Gwamnan Kaduna Ya Kare Shirinsa Na Sulhu Da ‘Yan Bindiga
Published: 31st, January 2025 GMT
“Da na tambaye shi dalili, sai ya ce al’ummominmu suna fama da barnar ‘yan bindiga da hakan ke janyo asarar rayuka da garkuwa da mutanenmu tsawon shekaru zuwa yanzu ba tare da samun mafita da shawo kan lamarin ba.”
Gwamnan ya ce bayan rokon, ya zauna da masu ruwa da tsaki ciki har da mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, kafin daga karshe suka amince da fito da shirin yin sulhun.
Ya kara da cewa matakin na zuwa ne bayan da ‘yan fashin dajin suka sako mutane 200 da suka yi garkuwa da su a kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari. Gwamnan ya nuna fatansa na cewa matakin zai dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ta yadda manoma za su sami damar komawa gonakansu domin yin noma da kuma dawo da harkokin kasuwanci yadda ya kamata.
“Gara na yi sulhu da ‘yan bindiga da ran mutum daya ya salwanta. Idan ba haka ba, ni ne zan je gaban Allah na yi bayanin wannan rasa ran domin na rantse cewa zan kare rayukan mutane,” ya shaida.
Kazalika, ita ma kungiyar Dattawan Arewa (ACF), ta shelanta cikakken goyon bayanta ga matakin Gwamna Uba Sani na yin sulhu da zaman lafiya da ‘yan bindigan a Kaduna da ma yankunanta.
A hirar da ya yi ta wayar salula da LEADERSHIP, jami’in watsa labarai na kungiyar ACF, Farfesa T.A Muhammad Baba, ya ce kungiyar ta yi maraba da yunkurin gwamnan na kawo karshen garkuwa da mutane da aikace-aikacen ‘yan fashin daji.
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamandan NDA Ya Bukaci Dalibai Su Dage da Karatu a Taron FGC Malali
Kwamandan, Nigerian Defence Academy NDA, Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya bukaci dalibai da su jajirce wajen ganin sun samu nagartar ilimi.
Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya yi wannan kiran ne a yayin bikin yaye dalibai da jawabai da kuma bayar da kyaututtuka da aka yi a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Malali Kaduna.
Kwamandan NDA wanda tsohon dalibi ne a kwalejin ya bayyana jin dadinsa da yadda dalibai ke gudanar da ayyukansu ya yabawa mahukunta da ma’aikatan FGC Kaduna bisa yadda suke kiyaye ka’idoji.
A nasa jawabin shugaban kungiyar tsofaffin dalibai ta FGC Kaduna, Kwamared Seyi Gambo ya ce kungiyar za ta ci gaba da bayar da gudummawar ta wajen daukaka darajar kwalejin ta hanyar daukar matakai na koyar da dalibai.
Shima da yake jawabi, shugaban taron kuma tsohon gwamnan jihar jigawa, Sanata Saminu Turaki ya bukaci dalibai da su tabbatar sun yi fice a fannin ilimi domin su zama masu amfani a cikin al’umma.
Shima da yake jawabi shugaban kwalejin gwamnatin tarayya ta Kaduna, Prince Adewale O. Adeyanju ya yi kira ga iyaye da su bada hadin kai ga hukumar makaranta domin ganin an kula da harkokin koyo.
An bayar da kyautuka na kyaututtuka da kudi ga daliban da suka kammala karatunsu da nagartattun dalibai da suka hada da malamai da suka kware sosai da kuma ma’aikatan da ba na koyarwa a kwalejin.
COV/SHETTIMA A.