziki dake jan hakulansu. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp