Iran Zata Ci Gaba Da Kare Shirinta Na Makamashin Nukliya Da Duk Karfin Da Take Da Shi: Ali Shamkahani
Published: 10th, February 2025 GMT
Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci shawara kan al-amuran siyasa Ali Shamkhani ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran za ta ci gaba da kare shirinta na makamashin Nukliya na zaman lafiya da duk karfin da take da shi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ali Shamkhani ya na fadar haka, a lokacinda ya ziyarci wata kasuwar baje koli, inda cibiyar makamashin Nukliya ta kasar Iran (AEOI) ta ke baje kolin irin ci gaban da ta samu a wannan fasahar a yau litinin a nan Tehran.
Babban mai bawa jagora shawara a kan al-amuran siyasa ya kara da cewa, gwamnatin JMI za ta ci gaba da kare duk abinda zai amfani mutanen kasar Iran, ko da kuwa manya-manyan kasashen duniya basa son hakan.
Ya ce, JMI bata da manufar kera makaman nukliya a yanzu ko nan gaba, amma fasahar nukliya tana da matukar muhimmaci, a fannonin ilmi da dama, daga ciki, har da samar da magunguna, ayyukan noma, makamashin lantarki mai tsabata, wanda baya gurbata yanayi, samar da ruwa, da kuma gyra yanani da sauransu.
Ali Shamkhani ya kammala da cewa, Don haka duk tare da adawar da wasu manya-manyan kasashen duniya suke nunawa iran kan mallakar wannan fasahar, ba za ta taba barin ta ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta roƙi China ta sa baki kada Iran ta rufe mashigar tekun Hormuz
Gwamnatin Amurka ta buƙaci ƙasar Sin da ta hana Iran rufe mashigar tekun Hormuz, ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar kayayyaki a duniya.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi kiran ne bayan da kafar yada labarai ta Iran, Press TV ta ruwaito cewa majalisar dokokin ƙasar ta amince da shirin rufe mashigar.
Duk wani cikas ga samar da man fetur zai yi tasiri mai tsanani ga tattalin arzikin duniya.
Ƙasar Sin ce babbar mai sayen mai daga Iran kuma tana da kyakkyawar alaka da Tehran.
Harin Iran: Amurka ta ɗebo ruwan dafa kanta Koriya ta Arewa za ta taimaka da gyara tashoshin nukiliyan Iran —Masani NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin NajeriyaFarashin man fetur ya tashi bayan harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran, inda farashin man Brent crude ya kai matsayinsa mafi girma cikin watanni biyar.
Matakin rufe mashigar tekun Hormuz wadda kusan kashi 20 cikin ɗari na man fetur da iskar gas na duniya ke bi ta cikinta, zai iya jefa duniya cikin bala’in rashin mai.
Masani kan harkokin kasuwanci Gerrit Heinemann ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Daily Mail ta ƙasar Birtaniya, cewa idan Iran ta zaɓi rufe mashigar, sakamakon zai zama “bala’i.”
Mashigar hanya ce ta kasuwanci mai mahimmanci ga duniya, inda kusan kashi ɗaya cikin biyar na man fetur na duniya ke bi ta mashigar teku. Kazalika adadi mai yawa na iskar Gas Mai Ruwa (LNG), na bi ta mashigar, wanda hakan ya sa ta zama “mafi muhimmancin mashigar isar da man fetur a duniya.”
Kwamandan Rundunar Juyi Juya Halin Musulunci na Iran kuma ɗan majalisar dokokin ƙasar, Esmail Kosari ya bayyana cewa wannan matakin yana cikin ajandarsu kuma “za a yi shi duk lokacin da ya zama dole.”
A ƙarshen makon jiya Kowsari ya sanar cewa rufe mashigar tekun Hormuz “yana cikin matakan da gwamnatin ƙasar ke duba yiwuwar ɗauka, kuma Iran za ta yanke shawara da ya fi dacewa.”
Press TV ya ruwaito cewa matakin rufe mashigar tekun Hormuz bai kammala ba, har yanzu Majalisar Koli ta Tsaro ta Kasa ta Iran ce ke da hurumin yanke shawara ta ƙarshe kan lamarin.
Amma Kowsari ya bayyana cewa Iran ba ta iyakance iya matakin da za ta ɗauka a kan Isra’ila ba, kuma, “martanin soji wani yanki ne kawai na martaninmu gaba ɗaya.”