Kasar Sin Ta Bayyana Sunan Tufafi, Da Na Motar Zirga-zirga A Duniyar Wata
Published: 12th, February 2025 GMT
Hukumar kula da ‘yan sama jannati na kasar Sin (CMSA), a yau Laraba, ta bayyana sunayen tufafin ‘yan sama jannati da motar zirga-zirga a duniyar wata na aikin binciken wata na kasar.
CMSA ta ce, an sa ma tufafin na ‘yan sama jannati suna Wangyu, wanda ke nufin kallon duniyar sama, kuma ya yi daidai da sunan tufafin da ‘yan sama jannati su kan sa lokacin da suka fita daga tashar sararin samaniya, wato Feitian, wanda ke nufin tashi zuwa sararin samaniya.
Kazalika, sunan motar zirga-zirga a duniyar wata shi ne Tansuo, wanda ke nufin binciken gaibu. Hukumar ta ce, wannan sunan yana nuna aikin da motar ke yi, da darajarta wajen taimaka wa jama’ar kasar Sin wajen gano ababen al’ajabi na duniyar wata.
A halin yanzu, ayyukan bincike da suka shafi Wangyu da Tansuo suna ci gaba yadda ya kamata, a cewar CMSA. (Mohammed Yahaya)
কীওয়ার্ড: yan sama jannati a duniyar wata
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban SUBEB Yayi Alkawarin Bayar Da Tallafin Ilimi A Jihar Nasarawa
A wani gagarumin ci gaba na inganta walwala da ci gaban yara da matasa wadanda suka isa makaranta, Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Farko ta Jihar Nasarawa NSUBEB, Dokta Kasim Mohammed Kasim ya karbi tawagar Kids & Teens Resource Center K&TRC a wani taron bayar da shawarwari da aka mayar da hankali kan shirin Ilimi don Lafiya da walwala, wanda UNESCO ke tallafawa.
An gudanar da babban taron ne a hedkwatar Hukumar NSUBEB, inda ya samu halartar kwamishinonin hukumar su uku, da Daraktoci da dama, da kuma tawagar K&TRC karkashin jagorancin wanda ya kafa kuma Shugaba, Mista Martin-Mary Falana.
Tattaunawar a yayin zaman ta tabo batutuwan da suka shafi rayuwar yara da matasa a jihar, wadanda suka hada da yawaitar cin zarafin mata kamar lalata da fyade, cin zarafi a makarantu, kananan yara da auren dole, kaciyar mata, da kuma yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.
Mahalarta taron sun amince da bukatar gaggawar samar da cikakken martani ta bangaren ilimi domin tunkarar wadannan kalubale.
Shugaban hukumar ya yi alkawarin ba da cikakken kudurin siyasa na hukumar tare da ba da tabbacin baiwa kungiyar K&TRC na NSUBEB goyon baya wajen samar da yanayi mai dacewa don samun nasarar aiwatar da aikin.
COV/Aliyu Muraki/Lafia.